*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*YESMEEN*
© *Ummyn Yusrah*
*7*
Haka nan rayuwa ta ci gaba da tafiya wa su Yesmeen, yau zuma gobe maɗaci, daga dangin mijin Gwaggo Habi, kishiyarta Hajiya Talatu da ƴaƴanta.
Fitowa ta yi da sauri da nufin shiga kitchen don ta ji kamar miyarta na kamawa, cikin rashin kula ta ji ta yi karo da abu, ɗagowar da ta yi da niyyar magana ta yi ido biyu da Hajiya Talatu ta buɗe baki
cikin yanayi na masifa ta ce
"Tooow! Muguwa, ƴar baƙin ciki, shi ne kika taho a guje don ki bangajeni, don baƙin ciki, cikin da ke jikina ya zube ko? Ta Allah ba taki ba wallahi, ke da haihuwa sai dai kiga ana yi, mun yi na biyar ga na shida yana tafe, bayanshi akwai wasu masu zuwa ma, Bibalo." Ta ƙarashe maganar, tana shafe cikinta da hannunta na dama.Wani irin abu ne mai ciwo ya doki zuciyar Gwaggo Habi, na gorin haihuwar da kishiyar tata Hajiya Talatu ta yi mata, ta ce,
"Don Allah ki yi haƙuri ba da niyya na buge ki ba, sallah na shiga, jin ƙaurin miya, ya sa na fito da sauri, ki yi haƙuri."
Sallama suka ji daga ƙofar falon, da sauri Hajiya Talatu ta durƙushe gurin, hannunta riƙe da ciki, tare da bubbuga ɗaya hannun bisa cinyarta, ta fara yamutsa fuska ta fara rintse idanuwanta, tamkar mai naƙuda.
Gwaggo Habi ce ta ta amsa sallamar tare da yi wa mai sallamar barka da zuwa. Sai dai ko kaɗan ba ta bi ta kanta ba, da sauri ta isa wajen da Hajiya Talatun ke durƙushe, ta fara tambayarta,
"Talatu me ke faruwane? Ko haihuwar ce ta zo, wannan baƙar dagar ta tasaki gaba ba tare da taimakon komai ba? Kodayake ba sanin ciwon abun aka yi ba."
Cikin muryar wahala ta ce,
"Dokemin ciki ta yi."
"Kamar ya ya ta doke miki ciki? Karo kuka yi ko ganganci da mugunta, da haushin rashi?"
Baƙuwar ta sake tambaya."Ina ɗaki na ji miya na kamawa a kitchen, shi ne na zo na duba, na fito zan koma ɗaki, daidai Habiba ta fito ta nufoni gadan-gadan ta gulleni a cikina."
"ita Habiban!?"
"Eh,wai don me ya sa zan taɓa mata girki alhalin nasan ba ranar girki na ba ne." Ta faɗa tana cije laɓɓan bakinta, da riƙe bayanta.
"To, mugunyar halinki ya biki, duk baƙin ciki da tsiyarki sai jikana ya fito duniya, ba ki haifa ba kuma kina yi wa mai haihuwa baƙin ciki. Sannu Talatu! Tashi mu je asibiti a duba ki, idan wani abu ya sameki da ɗan cikinki, yau sai ta bar gidan nan."
Cikin yanayi na damuwa Gwaggo Habi ta ce, "Wallahi ba da gangan na bugeta ba Haj..."
"Rufemin baki, tunda ta sami cikin nan kike baƙin ciki, Za mu je a duba ta, kuma Wallahi ina ƙara faɗa miki akasami wani abu a bakin aurenki."
Tana kaiwa nan, ta hau kiciniyar kama Hajiya Talatu da ke zube kamar kayan wanki.Har ɗaki ta tafi ta ɗauko mata hijabi ta sanya mata suka yi waje, Gwaggo Habi ta juya za ta nufi kicin, jiri ya kwasheta ta zube nan ƙasa tim!
Tana kaiwa ƙasa Yesmeen na shigowa hannunta riƙe da ledar aikan da ta dawo da shi. Ganin Gwaggon nata zube a ƙasa ya sa ta yi wurgi da aiken ta isa gareta da gudu."Umma lafiya? Me ya sameki?" Ta faɗa idanuwanta na shirin zubar da ƙwalla.
"Ba komai Yesmeen! jiri ne ya kwasheni, taimakamin in tashi."
"To, sannu!" Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga ta, nauyin da take da shi, ya sa ta kasa koda matsar da ita daga inda take. Ga shi ba wanda zai taimaka mata duk gidan.Da gudu ta fita ta yi gidansu Hanifa, rabon da su haɗu tun randa abun nan ya faru.
Har ƙasa ta ɗurƙusa ta gaida Mommy gami da tambayarta ko Hanifa ta na nan."Ta na ciki. Ya ya jikin naki? Ta ce ba ki da lafiya kwana biyu, ban sami zama ba shi ya sa ban shigo na duba ki ba."
"Jiki ya yi sauƙi sosai."
Ta faɗa tana jinjina ƙaryar da Hanifa ta yanka wa Mommy nata.
"Toh Allah k'ara afwa.""Ameen." Ta amsa tare da mikewa ta nufi ɗakin Hanifan.
Tana ganin Yesmeen, ta ji wani daɗi da farin ciki."Don Allah idan ba kya komai zo ki tayani wani aiki kaɗan." Yesmeen ta faɗa.
"Lahh! ba na komai, dama kwanciya zan yi mu je." Ta faɗa cikin zaƙuwa
Gidan suka nufa da sauri, yadda a ta bar ta nan ta sameta, ga su Rukky da ƙannenta biyu zaune a falon ba wanda ya kulata.
Suna kiciniyar ɗagata sai ga Zarah, ɗaya daga cikin yaran gidan ta fito hannunta ɗauke da ruwa, ta nufo gurinsu Yesmeen ta ce,
"Aunty Yesmeen ga ruwan. Aunty ce ta ce in ɗebo mata, za ta sha, na ce ta tashi, wai ba za ta iya ba." Ta na maganar ne tare da mika wa Yesmeen kofin ruwan da ke hannunta.
"Eh, Zahra jiri take ji." Ruwan ta ba ta ta sha, sannan suka taru su ukun suka ɗaga ta.
Har gado suka kai ta, sannan ta kwanta ko zuwa anjima za ta ji daidai. Sannan Yesmeen ta karasa girkin ita da Hanifar, duk da ba wani sakin fuska sosai ta samu daga Yesmeen din ba.
Sai wajen ƙarfe biyar na yammaci ƴan asibiti suka dawo, Hajiya Talatu ras! da ita, kamar ba ita ce ɗazu ke ta lanƙwashe-lanƙwashe ba.
Su Ruky suka tarar zaune an tasa tibi a gaba, wanda ko ƙuda ba su fatan ya gibta ta gaban kallon. Batun sallah kuwa, ba a magana, dama daga sallar asuba sai na magrib suka fi yi, kallo shi ya zame masu tamkar ibada.
Hajiya ta ce,
"Ina Biban ne ta ji mun dawo don baƙin hali ba za ta fito ta duba mu ba?"Zahra data fito daga ɗaki ta ce,
"Sannunku da dawowa. Aunty na ɗaki kwance ba ta jin daɗi ne.""Ƙarya take yi, ba wani rashin lafiya munafurci ne kawai, don na ce idan wani abu ya sami surukata da jikana a bakin aurenta shi ne bari ta kwanta ciwon ƙarya ko?"
Zarah ta kalleta cikin yanayi na rashin jin daɗin maganar kakan tasu, ta rasa laifin da Auntyn tasu ta yi mata, da ta tsaneta haka. A matsayinta na mahaifiyar miji, hakan tamkar zubewar mutunci ne ai a gareta."Hajiya rabu da ita, wani sabon salon munafurci ne." Cewar Hajiya Talatu, yayin da take shirin zama kan kujera.
Baki Hajiyar ta taɓe, ta ce,
"Koma mene ne, ita dai ta sani. Allah ya taimaketa ba abin da ya sameku."*2020*