9

89 3 1
                                    

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

      *YESMEEN*

     © *Ummyn Yusrah*

     *9*

Kokawar yadda za ta kwaci kanta take, shi kuma ƙoƙari yake ya cika birinshi, cikin ikon Allah! Aka buɗe ƙofar gate ɗin alamun shigowa, da sauri ya sa keta ya na ciza yatsa ya ce,

     "Idan kere na yawo, zabuwa na yawo, wata rana za su haɗu ne."

Ta yi saurin buɗe ƙofar falon ta shiga, sannan ta leƙo da kanta ta ce, "In Sha Allahu sai dai su yi kyakkyawar gano, ba gamon tsiya ba. Aniyarka ta bika, Allah kuma ya yi min tsari da mummunan nufinka. Ta na kawai nan ta yi saurin shigewa ciki, shi kuma ya wayance kamar wanda ya fito daga ciki. Ruky na ganinshi ta ce,

    "Ah! Yaya ba kai barci ba ne?"

    cikin yanayi na jin haushi ya ce,

   "Ban yi ba ƴar iska, jiranki nake, kin san tsoho ya ba ni aikin gadi, idan kun gama shigowa daga yawon la tazubar ɗinku in rufe mishi gida, tunda shi ba ya gari.

harararshi ta yi cikin duhu ta ce,

"Kai ma yauɗin ai sa'a a ka ci ka dawo gida da wuri, gara ni ba na wuce ƙofar gida."
Fizge ledodin hannunta ya yi, ya shiga dubawa yana faɗin, "Banza ta samu bari mu ɗebi ganima. A shiga tsohuwa na ciki tana gyangyaɗin zaman jira." Iya wuya ta kai wajen jin haushi, ta ce, "Da haka ka riƙe duka mana kawai."
"Abu mai sauƙi." Ya faɗa yana gyara riƙon hanun ledar zai tafi.
Kamoshi ta yi ta na faɗin, "In na yarda Allah ya tsinemin, wannan shi ne kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Ni da shan sanyin waje kai da kwashe ledodi. Sannu! Wallahi ka ban, ko in je in faɗa wa Hajiya." Ta ƙare maganar tana kokawar ƙwacewa. Sakar mata ya yi ya juya, ya ce, "Na kwashi rabona, idan kin shiga ki duba wutan nan, ganin duhun wajen ya sa na fito dubawa."

"Wallahi ba zan duba ba." Ta yi shigewarta, ya dawo ya kunna. Dama ya kashe ne don ya ji daɗin ritsa Yesmeen, sai dai Allah bai ba shi sa a ba.

A hankali ta shiga ɗakinan tare da sanya wa ɗakin makullin, don gani take zai sake biyota, ga gabanta sai lugude yake, tunaninta ɗaya ƙaryar da za ta yi wa Gwaggo idan ta tambayeta musabbabin daɗewarta.

Hamdala ta yi ganin ta yi barci, da alama kuma maganin barcin da ta sha ne ya fara aiki. Waje ta samu itama ta kwanta tare da addu'ar neman tsari dakuma fatan kar Allah ya ba Yaya Sani galaba a kanta.

Juyi kawai take sam! barci ya ƙi ɗaukarta, alwala ta je ta ɗauro ta zo ta fara jero nafila don kai wa Allahu kukanta.

Sai da ta yi sallar asuba ta kwanta, lokacin zuciyarta ta sami natsuwa.

Sai kusan ƙarfe bakwai daidai Gwaggo Habi ta tashi,tana mamakin irin nisan barcin da ta yi, sosai ta ji daɗin jikinta, yanzu ba jiri sai rashin ƙarfin jiki da ɗan ciwon kai.

Motsin da Yesmeen ta ji ne ya sa ta buɗe idanuwanta, gami da tashi zaune tana faɗin,

    "Umma kin tashi ne?"

"Eh, bayan kin ƙi tashina in yi sallah akan lokaci."

"A'ah! Ba ƙi na yi ba, gani na yi kin sha magani nasan kuma shi ya sa ki barci, kar in ta sheki in ƙara miki ciwon kai shi ya sa."

"Na ji daɗin barcin kuwa, don yanzu jikin da sauƙi sosai." Ta ba ta amsa

"Allah ya ƙara sauƙi Ummana!"
Ta faɗa fuskarta na bayyanar da murmushi
   "Ameen." Ta amsa tana maida mata da murmushin, don a rahiri ba ƙaramin daɗin Umman nan take ji ba. Ita ma Yesmeen ɗin tunda ta fahimci haka, sai take ƙiranta da shi.

"Barin sa miki ruwan wanka idan kin yi za ki ɗan ji ƙarfin jikin." Yesmeen ta ce lokacin da ta nufi hanyar banɗakin.

"Ai ko da kin kyauta.
Allah miki albarka."

     "Ameen Ummana."

Kafin ta fito wanka, ta gyara ɗakin tsaf! Ta ciro mata doguwa riga mara nauyi ta shimfiɗa mata sallaya,  sannan ta fita. Gabanta sai dukan uku-uku yake, addu'arta ɗaya kar Allah ya sake haɗata da Yaya Sani.

Duk wayewar gari sai ta je ta gaida Hajiya Talatu koda kuwa ba za ta amsa ba, ta dai yi.

Kicin ta nufa ɗauko musu abun karyawarsu, ba kowa ciki sai Zarah da take ta aiki, dama duk ranar girkin Hajiya Talatun ita ke yi, domin duk cikin yaran ta fita daban. Ganin Yesmeen ta shigo ta ce,

    "Aunty Yesmeen ya jikin Aunty?"

Dariya Yesmeen ta yi l, ta ce,

"Zarah ba ko gaisuwa sai tambayar jikin Aunty?"

Rufe bakinta ta yi, ta ce,
"Allah na damune, jiya ban iya barciba, ga shi tun ɗazu Hajiya na falo taƙi shiga ciki balle in shaga in dubata."
Ta faɗi kamar mai shirin rushewa kuka.

"Kada ki damu Zahrah! Aunty ta ji sauƙi, yanzu ma wanka ta shiga."

"Allah ƙara mata lafiya. Ga abun karyawarku tun ɗazu na gama."

"Sannu da aiki, mun gode."

Ɗauka ta yi, ta nufi ɗaki, ta samu Har Ummah tayi Sallah, tana zaune.

Bayan sun gama karyawa ta shiga wanka, lokacin da ta fito ta tadda Hanifa da Mommynta sun zo gaida Umman. Bayan tafiyarsu ne, ta sanarwa Umman saƙon Hajiya Amira, kan ba za ta sami zuwa da safe ba, sai zuwa yammaci, sakamakon ƙiran gaggawa da ta samu daga asibiti, ta ce a sayo sauran magungunan da ba a samu ba jiya.

Kuɗin maganin ta ba ta, ta ce, ta je
ɗakin sai da magani na Sha ka tafi da ke wajen kasuwan Central, nan za ta samu duka.

Tafiya take amma jikinta ya ba ta tabbas yana waje, tambayar kanta take

'Me ya sa duk inda yake in dai ta doshi wajen sai jikinta ya bata? Me ya sa ba ta jin hakan ga sauran mutane sai shi kad'ai? Wai meke faruwa da ita ne? Me ya...'
Sallamar da aka yi ta bayanta, shi ya yi silar katsewar tunanin nata. Da sauri ta juyo don ganin mamakin wannan murya.

Cak! Numfashinta tsaya na ɗan lokaci, yayin da shi kuma ke ta doka murmushi.
Magana ya fara yi, tare da ɗaga gira.

"Ba magana? Dama ji na yi kina ta ƙirana, na zo kuma ashe kunnena ne be ji da kyau ba."

"Am... Um... Am..." Ta shiga in ina na rashin sanin abin da za ta faɗa.
Ganin haka ya sanya shi juyawa yana faɗin,
"Na barki lafiya tun da dama ba ƙirana kika yi ba, duk sanda kike buƙatar ganina zuciyarki za ta kirani."

Ɗagowa ta yi ta ga tafiyar yake zuciyarta ta ce,

'Tafiyar ka yi kuma?'

Juyowa ya yi da murmushi ya ce,
"Ko in dawo ne?"
Da sauri ta rufe bakinta a hankali, ta ce,
"Ashe yajini."

"Ban ji ki ba, sai kin dawo, ku kularmin da kanki." Yana kaiwa nan ya yi tafiyarsu.

Juyawa ta yi tana addu'a, yau ta gamu da aljani, harta fita titi ba ta ƙara juyawa ba.

Taɗau lokaci mai tsawo tana jiran abun hawa amma shiru.

Dak'yar ta samu mai keke napep, sun yi gaba kaɗan suka ɗauki wata za ta sauƙa wajen City store.

Tun kafinsu ƙarasa tsayawa, ta ƙura wa  shirgegen Alhajin da ya daga cikin Store ɗin wata matashiyar budurwa na biye da shi, hannunta riƙe da manyan ledodi, kallo ɗaya za ka yi mata ka san cewar ba ɗiya ce da ta fito gidan mutunci ba.

_Littafin Yesmeen na kuɗi ne, duba da yanayin da muke ciki a yau, idan kina son cigaba, zaki turo katin MTN na 100 ta wannan number 08082435132 ta WhatsApp ko ta message. Na gode

*2020*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 08, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YESMEENWhere stories live. Discover now