*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*YESMEEN*
*© Ummyn Yusrah*
Cikin shirin tafiya Hanifa ta shigo gidan, sanye take da riga da wandon da ke bayyanar da duk wani sura na jikinta, sai abayan da ta ɗaura a kai, wanda bai da maraba da rariyar tata, tsinin takalminta ko, kamar cokali.
Kai tsaye ɗakin Gwaggo Habi ta shige, ba tare da ta yi wa mutanen gidan da ke zaune a falon magana ba.
A shirye cikin atamfa riga da zani, da gyale mai ɗan girma, ta sami Yesmeen. Kallon Yesmeen ɗin ta yi, sama da ƙasa, ta ce,
"Ke wallahi har yanzu ba ki waye ba, kamat ba girman Jos ba da ake yi wa kirari da tushen wanka?"
Kallon mamaki Yesmeen ta yi mata,
"Ban fahimceki ba? Wacce irin wayewa kike so in yi?"
Ƙarasowa ta yi kusa da ita,
"Kalla fa! Atamfa kika sa."
Baki buɗe ta ce,
"Idan ban sa atamfar ba tsirara kike so in fita?"
"Ni ban ce ba, ki yi irin shigar da na yi mana, sai mu fi haskawa."
Baki Yesmeen ta taɓe,
"Yo, wannan shigar taki, ai bai da maraba da tsirarar. Tukunna ma, gidan rawa za mu je ko gidan biki?""Duk biyu, kin wani ɗau atamfa kin saka habba! Ai sai ki ban kunya."
"Tooow! Shigar tawa ce ba ta yi ba kome?"
"Eh. Don Allah mu je gida in baki wasu irin nawa kisa."
Baki Yesmeen ta taɓe,
"Allah sauwaƙamin. Zuwan ba dole ba ne, za ki iya tafiya ke ɗaya."Buɗe baki ta yi da niyyar ta ba ta amsa, maganar Gwaggo Habi ya katseta.
"Wai ku me kuka yi ne a ɗaki har yanzu kun kasa fitowa, so kuke ku yi dare ko?"
"Ga mu nan fitowa." Hanifa ta ba ta amsa.
Fitowa suka yi suna hira, da dariya kamar ba yanzu suka gama rigima ba.
Ƴan gidan sai bin su suke da kallo ana maganganu ƙasa-ƙasa.
Suna fitowa Hanifa ta ce,
"Ɗan jira in shiga gida in ɗauko aika sai mu wuce."
"Ki sauri karki daɗe."
Ba ta jima ba ta fito, hannunta ɗauke da wani ɗann madaidaicin jaka.
"Mu je ko?" Ba tare da amsa ba suka wuce zuwa bakin hanya.
Adaidaita suka shiga Hanifa ta ce,
"Malam Fadamar mada zaka kai mu, gaba kaɗan da asibitin Alwadata."
Ciniki suka yi ya kwashesu, lokacin da suka zo wucewa wajen Makarantar kwana ta G.G.BAUCHI, Yesmeen ji ta yi kamar ta shiga, amma haka aka wuce.
Da sallama suka shiga gidan, cikin fara'a da sakin fuska wata matashiyar budurwa ta fito ta tarbesu.
"Snnunku da zuwa ku shigo."
Ta ce, tana yi musu iso zuwa wani babban falo.
Ba su jima da zama ba, wata budurwar da ta ɗan ɗara wa ta farkon shekaru ta shigo, ta na yi musu barka da zuwa.Ba jimawa aka fara shigo musu da kayan abinci da na sha, ga kuma girmamawar da ake ta yi musu. Yesmeen dai ta zama ƴar kallo, domin abun ya ɗaure mata kai, tunda suka zo ba ta ga matar gidan ko ɗaya ba, sai tarin yaran gidan da ke ta kai kawo, masu kama ɗaya wanda ta rasa ina ta san kamannin.
Hanifa kam ta ware sai hira suke sha.
Wajen k'arfe uku da rabi budurwar mai suna Salma ta ce,"Na kai muku ruwan wanka, ku shirya zuwa k'arfe hud'u za'a tafi."
Yesmeen ta yi saurin ce wa,
"Wanka kuma? ai mun riga mun yi wanka tun a gida."
Hanifa ta ce,
"Mun gode Aunty Salma."
Hanifa ce ta fara shiga, ni kam, shiga na yi kaiwa na gyara kai na kasantuwar ina fashin sallah.
Ina fitowa na tadda Hanifa ta sha ƙwalliya, ta sake canza shiga da wasu riga da wando. Baki kawai na saki ina kallonta, yayin da tun ɗazu zuciyata ke riƙe da tambayoyi kala-kala.
"Ga shi ki sanya tunda kinƙi ki yi wankan." Ta yi saurin katsemin tunani. Riga da wando ta miƙomin wanda ko gwiwata ba zai rufe ba idan na sa, tsabar takaici ban san lokacin da na wurga mata rigar ba, cikin ɓacin rai na ce,
"Evening show za mu fita ko me? In da ina da buƙatar yin shiga irin wannan, da tun a gida gaban iyayena zan yi, tunda ko ban yi a gaban nasu ba, banga dalilin da zan yi a bayan idonsu ba, idan ba su ganina, Allah na gani na."
Kwashe kayan ta yi ba tare da ta ce komai ba, sauƙin ta ma ba kowa a ɗakin sai su biyu. Ƙiransu a ka yi su fito ana jiransu a waje.
Godiya sosai suka yi, motar da Yesmeen ta gani shi ya sa ta faɗuwar gaba, motar abokin saurayin Hanifa ne.
Sai yanzu ta gane ƴan gidan da abokin saurayin suke kama.
'Tirƙashi! Dama gidan saurayi ta kawosu?' Ta faɗi a zuci,
Ranta kuwa in ya yi dubu ya ɓaci, har suka shiga ba wacce ta yi magana, sai ma Hanifa da ke ta shan hira da mai motan.Ba bu zame ko ina ba sai makarantar sojoji da ke cikin bariki, daidai ƙofar wani babban ɗakin taro ya tsai da motar, tun daga ƙofa ƙofar wajen wani mahaukacin sautin kiɗa ke tashi. Hafiz na sauƙesu ya abunshi, Hanifa da saurayinta Adam riƙe da hannun juna, Yesmeen na biye da su har cikin.
Wajen cike yake da ƴammata da maza, musulmai da chirista. Sai dai ko abu ne mawuyaci ka iya bambance wace Saratu wace Sarah ba, duk shigar ɗaya ne, sai rungememeniya ake tare da taka rawa. Wasu a gefe sai shaye-shayen kayan maye suke ta yi.
Wasu zafafan hawaye ne, ya sauƙo daga cikin idanuwanta ya gangaro zuwa ƙuncinta.
'Ashe akwai masu walwala da nishaɗi haka? Akwai mutanen da ke ta more rayuwarsu ba tare da tunani ko tausawa ƴan uwanta da faɗa ya yi silar mutuwar iyaye, ƴaƴa, yayye, ƙanne ko ƴan uwa ba? Allah sarki! Kenan idan abu ya sameka a yanzu kai ɗaya ya shafa, ba wani mai tayaka kuka da alhinin abin da ya faru da kai. Allah sarki! Ko yanzu ina ƴan uwanta da ke cikin wani yanayi? Wani irin rayuwa suke fuskanta? Wa ke tallafa musu? Wani muhalli suke kwana? Sau nawa suke ci a rana? Rayuwa kenan!' Cikin sauri ta fice daga cikin waje, nesa can ta koma tana tunanin ta ina za ta fara? Ya ya za ta yi ta koma gida a yanzu?
Ta jima tsaye a wajen, tana tufka da warwara, ba ta ankara ba ta ji, an riƙo ƙugunta tare da faɗin,
"Kyakkyawar yarinya ke ba zaki shiga a yi rawar da ke ba ne?
Wani irin faɗuwar gaba ta ji, cikin zafin nama ta juyo ta hankaɗeshi, tare da sauƙe mishi wani lafiyayyen mari.
*2020*