Page two

17 0 0
                                    

*°🔘°MATAN GIDAN MU°🔘°*
            *1441H/2020M.*
          *SHAWWAL/JUNE.*
   


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_


         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*REAL QUEEN✍🏼*
~INSTAGRAM~
~real_queen_abeedat~
~wattpad~
~REAL QUEEN~

*WANNAN SHAFIN SADAUKAR NE GA MAHAIFIYATA ALLAH YAJA NISAN KWANA,YA CIKA MIKI BURINKI❣❣❣•*

*JIGON RAYUWANA INA MAKA FATAN ALKHAIRI ALLAH YA TSAWAITA SHEKARU YA KARE MANA KU DAGA SHARRIN MUTUM DA ALJAN MAHAIFINA❤❤❤•*

*YAN AMANA TA INA SONKU SOSAI,MRS ZAK'S (BAZAN TAƁA MANTAKI BA MAI GAYYA MAI AIKI), A'ISHA HUMAIRA INNARO,MY KHADY JIKAR HAJIYA,SIS NUSAIBA(NUBEE), NEATLADY🙄🙄, SAJEEDATOUR IN-LAW,MARYAM MUƘADDEESA IN-LAW,MUCH LOVE YOU ALL🥰🥰🥰🥰💓💓💓*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*

Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com

Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*

Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*


*SHAFI NA 2📑*


*__________📃* Dogon tsaki Na'ima taja tace,"wai ke kullum Mariya maganarki shine Samari su soni,nifa gaskiya kin takuramin,kullum bani da aiki sai zuwa hira gurin kowa".

     Ta ƙarashe maganar da murguɗa baki.

    Shiru Mariya tayi kamar ba zata ce wani abuba,sai can kusa minti goma sannan tace,
    "Kefa Wallahi bakya ganewa,yanzu kina tunanin da bana karɓo miki waɗannan magungunan gurin boka ai da har yanzu babu karen da zaice yana sonki tunda dai kinga Wannan mayyar ta fiki kyau sau ɗari".

      "Ok wato kina nufin Ni bani da kyau ko?, hmmmm amma dai ai na fiki kyau tunda ni ina da ido da hanci,ba irin naki ba".tana gama faɗa taja dogon tsaki ta bar gurin dan ta gaji.



       To haka rayuwar gidan taci gaba da tafiya yau da daɗi gobe babu,dan babu abinda ya canza a cikin halin *matan gidan* sai ma abinda ya ƙaru.

        Shafa'atuce zaune da ƙawarta a daƙi suna hira,ƙawartata ta kalleta tace,"wai ke haka zaki zauna,ko irin ɗan magungunan mallakar nan ba zaki samo ba?".

       "Hmmmm wa zan mallakar? Uban ko Ƴaƴan?".

      "Mtsss dukkansu mana,meye amfanin su?".

     Murmushi shafa'atu tayi tace,"Ni bani da ra'ayin zuwa gurin wani malami ko boka,nafi so inyi Abu da basirar da Allah yayi min".

       "Ban gane me kuke nufi ba?". Cewar ƙawar shafa'atu mai suna ladiyo.


      Dafa kafaɗar ta shafa'atu tayi tace,"Su bokaye akasari sai dai suci kudinka, buƙata bata biya,amma Makirci kuwa ba sai kayi asarar kuɗin ka ba".

      Wani irin ihu ladiyo tayi tace,"Wallahi kina birgeni ƙawata, dama nasan ba zaki gyalesu haka ba, wallahi ki gwara kan ƴan iska karma Wannan Asma'u ɗin".

     "Ai wallahi Yarinyar nan ita da ƙannenta sai shan ruwan gidan ubansu ya gagaresu,Kawai lokaci nake jira".

    Ladiyo miƙawa shafa'atu hannu tayi suka tafa tace,"Allah ya ida mugun nufi Aminiya,yanzu mai zan samu dan nasan babban gida kamar wannan dole na samu abin arziƙi".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 23, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now