27&28

89 17 0
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
       _5/7/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
    _AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

                27&28

Tun daga sama har kasa maahe ya tsaya yana karewa Dr tanimu kallon mamaki, wata shiga ya ganshi da ita da bai taba gani ba, riga me hade da wando ce ajikin sa na buhu ga wani kwabcecen takalmi akafarsa fuskarsa ya nade ta da wani farin kyalle hannuwan sa sanye da safa daga sama an kara buhu annade shi, hannunsa ne rike da zabgegen tiyo, nalami na rike da wani inji irin wanda ake yin ban ruwa dashi a gona, muta'kka da idi sun karaso da wata amalanke andora mata garwa manya-manya guda hudu kowacce cike take da wani irin ruwa me wani irin launin kala.

        Dr tanimu lafiya naganku haka kamar masu shirin zuwa yaki anya lafiyarku kuwa, maahe ya fada yana karewa su muttaka kallo da suke ta hidima da amalanke, lafiya klau agajin gaggawa ne muka kawo muku nida su nalami, ina megarin yake................. Wai maahe su waye ne najika kuna magana dasu kuma maganar taki ta kare, matar me gari ce ta katse musu maganar da sukeyi lokacin da ta leko.

Washe baki ta shiga yi cikin farin ciki take fadin au Dafta tanimu ne barkanka da zuwa likita bokan turai, yauwa inna ayi mana sallama da me gari inasan magana dashi, tun kan dr tanimu ya rufe baki megari ya dingiso yana fadin waye yake nema na gani nazo ina fatan dai lafiya.

Au dan nema ka kara zuwa ka cimun mutumci ne har gida tunda yanxu naga harda mukarrabanka ka taho , shi ne duk kuka toshe hanci ko, to mungode basai kun kara dizgamu ba wanda ka mun daxu ma nagode kai maahe ke wuce muje ci............ Dr tanimu katse me gari yayi da, Allah ya baka yawan rai taimako ne mukaxo kawo muku game da ita wannan cuta da kuke da ita, nalami yaje ya same da maganar cewar abokinsa ya gaya masa wadansu abubuwa da ake hadawa a gargajiyance,  wanda kuma yace acen gurinsu angwada kuma cikin ikon Allah ansami nasara, da farko ban gasgata maganar ba sai da nayi waya da wadanda aka gwada musu kuma suka warke, kuma sai da na duba naga shin idan anyi amfani dasu babu wata illah da zatayi wa mutum, sannan a likitance nayi wani bincike na gano wadansu magunguna da idan na hada na baku za'a samu waraka, akarshe ina neman gafarar me gari bisa kuskuren da nayi ayafemun na tuba sharrin shaidan ne da kuma firgici domin lokacin ina cikin firgici da tashin hankali.

   Ajiyar zuciya megari ya sauke, sannan yace, duk naji bayanan ka kuma na gamsu sai dai baka yimana bayanin irin magungunan ba, da yanda za'a saraffa su, kuma su wadannan rigunan buhun da kuka sassaka maganin me sukeyi sannan ta kan wa za'a fara gwajin maganin?

Gwajin magani ay ba wani abun damuwa bane Allah ya baka yawan rai, ko da kai ay sai a fara gwadawa, su kuma rigunan nan daxu nasa yakubu ya dindinka mana su sune suke bada kariya ga wadanda basu da wannan cutar, su likitoci a birni ba irinta suke sawa ba amma nan tunda bamuda irinsu sai na yanke shawarar bari na sa a dinka ma buhunhuna (🤣 _chaiii tanimu wai kuwa dr gaske ne_🙄).

     Sannan sukuma magungunan gasu zan maka bayaninsu.

Wancen katon buhun dake hannun idi ni'ka'kken rogo  ne wanda aka hadashi da tafarnuwa da kajiji sai dan kaninfari da aka kara dashi kadan.

Waccen amalanken shanun kuma garwoyin cen da kuke gani ruwan tafarnuwa wanda aka hada da ganyen rai dore ne, sai alimun da dan tsami da karin dan gishiri aciki, za'a dauki garwa daya a tafasa shi sai axuxubawa kowannen ku yayi sirace da shi, sauran garwa ukun da suka rage kunga wancen injin na hannun nalami za kunna shi ajonashi, sai nad'e muku idanunku da wani kyallen saboda kar afara yi muku feshi ya shiga ido.
Ita kuma wannan tafarnuwar zaku dinga bare ta kamar cikin murfin buta kuna hadiya ba'a tauna ta hadiya zakuyi da ruwa.

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now