19&20

107 16 1
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
       _25/6/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
    _AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

                19&20

   Mungode kaji yaro Allah saka maka dagidan aljanna, Allah ya jikan mahaifa ya raya zuri'a, hjy iya ce ke ta zabga Addu'a tun yana amsawa daga karshe yace iya ku hawo man kunga fa dare karayi yake, nikaina yau rabon zan dauko ku ne ya tsaidani da tuni na manta da naje gida, ku hanzarta mu karsa kunsan tafiya da dare bata da dadi.

Rufe bakin me amalanken shanu keda wuya, saurayin nan yayi wuf ya d'ane kai, hjy iya saida ta kara kokartawa da kyar sannan ta samu ta kara komawa kai.

Driver da kwandasta  yanke shawarar kwana sukayi amota, wasu sauran mutum hudu suma suka amince, sauran mutum biyar acikinsu akwai dan tsoho me buhu.

Suna nan tsaye sai ga wata motar tirela ta karaso kusa dasu,  wani mutum ne ya bude tempol din saman motar  ya sauko, da 'yar jakarsa a hannu, kafin kace me mutanen nan suka zagaya ta gefe suna neman alfarma gurin driver ya taimaka ya rage musu hanya, ba musu hanya,kuwa yace su bude tempol su shiga, ko sallama basu yiwa driver da su hjy iya ba suka yi tsalle suka kama karfen jikin mota suka haye, mota ta tafi dasu ko waiwaye basayi.

Driver su hjy iya shima cen kasan wani layi, ya gangara da motarsa jikin wani gidan kallo daga dan lungu, bazakayi zaton akwai wata mota agurin ba saboda duhu.

Mutuwar tsaye dan tsoho yayi, ganin duk anwatse anbarshi agurin, wata irin kara ya kwalla cikin karaji ya zuba da gudu gangaren da ya hango su hjy iya sunyi da me amalanke, hadizatu  hadizatu Andizo dan Allah ku tsayani, kun tafi kun barni a dokar daji, wayyo Allah kar kura ta fito ta cinye ni.

Me amalanke ne ya dan tsagaita da jan akalar yace, iya wancen ba mijinki bane yake kiranki ko baki nemi izninsa ba kika hawo amalanken nan? kai yaro ina ganin mutumci da kimarka, waye mijin nawa ? Wancen tsohon to ni nan da ka ganni ba dangin iya bare na baba, haduwar mota rabuwar mota ce.

       Hadizatu magana nake fa kinmun banza dan Allah karki mun haka, gudu yake dan  tsoho buhunsa na biye dashi, duk inda yasa kafa ji kake facal-facal da ruwa har ya kusa karasowa wajen amalanken shanun.

         Maganar gaskiya iya idan kinsan za'a samu matsala ki sauka daga amalanken nan, babu yanda za'ay muna tafiya mijinki na biyo mu har mu karasa gidan me gari, kince ba mijinki bane yanxu idan muka je gidan me gari yayi kara ta wa gari ya waya, kinsan horon da me gari zai  sa ayi mun ne?

Bakin ciki ne ya cunkushe hjy iya ta kasa magana, shi kuma  dan tsoho be daina binsu yana magiya ba, wannan karan y kusa karasowa gurunsu, da karfi yake kwalla musu kira,      " kai yaro me amalanke ka tsaya mana magana fa nake ta muku, cikin kosawa me amalanke ya juya yana tambayar saurayin da suka hau da hjy iya tare,   " Abokina wai wannan tsohuwar ba matar dan tsohon nan bace gwara in tambayeka tunda tare na ganku, kar insa kaina a matsala.

            A dakile matashin saurayin ya bashi amsa, ba matarsa bace kowa tafiyarsa daban.............. Cikin azama dan tsohi ya katse musu magana,  " yauwa to na karaso dan Allah ku gyara mun in haye ciki, da ido kowannen su ya bishi ba wanda yace mai uffan , tunda ya hau yake ta zabga surutu ba kakkautawa, cikin gajiyawa saurayin nan ya kalleshi afusace yace,
                   " wallahi ko ka rufe mana baki ko inwurga ka cikin kwatamin cen, ka damu mutane da surutu kamar ka kone aka, bakinka cakwai kamar wanda akayiwa gorin magana, nan-nan dazu haka ka kusa yimun jini da majina ashe kana sani iskanci ne, kasan kana jin tsoron kurar dazu ka bamu wuya, muna janka kana janmu.

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now