👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
_16/7/2020_*Written by*:- _Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@wattpad**HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*
35&36
Tunda magriba ta doso hjy iya ta kasa nutsuwa idanunta suna kan kofa, duk motsin wanda taji zai shigo sai ta waiwaya ta kalli gurin, dan tsoho dake gefen bishiya ya kalleta bakinsa da murmushi yace, " su hadizatu baki har kunne ana murna za'aje aga habibu" kallansa tayi bata bashi amsa ba ta cigaba da yan kalla-kallenta.
Kamar wanda aka kara tsunkula ya kara kallanta yace, " hadizatu nifa Abinda yasa kikaga naki tafiya na biyo ku wata shawara na yanke" karaf yusuf ya tsomo musu baki, "wace shawara ce baba?" ehto, nikam maganar gaskiya kafata kafar hadizatu dan akwai wani abu da yake tamun yawo araina kuma na tabbata zai zame mana alheri nida ita".
Dariya yusuf ya shiga yi yana kyakyatawa harda rike ciki, cikin zolaya ya kara zolayo dan tsoho da hjy iya, " nifa baba da farkon hawa mota ta na dauka matarka ce dan kunyi bala'in birgeni har ina fatan nima idan nayi aure nida mata ta mu kasance kamarku har tsufanmu" zuciyar dan tsoho tas har wani murmushi ya kara saki sannan yace, " yaro kenan, ashe kaima ka hango abunda yake cikin raina, gashi tunda naga habibu naji ya kwanta mun azuciyata ji nake kamar ni na haifeshi, nasan idan nayi masa bayani shi zai fahimceni"
Hjy iya da kamar bazatayi magana ba amma ganin dan tsoho sai zance yake kamar ya kone aka yasata yi masa magana.
" dan Allah mai yasa kai idan kana magana kamar karamin yaro kaifa kace gurin jikokinka zakaje, kawai daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki, kamar muna garin gab'a-gab'a sai kawai ka debi jiki zugwi-zugwi ka bini mu tafi, to ba habibu ba kowa zaka gayawa duk abunda yake cikin zuciyar taka sai dai kayi ta fada" hjy iya na gama maganar ta tashi ta dau buta kasancewar anata kiraye-kirayen sallah, da ido dukkansu suka bita dan tsoho wannan karan yaji haushi, shi ba haka yaso ba amma ya lura hjy iya akwaita da taurin kai.( _yoooo kaine sai yanxu kasan taurin kan hjy iya, tunda habibu ya hanata tafiya ta kafe gashi nan ta d'aga hankalin bawan Allah._🤣)
Yusuf dariya har son subuce masa tayi ya maze yace wa dan tsoho, " yanxu baba Tsakani da Allah yaushe ka karewa habibu kallo da har kaji ya shiga zuciyarka, ko ni da na fika kwarin ido bana shaida kamanninsa ba, ko dai dankwaleliyar motarsa ce ka karewa kallo har kaji ya shiga zuciyarka?" mtsswwww, dan guntun tsaki dan tsoho yayi sannan yace, " kai kam wannan yaro anyi jarababbe da bin k'ok'k'ofi kai ko tusa mutum yayi sai ya kafeshi da tambayoyi, to idan ma motar tasa na gani meye aciki, nan da dan lokaci nima zaka ji labarin anfara tuka ni acikin irinta bayan Aurenmu da hadizatu na"
😨😨 _kai kam dan tsoho wallahi anyi kwadayayye, ance ba'ayi amma kana kara tura kanka._
Wannan karan tusuf dariya yake harda rike ciki, ganin irin san abun duniyar dan tsoho karara afili, larai matar musa tana gefe tana jinsu itama har suka so bata dariya.
_BAYAN MAGRIBA_
Musa sallama yayi ya shigo bayan sun gaisa hjy iya cikin k'aguwata jehomai tambaya, " musa nace har yanxu dan uwan naka bai dawo bane kar dare yayi" wallahi iya yanxu haka daga shagon nake na samu yaron da suke kwana abakin titi ina tambayarsa haruna yacemun, yace masa unguwa zashi amma bai gaya masa takamaimai inda zashi ba, shi ne na dawo inxo in zauna a gidan dan nasan ,bazaiyi nisa ba tunda yasan ina jiran sakon da ke gurunsa, nasan dai idan ya dawo tanan zai biyo" musa yake wa hjy iya bayani, ji tayi kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu dan bakin ciki.
YOU ARE READING
YAWON SALLR HJY IYA Complete
Short StoryGudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar h...