6

37 3 0
                                    

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

        *YESMEEN*

       *Ummyn Yusrah*

                 _6_

Mutanen da ke wajen duk suka juyo don ganin abi da ke faruwa.

Wata daga gefe ta ce,

"Kai! yau Gentle  aka wa wanna marin? tashin hankali."

Da gudu ta garzaya ɗakin taron  don isar da abin da ke faruwa a waje.

Cikin masifar da ba ta taɓa sanin tana da shi ba, ta fara zazzagamar masifa,

"Don tsabar iskanci uban wa ya baka izinin tab'amin jiki?  Kai waye cikin muharramaina da har zaka kai hannunka jikina? Ce maka aka yi ni ɗin tambaɗaɗɗiya, mara kamun kai ra rashin sanin darajar jikinta ne kamar sauran ƴammatan da kuka saba riƙewa? Idan ba tsautsayi ba, me zai kawo ni wajen nan. Kun mai da taɓa jikin mata, tamkar wani sabon salon wayewa, babu wani burgewa cikin hakan sai zubewar kima da daraja. Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi sai Allah ya saka min." Ta ƙarashe maganar tana kuka mai ciwo da takaicin abin da ya yi mata.

Waje ya gama cikewa da mutane, a daidai nan Hanifa ta iso ita ma, ganin Yesmeen tsaye na masifa gami da kuka ya sa ta nufo ta, hannu ta daga mata,
"Kada ki kuskura ki iso gareni! Kin ha inceni, dalilinki wani ƙaton banza ya kai ƙazamin hannunshi jikina. Dubi yadda wasu ƙattin maza ke rirriƙeku da shafeku, ku a hakan wayewa ne da burgewa, kuna tunanin duk namijin da ya yi muku haka zai so ya aureku ku zame mishi uwa ko ka zame mata uba ne ga ƴaƴaƴen da za ku haifa? Kun yi kuskure, wannan ba wayewa ba ce wallahi, duk abin da namiji ya yi ado ne, ke mace me ye ado a wajenki? Da wani ido za ki ɗaga ki kalleshi duk ranar da kuka haɗu a wani waje na daban, da auren wani a kanki ba shi ba? Ki tuna, wacce irin takaici za ki yi a lokacin da taɓa sassan jikinki da ya yi a baya? Da yawanmu nan, na sani ha intar iyayenmu muka yi ta hanyar zuwa nan ba tare da saninsu ba, ya ya za ki ji a nan gaba idan kika kama ɗiyarki da wannan kalar ha'incin da ke kika yi wa naki iyayen? Kada ku manta, duk abin da ka yi sai an yi maka."

Sake kallon Hanifa ta yi, kallon da ke nuni da tsantsar tsana, ta yi kwafa ta wuce.
Gabaɗaya wajen ya kaure da tafi da ihun,
"Allahu akbar malama."
Yayin da da yawa suka koma ciki suna mamakin yadda aka yi, yarinyar ta kwashi banza ba tare da Gentle ya ɗau wani mataki a kanta ba, sanin da suka yi mishi na ba mai taɓashi ya zauna lafiya.

Tsantsar takaici da baƙin ciki ne ya sanya shi ɗaukar mataki akan lokaci, bai yi aune ba, sai hango bayanta ya yi tana tafiya. Sanin da ya yi cewar kowa jira yake ya ga hukuncin da zai ɗauka, kawai sai ya saki wani shu umin murmushin da shi kaɗai ya san ma anarshi.

Hannunshi na dama ya ɗaga sama, ya kaɗa makullin motarshi da ke ƴar yatsarshi manuniya, ya ce,
"Gayu! A ci gaba da harƙa kawai, ba yawa." Duk suka ɗau sowa, suka yi ciki, amma fa banda wanda maganar Yesmeen ta fara tasiri a zukatansu, shirin tafiya gida ma suka fara yi.

Adam ya kalli Hanifa ya ce,

"Wai ina kika kwaso mana wannan ƴar ƙauyen ne?"

"Ƴar ƙauye fa ka ce?" Ta yi tambayar tana yi mishi kallon mamaki

"Yesmeen ɗin ce ba ka sani ba ko me?"

"Idan nasanta sai me? Ba ki faɗa mata inda za ki zo ba ne?"
Ya tambayeta cikin ɓacin rai, ya juya zai koma ciki, "Duk ta ɓata mana show, yadda mu ka ci burin chashewa, da kwasar garar y'an mata duk ya tashi a banza." Ya yi maganar ne ba tare da sanin ta ji shi ba.

"Owo!Kuna nufin a kanmu kenan za ku kwashi garar? Ta Allah ba taku ba wallahi, kuma wallahi da sai na gwada maka cewar ni cikakkiyar girman bariki ne a yau, ka sani duk bibiyar club ɗina, ban taɓa ba wani ɗa namiji damar da zai keramin mutunci ba. Na jera da manyan ƙwarin da suka fika wallahi, ba ka isa ka ɗau komai daga gareni ba. Ka sani, zan iya ɗaukar komai, amma kada ka sake ka sanya Yesmeen ciki, domin a kanta sai inda ƙarfina ya ƙare."

Haka suka rabu baram-baram, ta kwashi shirginta ta yi gaba.

Can nesa ta hango Yesmeen, lokacin gari ya fara duhu, sauri-sauri gudu-gudu ta iso gareta, ta ce,

"Don Allah ki yi haƙuri ƴar uwa. da na san hakan zai faru koda wasa ba zan fara gaiyatoki ba, Don Allah kimin afwa na tuba."

Kallonta ta yi ba tare da ta ce komai ba, adaidaita suka shiga, har suka iso gida ba wanda ya yi magana, suna sauka ta shige gida, Hanifa na sallamar mai adaidaita ta juyo ta ga ba ta nan.

Ji ta yi kamar ta bita, sai kuma ta fasa za ta ba ta lokaci har ta huce.

Lokacin da ta dawo Gwaggo Habi  ta ga duk yanayinta ya canza, tambayarta ta yi,

"Me ya faruwa? Faɗan da kuka saba kuka yi da ƙawar taki ko?"
Kai ta girgiza, sai kuma hawaye ya gangaro mata, ta so ta ɓoye, sai kuma ta ga ba riba, ƙarya kuma ba ɗabi arta ba ne, hakan ya sa ta sanar da ita duk abin da ya faru. Gwaggo Habi  ta ce,

"Amma bai kamata ku rabu haka ba, idan kin ga mutum ya kauce ƙoƙari za ki, ki saitashi bisa hanya  ba ki bar shi ya cigaba da gurɓatacciyar rayuwa ba."

"Haka ne, raina ne kawai ya ɓaci."

"Ka da ki manta, Hanifa mai son mu CE, ba ta da wani mummunan hali, duk abin da take a cikin gidannan tana yi ne don jin haushin abin da ake mana ba don rashin tarbiya ba. Yanayin shigarta kuma, a hankali za ta daina tunda cikin barikin sojoji ta taso cikin garin Lagos, dole yanayinta ya bambanta da mu. Kada ki manta, da taimakon mahaifinta na sami zuwa Jos na ɗaukoki, ki yi haƙuri ku daidaita, ki kuma riƙa yi mata nuni da abin da ya dace, ki kuma cigaba da tsare mutuncinki."

"In sha Allah Ummanah." Ta faɗa tana murmushi, haɗi da goge idanuwanta.

Ita ma murmushin ta yi na jin daɗin ƙiranta da Umman da ta yi.

*2020*

YESMEENWhere stories live. Discover now