🌼🌸🌼🌸🌼 *ALEEYA* 🌼🌸🌼🌸🌼 *HISTOIRE ÉCRIT PAR* *MARIAMA SANI* 🌼🌸

9 2 0
                                    

🌼🌸🌼🌸🌼
     *ALEEYA*
🌼🌸🌼🌸🌼

*HISTOIRE ÉCRIT PAR*
*MARIAMA SANI*
🌼🌸🌼🌸🌼🌸
*_(Maman Souraya) 'yar mutan Niger🇳🇪*


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
'''(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛'''



*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*


✍️ PAGE   12---13


°•°•°•°•°• Yana tsaka da mafarkin suna cikin wani waje mai kyau da yawan ciya yi shida wata kyakkyawar budurwa murmushi d'auke a bakinta tana so ta fad'a masa wata magana harda lumshe ido yake dan tsabar farin ciki da jin dad'in da yake sai kawai ya ji ana jijjiga masa k'ofar da k'arfin tsiya, wani irin firgigit yayi ya zabura ya mik'e zaune yana dudduba ko ina na d'akin wai ko zaiga Aliya, yana cikin haka Karima ta tura k'ofar da k'arfi ta shige tana rusa kuka hannuwanta duk biyu suna a saman kanta ga wata uwar zufa dake tiyaya a fuskarta, katse mata kukan yayi da cewa.

''ke lafiya ki shiga min d'aki kina rizgar wannan uban kuka"?

Jin haka yasa ta k'ara wage baki ta shiga yi masa magana tana cewa, ''ya kai Musa d'an baiwa kataimakan kamar yadda naji a garinnan  kowa maganar ka ake da irin taimakon da kake a ko'ina, shina nima nazo maka da tawa buk'atar ka taimaka min kamar yadda Allah ya taimake ka'', ido tabisa dashi tana kallonshi.

''ke kuwa yarinya wane taimako kike so ayi miki?.

Rage kukan tayi cikin nuna kalar tausayi zayyano masa da buk'atar ta tare da yi masa Alk'awarin zasu mallaka masa duk abinda yake so daga cikin dukiyasu, tace dashi Abbanmu ya mutu ya barmuna dukiya nida 'yar uwata, kuma komai da ya mallaka a hannunmu yake daga  kud'ad'e har shanu da rak'uma, ba muda uwa bare uba a hannun kakarmu muke kuma yanzu haka da ciwanta ya tashi kakarmu ba tanan tayi tafiya shi yasa na garzayo gunka dan ka taimaka mana'', ta gama maganar tana kollon yadda zai d'auki zancan nata,

A b'angaran Musa kuwa da farko har zaice dasu ba zaiyi ba amma da yaji zancan kud'i ai tuni zuciyar sa ta hango yadda zai yaudare su ya gudu tare da yarinyar nan da ya kwallafa ido da rayuwarsa a kanta, cikin in ina yace, ''kin tabbatar da maganar ki gaskiya ce?, dan fa aikin naki zaiyi tsada dan sai na had'a da su d'an malingo sannan za'a samu dacewa, a yadda kika kwatantamin irin abinda ke damunta na gane da tana tare da bak'ak'yen Aljannu, amma idan zaki bada duk wani abinda za'a buk'ata to ba matsala zan taimaka muku kuma zata samu lafiya''.

Cikin kuka Karima tace, ''kar ka damu da wannan, ni d'ai fatana 'yar uwata ta sami lafiya, duk abinda ka zab'a daga cikin dukiyar zamu baka, gidaje ne, gonaki  kud'i duk zamu baka abinda ka zab'a, duk bamu damu dasu ba lafiya mukafi buk'ata, sannan kuma sai kayi sauri dan yanzu haka ma kulleta nayi a d'aki gudun karta guda''.

Cikin sauri Musa ya shiga tattara kayasa na yaudara jikinsa har yana rawa dan tsabar zalama.

Cikin sa'a suka isa gidan su Saude ba tare da mutane sun ankara ba, shiga su kayi kai taye ta bud'e masa k'ofar d'akin, a hankali ta zura kai tana duddubawa kamar mai tsoro, rad'a tayi masa da kar ya sassauta musu dan har duka suke.

Har ya razana amma idan ya tuno da zai samu dukiya sai yaji wani nishad'i a ransa, cikin nuna shi gorzone ya tura kasan cikin d'akin hannuwa rik'e da wani abu mai gashi yana jijjigashi yana wata maganar sa k'asa k'asa, ita kuma taka bakin ko'far d'akin tana kunshe dariya.

Rarraba ido Musa ya shiga a d'akin kasan cewar Yana da d'an girma kad'an, zaune take a tsakar d'akin lullub'e da Wani bak'in abu tana gunjin kuka da karkarwa kamar mai jin sanyi yayi kicib'is da ita, wanda ganin hakan ya sashi tsaya cak wuri guda zuciyar sa sai dukan hamsin hamsin take, k'arfin hali yayi ya zura hannu don ya bud'eta cikin karkarwar jiki ya zare zanin da take lullub'e dashi, gabansa ne ya buga da k'arfi tare da yarda zanin cikin sauri, mamaki ne ya kamasa dan ganin wace yayi arba da ita, ita kuma k'uri tayi masa da ido tana kallon sa tare da k'ara warosu waje suka k'ara girma dama gasu dara dara dasu kuma farare fes dasu.

D'an murmusawa yayi a ransa wani sanyi da dad'i ya ziyarci zuciyar sa, gashi ga abinda yake gurin samu, ga Aliya ga dukiya, komawa yayi bakin k'ofar ya umarci Karima da ta kawo masa ruwa a kwano, d'ibowa tayi ta kawo masa sannan yace da ita, ''ki rufe k'ofar nan duk wani abinda le kaji kada ki bud'e har sai inni na umarce ki da ki bud'e d'in, dan naga Alamun sai nasha fama kafin asamu yadda akeso, da alamu ma sunfi su d'ari a kanta....''

Katseshi tayi da cewa, ''koma runduna nawa ne ka watsar mana dasu da irin baiwarka, maganar rufe d'akin kuma yadda kace haka za'ayi Kai dai karka manta da arzikinda zaka samu''.

Komawa yayi d'akin ita kuma ta rufe d'akin gam ta koma gefe ta tsaya.

Zaunawa yayi ya ajiye ruwan ya fido k'ullukan magun gunan ya shiga kwancesu Yana zubawa cikin ruwan amma fa idanunsa k'af a akan Aliya suke har yawunsa na sark'rwa dan kwad'ayi da zalama, bari tayi sai da ya kammala duk wani abu da yake idonts k'yer a kansa tana wani muzurrai tana zazzaro masa su, tsoma wannan abun mai gashi yayi a ruwan da niyyar ya yayyafa mata su a jikinta.

Wani irin tsalle tayi ta dire a d'ayan gefe tare da kurma wani uban ihu tana fad'in, ''kar ka kuskura ka zuba mana wannan ruwan masu warin tsiya'', tana magana tana tsalle tsalle yare kare jikinta da hannuwanta.

Wani ras yaji a zuciyarsa lokacin da tayi tsalle ta tashi tare da kurma ihun da tayi, amma yana jin tace karya zuba mata ruwan yaji wani sanyi a ransa,  nufar inda take tsaye yayi yana wata irin maganar sa ta yaudarar da ya saba wanda ya hardace ta, hausa ce yake amma saika rantse da wani yare ne yake maganar ba da hausa ba, lokacin da ya fara maganar tsayawa tayi cak wuri guda.

Yana ganin haka ai kuwa ya shiga yayyafa mata ruwannan da ya barbad'awa magani.

Wani irin ihu ta zunduga tana tsalle tana fad'in''kar ka k'ara zuba mana wannan ruwan masu warin da zafi a jikinmu, ka dena narkar damu za suyi, munsha Talatin ba ukku ba, wayyo kar ka k'ara zuba mana su warinsu yayi yawa zamu amayar da hanjin cikinmu, ka dena wahalarda kanka ba zamu fita ba ita d'in ta zame muna gida a jikinta muke duk wata rayuwarmu dan haka ba inda zamu,'' cikin hanzari Musa ya kwara mata ruwan a jikinta, ai kuwa wata iriyar k'ara ta saki tare da fad'uwa k'asa tana shure shure da gurnanin idonnan duk a kakkafe suke babu ko d'igon hawaye.

Mamaki da Al'ajabi ne ya mamaye zuciyar Musa, a tunaninsa dai yasan cewa shi ba mai bada maganin gaskiya ne ba to ta yaya hakan yake faruwa, ko dai baiwar da yake ikirarin yana da ita ce ta fara bayyana, shin ko kuma itama Aljannu nata ba na gaskiyar ne ba? to indai hakane zani d'auketa mu gudu '', wata dariya yayi yanna hangota a matsayin matar sa.

Aliya kuwa tana lura da yadda hankzalinsa ya bar jikinsa tayi sauri ta tashi daga wajan da take k'wace Saude tayi saurin maye gurbinta fuskarnan kuwa ta shafeta da farar laka, idon sunsha yaji sunyi jawur dasu, a hankali ta jawo bak'in zanin ta rufe jikinta da shi ta shiga rizgar kuka.

Sauran ruwan da ke hannunsa ya ajiye ya nufi inda take duk'unk'une ya shiga yayyafa mata wannan gashi gashin yana yi yana magana.

Kuka take tana fad'in, ''daina zuba mana ruwannan a jikinmu zafi ne dasu, idan ba haka ba kuma zamu kasheka tunda taurin kan naka yayi yawa, mugu azzalumi ma yaudari''.

Musa kuwa ko d'ar baiji ba daga k'arshe ma ruwan gaba d'ayan su ya juye mata su a jiki yana dariyar mugunta, yana fad'in, ''k'arya kuke yi ni Musa d'an baiwa nafi k'arfin irinku, ku fice daga jikinta tun kafin na toyaku''.

Shiru Saude tayi ta dena kukan da take yi amma tana nan a tsgunne, ganin haka yasa Musa yaye mata bak'in zanin da ta lullub'a yana kallonta, d'ago kan tayi a hankali har ta kife su a fuskar Musa, wani irin juyi Musa yayi wan har saida ya wuntsula gefe d'aya, inda tsorata Musa yayi matuk'ar tsorata da ganin yadda Fuskar ta ta canza cikin k'ank'anin lokaci, rairafuwa tayi tana gurnani ta nufo inda yake, jikinsa duk yayi sanyi wani irin tsoro ne ya shige sa jikin sa kuwa ko ina rawa shike, da k'yar yake komawa da baya da baya dan tsabar nauyi da jikinsa yayi masa, karo yaji yayi da wani abu a bayansa, a hankali ya juya kansa dan ganin abinda yayi karo dashi.....


'''Tofa jama'a Mutuminku Musa d'an baiwa ya fa shiga tsaka mai wuya, k'ara k'ara k'ak'a......'''

_Ku muje zuwa......_

*Daga Alk'alamin ✍️✍️ Mmn Souraya 'yar Mutan Niger......*🇳🇪

Comment les amis

Vous avez atteint le dernier des chapitres publiés.

⏰ Dernière mise à jour : Aug 29, 2020 ⏰

Ajoutez cette histoire à votre Bibliothèque pour être informé des nouveaux chapitres !

Labarin Aliya labari ne na wata hatsabibiya mai taken piya piya kashe kwari Où les histoires vivent. Découvrez maintenant