*°🔘°AISHA LAMIƊO°🔘°*
*1441H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*UMMU NABIL✍🏼*
🅖🅦🅐ᏢᏒᎬsᎥᎠᎬᏁᏆ.
*WattpadUMMUNABIL6034**SADAUKARWA GA:-*
*SAFIYYA*
_(Autar Umma❤)_*TUKUICI GA:-*
*JIKAR KULU*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 11&12📑*
*__________📖* tana fita ta iske Safiyya zaune gefe guda tayi tagumi.
Ƙarasawa tayi a kiɗime, zuciyar ta sai luguden duka ta ke, kamar zata fito ƙasa tayi rawa.
Wani zazzafan gumi ne ya keto mata lokacin da ta isa inda Safiyya ta ke, ta cafki hannun ta, hannun Safiyya taja suka don su bar gurin, gudun kar ya fito ya iske su, duk cewar mutane suna wucewa amma halin da Aisha ta ke ciki shi kaɗai zai tabbatar kama da ita ta shiga ofishin nashi.
Tsabar riƙon da Aisha tayi ma Safiyya ya shiga jikin ta, a razane ta ke duban Aisha da tambayoyi kala-kala a bakin ta amma bata samu damar hakan ba sai da suka yi nesa daga inda suka baro.
Safiyya cikin firgici da yanayin data ga ƙawar tata a ciki ya sanya ta faɗin, "ke lafiya? Meye haka kike yi? Kina hauka ne? Saki min hannu mana haka".
Duk wannan jerin tambayoyin da Safiyya tayi ma Aisha bata samu damar bata amsa ba, sai kaiwa da komowa ta ke yi a harabar in da suka tsaya.
Ganin kamar Aisha bata cikin hankalin ta yasa Safiyya taja hannun ta suka samu gefe guda suka zauna, Safiyya ta dubi Aisha ta gama nazarin halin da ta ke ciki sannan tace,
"Aisha".
Juyowa idanun ta tayi wanda tuni sun kaɗa sunyi ja tamkar an zuba masu garwashin wuta saboda tsabar jan da sukayi, tsoro Safiyya taji ta matsa gefe kaɗan tana faɗin,
"Subhanalillahi! Ke wai meye ke faruwa ne?, ko gamo kika yi da kika shiga ofishin, ko kuwa yaci zarafin kine ban sa ni ba, wannan halin da kika shiga gaba ɗaya kin tayar min da hankali wallah, meye ke faru ne kiyi min baya ni Aisha, kin saka zuciyata cikin zullumi da neman sa nin abin da ke faruwa cikin gaggawa".
Aisha ta goge hawayen da suka samu nasarar zubowa tun fitowar ta daga wurin Abbakar ta dubi Safiyya sosai tace,
"Safiyya wallah ban taɓa yima Abbakar sharri ba, ban kuma yi tunanin haka halin shi ya ke ba sai yau, Safiyya kinsan kuwa abin da yayi?".
Cikin firgici Safiyya ta zaro ido tana faɗin, "nashiga uku! Aisha badai wani abin yayi maki ba ko, wayyo ni rayuwa ta meye yayi maki?" ta ƙarasa Maganar tana rarumo hannun Aisha.
"babu abin da yayi min, amma nayi mamakin halin shi, haihuwar uwar sa na tarar dashi da wata yarinya a shekaru bazata wuce ni ba".
Ajiyar zuciya Safiyya ta sauke tare da dafe ƙirjin ta tace, "kashhh amma wallah kin matuƙar tsoratar da ni, gaba ɗaya na rasa abin da zan faɗa, ke yanzu akan ɗan ƙaramin wannan abin kika tada hankalin ki, kika tashi nawa Aisha wai ke wace irin yarinya ce ne, na kasa sa nin halin ki, meye haka Aisha wallah ba ƙaramin tada min hankali kika yi ba, duk na gama ruɗewa nayi tunanin ko wani abin yayi maki ashe sam ba haka ba ne, to don kin gan shi a haka tunda ba ke yayi ma ai kawai ki bishi da addu'ar shiriya, kiyi mashi addu'a Allah ya shirye shi, haba don Allah ki riƙa sakawa zuciyar ki jarumta kar ki bari zuciyar ki tayi sanyi, tashi mu tafi ni don Allah, duk kin ɓata min rai".