GIMBIYA SUHYLAH

70 4 0
                                    

2

SUHAILAH

NA NANA DISO

https://arewabooks.com/u/nanadiso10

Binta yarima khalid yayi yana danAllah baiwar Allah ki tsaya wallahi nafi awa biyu ina kallonki,ina jiran fitowar ku...

Cikin murmushi gimbiya suhylah tace ina sauraron ka cikin mintuna biyu..

Fara'a yayi sannan yace mata nagode,dafarko dai danAllah kibani nombar wayarki...

Dogon numfashi tayi taga yadda shareef yabata ransa sannan tace kayi hakuri bawan Allah na bar yayana atsaye ...

Zaiyi magana yaga har ta juya tatafi...

Cikin bacin rai yashiga motarsa cike da tunanin gimbiya suhylah, tunani yakeyi kada sha'awar dake damunsa tasashi yayi zina,bakaramin kokari yakeyi ba gashi Aisha takasa fahimtar sa kullum kalamanta basa huce nace masa rago,shikansa yasan ada bashida lafia amma yanzu kuwa yadd yake jinsa mata uku ma zai iya dasu jan motar yayi ya nufi gida cike da baccin rai...

Gimbiya suhyla ce tace yayana donAllah kayi hakuri banaso naga ina wulakanta mutane ne shiyasa natsaya na sauraresa...

Shareef ba karamin mamaki yake ba yadda gimbiya suhylah batada wulakanci ko girman kai,wata lafiyayyar ajiyar zuciya yayi yace kanwata bakomai don kin barni atsaye ,amma kisani mijin da zai aureki yafi kowa sa'ar mata domin kinada kirki,saukin kai ga hankali..

Murmusa masa tayi sannan ta bude mota tashiga cike da kaunar yayan nata..

Yarima khalid zaune kan kujerarsa yana danna waya,shaidan sai raya masa yakeyi cikin zuciyarsa...aisha ce tashigo cikin wata fitinanniyar shiga wacce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da yakeyi atake jikinsa ya mutu tare da fadin MashaaAllah,bata tsaya ko'ina ba sai k'an kujerar da yake zaune cikin isa irin tata ta uwargida tace..

Yarima yaushe kashigo banji karar mota ba..

Murmushi yayi wanda ya bayyana hakorin makkansa sannan yace aisha wai yaushe zakisan darajata da mutuncina?

Cikin bacin rai tace me kuma nayi maka sarkin masifa...

Cikin zafin nama ya kifa mata mari sannan yace ki iya bakinki da sarkin gobe kike magana,don kinga ina kyaleki? So kikeyi n fara zina ne kokuma kinfi so nakashe kaina da sha'awa???

Jiyowa tayi cikin masifa tace kaje kayi zina mana kokuma ka kara aure wanda bashida asali naga maccen da zata iya zama dakai...

Mamaki ne yasa yarima khalid zama wanda yasa shi zubda hawaye cikin mamaki yace aisha nayi danasanin aurenki nabi kyau na manta da rashin addinin ki kinmanta da halaccin danayi miki, don na nemi hakkina shine kike gayamin kalaman nan? Aisha kin manta da labarinki kin manta kin zubda mutunci na aureki ? Kin manta kinrasa miji na taimaka miki? Kin manta mahaifinki zaiyi miki baki nace ni zan aureki? Aisha ni kikecewa mara asali cikin wani zazzafan kuka yatashi tsaye yace indai ni danhalak ne bazan kara nemanki ba kuma bazan taba rabuwa dake ba zan dinga yin azumi har Allah yakawomin mafita...

Tsaki tayi sannan tashige cikin daki..

Uwargidan sarki ce tashigo cikin babban daki cike da masifa tana fadin ina suhylah ne shigeyar yarinya dabatasan mutuncin kanta ba mahaukaciya...

Suhylah ce ta mik'i jikinta na rawa tace hajiya gani...

Jawota tayi sannan tace kije mai martaba yanason ganinki nasan bazai huce yace zai aurar dake ba muma muhuta da wannan mugun halin naki..

Jikim suhylah yana rawa tatafi fadar mai martaba bayanan sai ta nufi makwancin sa nan ta tarar da matarsa hajiya bilkisu cikin rarraunar murya tace Allah yaja da ranka gani...

Cikin isa tasa ta sarki yakalli hajiya bilkisu da alamar taje ta basu guri tafita tabar dakin...

Suhylah!

Naam Babana ina fatan ba laifi nayi ba...

Cikin gyaran murya yace bakiyi laifin komai ba suhyla insso muyi magana dake ta sirri tabbas ke yarinyar arzuki ce inaso nabaki dan takaitaccen tahiri game da babban d'ana yarima khalid..

Cikin mamaki tace Allah yakara maka lafiya babban d'a daman kanada wani d'an bayan yayana yarima usman?

Murmushi yayi yace tabbas suhylah inadashi matata ta farko wacce tarasu itace ta haifa min shi ni da hannuna ta bawa kanina shi saboda yunkurin kashe sa da akayi...

Baba ina yake yanzu?

Yan gurin baffah na agarin batulde nabasa amanarsa tun yana shekara 5 sannan nace adinga cemasa yarima yanzu haka yayi aure ma sama da shekara biyu ,inaso in hadaku aure ke dashi...

Zabura tayi sannan tace baba yayana zan aura...

" murmushi yayi yace yarima khalid ba yayanki bani ba ...

Wasu zafafan hawaye ne suka fara zubo mata tace yanzu duk irin hidimar da kake dani bakai ka haifeni ba?

Suhylah tabbas bani na haife ki ba...

Akwai ranar da nayi tafiya nikadai zuwa wani kauye muna cikin tafiya mukaga wata baiwar allah dauke da jaririya a hannu na durkusa domin yi mata magana sai naga idanuwanta sun cika da hawaye wanda hakan yasa na tambaye ta me yafaru? Budar bakinta tace ita jakadiya ce anturo ta takashe jaririyar nan a dokar dajinnan itakuma bazata iyaba saboda da zarar ta ajiye jaririyar sai tasaka mata kuka, lokaci daya naji jaririyar nan takwanta min acikin rai na sannan nace mata danAllah ni ki mallakamin jaririyar nan inasonta sosai da sosai...

"Cikin hanzari ta mik'omin ke sannan tace wannan yarinyar jinin masarauta ce kuma sunanta gimbiya suhylah wannan shine sarkarta ka kula da'ita kaji tsoron Allah gurin riketa domin na rabata da mahaifiyar ta in ka wulakanta ta Allah zaisaka mata...murmushi nayi na karbeki sannan natawo dake cikin masarauta ta inda nasanar da matana kowanne yace bazaiyi raino ba kullum inna tirsasa sai naga ana wahalar dake watarana ma har hajiya zainabu wato uwargida ayanzu natarar tana yayyanka ki da wuka amma tun kina jaririya ni nake hadamiki madara dakomai da komai na soki suhylah kuma na nunamiki gata cikin ikon Allah kikayo tarbiyata kike kaunata kema jakadiya harira ita tadinga rainonki harkika girma..

Cikin kuka suhyla tace banida asali dama banida gata dama abba kai ka taimakeni kai kanunamin kulawa kai ka kauna ce nagode sosai Allah yasaka da alheri banida abunda zanbiyaka kuma duk wanda ka auramin zan zauna dashi...

Wannan maganar tazama sirri tsakanin mu Allah yayi miki albarka zaa daura aurenku zuwa wani satin domin nayiwa baffa na maganar ma dazu...

Cikin hawaye tace babu abunda zance maka sai dai nayi maka addua domin dukkan kalaman da zangayamaka bazasu kai adadin kulawa dani dakayi ba...

Murmushi yayi yace babu komai gimbiyata kikula dakanki sannan kikara hakuri akan kowanne irin yanayi dazaki shiga..

Fita tayi idanunta na zubda hawaye tare da fadin yaaAllah kanagani kuma kanaji Allah kakara zama gata gareni, wani sabon son shareef ne yakara saukar mata tayaya zata fahimtar dashi wannan maganar anya yaya shareef zai yarda da dukkan furucinta kuwa anya???

Yinin ranar kuka takeyi mai juma jiki kowa yakasa gane kanta tana kwance akan gadonta taji an bude dakin cikin yanayi na damuwa ta dago taga wanene bakowa baniba face yayanta wato shareef...

Kokarin karasowa yayi cikin hanzari da fadin me yasameki kanwata me akayi miki...

Wani matsanancin kuka takara fashewa dashi sannan tace yayana danAllah... can kuma tayi shiru bata kara furta komai ba...

Cikin yanayi na damuwa yace nace miki kidaina dakuwa da halin mutan gidannan inajiran takarduna sufito ne muyi auren mu mu barmusu gidan...

Dago da kanta tayi wasu zafaffan hawaye suna bin fuskarta yaya...

GIMBIYA SUHAYLAWhere stories live. Discover now