Vote
and
FollowZaman tayi kamar yanda yace tana cigaba da satar kallon shi,ganin tana kallon nashi sai ya dadah yin abubuwan da zasu dauki hankalinta, ita kuwa saita kara sakankancewa da kallon nashi juyowa yayi ya kalleta yayi gyaran murya amma koh gizau batayi ba,a ranshi yace so its very easy nayita wahalar da kaina so let's play some game here
"Uuhumm"yayi gyaran muya wadan ya saka ta saurin dawowa daga yanayin data shiga tare kawar da kanta daga kallon shi cike da kunyar yanda ta kura mai ido
"Zo zauna kusa dani yau so nake naji dumin matata"ya fada yana yimata nuni da kusa dashi mamakine dai ya sake cika ta taki ta tashi taje inda yake ,ita data zo dan ya mata fada sai kuma taga akasin hakan dan tasan cewa da dade da sanin tana son Abdallah tun kan ya aureta.
Da yaga bata da niyar zuwa sai ya tashi da kanshi yaxo ya yauna a kusa da ita tare da janta a jiki ita kuwa sunne kanta tayi yace "idan bakuwar mu ta tafi sai ki shirya akwai inda nakeso muje and please kar in kara jin kin daga mata murya harta bar gidan nan ok?kanta ta daga mai ba tareda ta amsa shi ba
"Yawa so you can go fita zamuyi tare da Abdallah we will talk later"ya fada yana shafa kanta tashi tayi cike da sanyin jiki ta fita,tunda ta tashi yake kallonta yana murmushi cike da ma'anoni a zuciyarsa
Tana fita ta sauke ajiyar zuciya tare da jinginawa a jikin bagon sai data tabbatar ta daidaita natsuwarta tukuna ta koma living room ta jira mamah tazo suci abinci takai kun 30 minutes a zaune kamin ta dawo ko zama bata bari tayi tace "zo muje muci abinci"
"A koshe nake"
"Haba mana yar uwa zoman dan Allah am sorry kinji"kallonta tayi taga lallai dagaske takeyi ta tashi suka nufi dininig din.
Agurguje
Shekara daya kenan daidai da watanin babyn fuhutu biyu da haihuwa babyn mai kyaue sosai dashi wanda Aka sakawa muhammad suke ce mai(khalifah),sosai ta murje tayi kyaue abunta basa cikin wata matsala sai dai yaue da gobe akace bata bar komai ba
Zulfa'u kuwa yanzu gaba daya su fuhutu basa gabanta dan sosai khalifah yake kokarin mantar da ita son maso wani da takeyi tayi fresh tayi kyaue tana dauke da cikin wata2,wanda har yanzu ba wanda ya sani tsakanin su biyun sabida cikin bayada laulayi kamar na fuhutu,lafiya lau take zamanta da mijinta suna kokarin farantawa juna sai dai yan matsalolin da ba'a rasa ba na yaue da kullum duk wani kuduri na daukan fansa ta aje shi dadin aurenta kawai takeji dan ta lura khalifah ba baya bane.
A gurinsu jiddah bayan zuwanta Nigeria ta zaga gun yan uwa da abokan arziki hajiya da Ammi sosai suka hadata tayi bulbul,fuhutu ta kara mata wasu kayan taje dasu,tun dawowan ta calfornia bata kara komawa naija ba koh sunan muhammad (khalid) dan fuhutu bata samu taje ba mujahid kawai ne ya tafi hamidah kuwa isakancin ta kamar qaruwa ma yayi akan na da dan yanzu koh ba girkinta bane idan suna xaune a daki da mujahid sai kawai tashigo ba sallama wai magana zatai dashi ko kuma sai cikin dare tazo tana knocking kofa wai tsoro ake bata bazata iya kwana ba,abun yana damun jiddah sosai amma sai take mata kamar bata san duk plan bane take shiryawa jira take ta kaita bango su kwashi yan kallo dan wallahi bazai yuwa ba wai namiji da suna hajara(kakar tawa😦)
****************
"Hello hello"jiddah dake zaune living room din kasa taji wata na fada a bakin kofa har mai aikinsu zataje ta bude"Grace don't worry bari na duba"ta fada tana tashi ta nufi kofan tana budewa idanunta sukayi arba da wata farar yarinya rike da akwati taci kwalliya kamar zata gasar kyaue kayan jikinta bako kyan gani kafafunta duka a waje kirjinta kuwa zata iya cewa ma kamar bata saka riga ba, cikin mintunan da basu wuce uku ba jiddah ta mata wannan kallon wata irin kyamarta da tsana taji ya taso mata muryan yarinyarce ta dawo da ita daga tunanin da take
"Meye kike wani kallona sai kace kin ga sabuwar halitta dan Allah bani guri na wuce"ta fada tareda matsar da jiddah daga kan kofa ta shige ciki mamakine yasa ta kasa motsi ana nufin yar bahaushe ce tayi irin wannan shigar koh dai tana jin hausa ne kawai,bayanta tabi dan taga da wace tazo a zaune ta tadda ita hakimce kan kujera sai kace gidan ubanta ne daurewa jiddah tayi tace
"Baiwar Allah lafiya kuwa kamar fah ba nan ne gidan da kike nema ba a yatsine ta dubeta
"Da wannan tambayoyin da kike mun da kin kira mun madam din it will be better"imani ne ya kara kama jiddah,yar aiki ta dauke ni ne ko kuman yayah cike da natsuwa tana dariyar bakin ciki tace
"Nice madam din ai"
Kallon bakida hankali ta mata ba tare da tace komai ba cigaba ta kadah kafafun ta data dora daya kan dayan guri ta samu ta zauna ta kura mata ido a ranta ta kodai yaya tazo nema but tasan baya muamala da irin wayen nan matan da basuda banbanci da karuwai
"Astagafurillah"
Suna cikin zaman kuramen ne hamidah ta shigo gidan bakuwar na ganinta ta tashi cike na murna tace
"Surprise"
Hamid da bata lura da ita ba sai da tayi magana ta juyo cike da mamaki ganin wacce itama ta yada jakarta suka rugume juna.
"Wlh kinyi surprising dina sosai am so happy"
Hamida ta fada cike da farin ciki bayan sun gama tsalle tsallen su itama yarinyar tace
"Dama na san zakiyi farin ciki sisto"
"Sisto kuma?tana nufi kanwar hamidah ce ita kan uban...."ai kuwa da matsala wlh dan ba zata zauna gidan nan ba"jiddah ta fada a ranta kamar a mafalki taji hamidah tace
"Let's go in na san kin gaji but meyasa baki shiga ciki ba kika zauna a living room keda gidan yayarki sai kace wata bakuwa" ba musu taja trolley dinta ita kuma hamidah ta dauki jakarta dake kasa suka nufi upstairs,kamar walkiya jiddah tasha gaban su ta tare hanya,kallon sama da kasa take masu cike da isah tace
"Ba inda zaku"
Sakato hanidah tayi cike da mamaki ta maimaita "ba inda zaku? Cikin sigar tambaya kauda kai jiddah tayi ba tare data amsa mata ba dan tasan ai she knows that dasu take toh meye abun tambaya kuma a zuciye hamidah tace
"Ke karamar karuwa bangane me kike nufi ba"
"Izuwa yanzu ya kamata ki gane waye karuwa a cikin mu idan kika kalli wadda take gefenki dan a zuri'ar mu bamu masu irin zubunta balle dabiunta,kinga kuwa idan karuwanci ne ai kinfi kusanci dashi dan naga allamun rugumarshi ma kikayi kika maidashi abun alfaharin ki,maganar baki gane ba kuma ki tambayi babbar karuwa dan naga kamar ta fiki fahimta"jiddah ta fada cike da shakiyanci
Mamaki ne ya kusan kashe hamidah a tsaye "ashe haka yarinyar take da mugun baki?bata taba zaton zata iya mayar da magana haka ba yanda take ta mata abubuwa bata tankawa wato kan mage ya waye "da kyaue"dama haka take so.
"Ni kike zagi"ta fada tana nuna kanta da dan yatsa jiddah tace
"Aa nikam rufa mun asiri umar gida sarautar mata nina isa na zageki ne,kawai da amsar da tambayarki na baki"
Duk maganar nan da jiddah keyi ba allamu fushi koh bacin rain a tattare da ita,cike da kwanciyar hankali take abubuwan ta,muryar hamidah kawai kakeji a sama kamar engine markade sai kace ba mace ba,yarinyar da bamu san sunanta ba har yanzu ce ta rikewa jiddah riga zata zabga mata mari sukaji ance
"Karki kuskura koda wasa hannunki ya taba fuskanta idan ba haka ba zan maki jibgar da za'a rasa mai daure maki kashi duk fadin California"
Hannunta ya kage kan iska ita bata mareta ba,bata kuma sauke hannunta ba cike da mamakin wacece tayi wannan maganar,jiddah kuwa farin ciki ne yazo mata lokacin kamar an tsundumata a aljanna.
*******************
Wace ce?wa kuke tunaniBarkan ku da sallah
Ayita hakuri
Vote
And
FollowMrs umar
Jazakallahu khairan
YOU ARE READING
Fuhutulkhairi
Short Story"Jiddah kin san Allah tafiya zanyi na barki a nan gurin"a yanda tayi maganar zaka fahimci cewa akwai gajiya a jikinta "Ki bari nazo mana report din mu fah nake submitting kin san cewa idan ba muyi ba wlh zai iya bamu carry over ba imani ne dashi ba"...