1&2

12 0 0
                                    

👠👠👠
      👠
👜👜👜
      👜
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_)
_15/6/2020_
👠👠👠
         👠
👜👜👜
     👜

*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }
    
    📚 *HADAKA*📚
   📝 *WRITER'S*📝
🖊️ *ASSOCIATION* 🖊️
_Home_ _of_ _copration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_

@: *wattpad*
_AmeeraAdam60_

*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🤝🏻
_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

          1&2
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

Wata matashiyar budurwa ce ta shigo   cikin falon hannunta dauke da babban faranti wanda yake dauke da jug da food flaskes gefe guda kofuna da plate ne, da sallama ta shigo ta dan durkusa gaban wata dattijuwa ta ajiyesu a hankali ta mike zata tafi, dattijuwar dake zauna kan dadduma  tana Addua bayan idar da sallah tayi mata gyaran murya, "ahankali matashiyar budurwar ta koma ta zauna cikin zuciyarta tana ayyana sabon aikin da hajiya iya zata sa ta.

Sai da ta kammala Addua ta shafa sannan ta kalli budurwar data kawo mata abinci cikin kulawa tace, " hansai bude mun kwanikan nan da sauri hansai ta hau bude food flasks din, flask na farko soyayyiyar doya da kwai ce ta biyu kosai ne ta uku farfesun kaji, jug din ta bude kunun tsamiya ne gefe karamin flask din tea ne, " sai da ta gama kallonsu daya bayan daya ta kalli hansai tace wuce ki tafi komai yayi dai-dai amma kamar akwai abunda ba'a hadomun dashi ba? Ta karasa maganar ta kallon hansai data tashi tana niyyar tafiya, "ganin bata  ba ta amsa ba yasa tace mata ta tafi.

Har hansai taje bakin kofa tajiyo muryar hajiya iya na kwala mata kira, "mtsswww, dan guntun tsaki taja kasa-kasa tace tsohuwa sai rigima komai kayi mata sai ta nuna ma san iyawa 😏 wai hansai ba kiranki nake ba kiji ja'ira yar nema tsaiwar me kike abakin kofar ko ni zan biyoki? A'a hjy iya tintibe nai gani nan zuwa ta karasa maganar tana dingisa kafar karya🤣

Gani hjy iya me kike bukata? Hansai ce durgushe gaban hjy iya,Yauwa hansai ina lemon tsamiyar naga ba'a kawo mun ba ko sai na tambaya? Ummm..... ay...... Dama...... Ban..., Ke banasan shashanci ki bude baki kimun magana kya dinga mun kame-kame, eh dama yau bamuyi lemon tsamiya ba saboda jiya Munji kince alala ta bata miki ciki kina ta gudawa, to sai mukace yau kar ayi lemon tsamiya kar ta kara rikita miki ciki, abari zuwa gobe ko jibi lokacin cikin ki ya yi miki sauki.

Too sannu iyaye na wato har kun fara yanke hukunci baku tambayi shawarata ba ko? Da ciki na ya lalace sai nace muku bana bukatar lemon ko, " a'a hajiya kiyi hakuri insha Allah bazamu kuma ba.

Ay karshen maganar kenan mutanen banxa sai kuje ku hada mun shi kuma kar akira sallar isha'i ba'a kawo mun ba, tafi ki bani guri ina jiranki.

Da hanzari hansai ta wuce tana mita kasa-kasa galala hjy iya tabita da kallo tana fadin, hansai ni kike yiwa gunguni lallai yarinyar nan kin kai minzali, wlh bari habibu yaxo bazan iya da sakarcinki ba,   " da sauri hansai ta juyo wlh hjy iya ba gunguni nake miki ba cewa nai hajiya iya dai tanasan lemon tsamiya.

Au hoo na dauka mita kike mun insa habibu ya mai daki garunku, a a wane ni hajiya Allah  ya kara girma hajjaju makkatun, " Aameen, to na barki lafiya hjy iya, "to maza ina jira dai, "angama hjy iya.

mtswww wallahi nagaji da matsalar hjy iya ace tsohuwa sai iko da sa aikin tsiya wallahi da badan kudin kayan daki nake tarawa ba da tuni na dade da barin gidan nan, ke hansai ki dinga iya bakinki wallahi kinsan halin suwaiba sarai gurin gulma da munafurci yanxu idan taji ki kinsan ba makawa gurin hajiya iya zataje ta fada mata, kuma kinsan halin hajiya iya inzaki kwana kina mata magiya kingama aiki agidan nan kenan, "inna zainabu ce take mata fada bayan taji abunda hansai ke fada lokacin da ta shigo sashen yan aiki.

ummmm aykuwa dai inna zainabu, gashi kuwa innarmu tace inban tara kudi da yawa ba baza ta mun kayan daki me yawa ba, "atoh kinji ko duk wani abu da zai kawo miki matsala da hjy iya ki kiyaye, insha Allahu inna zainabu zan kiyaye.

Hansai bata gama yiwa hjy iya lemon tsamiya ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i, da sauri ta karasa falon hjy iya lokacin hjy iya ta gama cin abinci tana wanke hannu aroba, "barka da hutawa hjy iya ga lemon tsamiyar na kammala, ta karasa maganar tana ajiyewa hjy iya jug din agaban ta, " ke hansai me yasa wani lokacin bakida kan gado ne? Hjy iya me kuma nayi? Au bakima san me kika yi ba kin shigo mun daki babu sallama kamar ba diyar musulmai ba, cikin kosawa hansai tace to tuba nake hjy iya ayi hakuri ta karasa maganar tana kokarin tashi.

Ay bakida aiki sai na bada hakuri kamar gaske shashasha tashi ki bani guri, to hjy iya atashi lafiya, "hansai har taje bakin kofa ta juyo, "hjy iya nace akwai abunda za'a miki anjima ko sai da asuba?

A'a ba abunda nake bukata sai da asuba ki jamun kofar, to hjy iya Allah ya tashemu lfy.

Aameen yauwa ki cewa zainabu karta kawon kunun tsamiya da asuba akwai ragowa anan, angama hjy iya zan gaya mata.

Hajiya iya sai da ta kammala komai wajen karfe goma na dare sannan ta wuce dakin baccinta, shigar ta dakin keda wuya wayar ta ta fara ringing, daukar wayar tai tana fadin dan halak yanxu nake zancenka azuciyata, "daga cen bangaren cikin girmamawa ya gaida mahaifiyar tasa suka shiga hira, sannan sukayi sallama, hjy iya harta kwanta ta tuno da maganar dinkin kayan sallar su.

Da sauri ta dauko waya ta kara kiransa, yana dauka hjy iya ta fara magana, habibu waini ya maganar dinkin mu ne? gashi yau har munkai azumi ashirin da biyar ba'a turo yarinyar nan fa'iza dasu ba kullum nai maka maganar sai kace sai fa'iza zata xo ta kawo mana, " hjy iya kiyi hakuri insha Allah gobe zata zo kinsan halin madinkan nan,sai  yau telan ya kawo muku zata hado muku gobe insha Allah ta kawo tacemun ana gurinki ma zatayi sallah.

To Allah ya kawo ta lafiya kaga na samu yar rakiya *YAWON* *SALLAH* dama tafiya bibbiyu tafi dadi, " hjy iya yawon sallah kuma? Ana cikin wannan yanayin dan Allah karki wahalar da kanki bakiji ma anhana shiga cinkoson jama'a ba saboda wannan annobar corona virus din?

kai habibu dakata mun banasan maganar banza da wofi, " wannan duk makircin yahudawa ne turawa masu jan kunne, " babu wata cuta wai korola boris duk zancen banza ne, a'a hjy iya wannan cutar fa gaskiya ce akwai ta, " dan Allah kiyi hakuri wata kila ma gwamnati bazata bari afita ba tunda kinga har yanxu zaman lockdown din nan akeyi, hjy iya hanyar lafiya abita da shekara gsky ba inda zaki.

To sannu ubana nace sannu ubana idan na tashi tafiya ka tade kafafuwa na ko ka sa mukulli ka rufen kofar, a'a hjy iya Allah ya huci zuciyarki adai duba maganar, kaga habibu wlh ka fita idona, shekara da shekaru ana abu sallah daga shekara  sai shekara asawa mutum takunkumin rashin fita, zancen banza ma kenan.

    An hana mu sallar tarawee anhana mu jin tafsir a masallatai, zumuncin ma hana mu za'ayi.

Hjy iya kiyi hakuri dan Allah ban fadi haka dan wani abu ba, lafiyarki nake kiyaye miki amma gobe ni zanxo da kaina sai muyin maganar, " oh ni tame gari yau nagode wa Allah habibu dama kai kake kiyaye lafiya ta ba Allah ba? Wato boko tasa zaka fara kauce hanya ko? To ni bana iya da sakarcinka ba sai da safe.

Allah ya tashemu lfy hjy iya sai na shigo, Ameen ka shigo ka gama surutanka ba abunda zai hanani zumunci sai mutuwa sai rashin lafiya, ta karasa maganar tana kashe wayar, tana mita.

Sakarcin banza da wofi wai wani zaizo da kansa saikace ubana, duk wani abu da zai hana cigaban musulmai turawan nan sun san duk wata hanya da zasu bullo da ita, suma kuma mutanenmu idanunsu Ya rufe,.. hjy iya na cikin mita taji cikinta ya karta nan da nan ya hautsine da sauri ta tashi kafin taje toilet sai ga gudawa ta farabin kafarta 🤭 typin.......✍🏼

*Vote*
*Comments*
*Share* 😎

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now