Bayan Inna delu ta shigo ta tsaya, Ummu Sulaim ta fara Mata tambayoyi "Inna delu Ina so ki gabatar ma koto da kanki." Cikin dakiya da k'warin gwaiwa ta fara magana "Nidai sunana Suwaiba amma anfi kirana da Inna Delu, na dad'e Ina aiki a gidan Alhaji Hamza, Kuma shine ya bani damar inzo nan kotun in f'adi iya gaskiyar abunda na sani, kamar yanda Safara'u tace tabbas Faruku yayi ma diyarta fyad'e saboda tabbas a ranar duk akan Ido na komai ya faru, don ban mantawa ranar gidan babu kowa, ita yarinyar da akayi ma fyad'en ita kad'ai ce a gidan a ranar, Hajiya ta tafi sabgar gaban ta ni Kuma na tafi kasuwa dan siyo kayan miya, bayan na dawo na iske shi yana wannan ta'asar, nikuma nan take na tsaya na d'auki komai a waya ta, ita kuma saboda wannan ba shine karo na farko ba da Faruku yayi ma yar aiki fyad'e ba, wannan shine dalilin da yasa na k'udurci inshaAllahu wata rana sai na tona masa asiri saboda abun yana damuna, a baya kam bani da wata sheda amma yanzu Ina da sheda ta..." ta ciro wayar ta mik'a ma Ummu Sulaim", ita Kuma ta mik'a aka ba Alk'ali, bayan Alk'ali ya gama kallon video, ya d'ago ya kalli mai kare eanda ake kare yace 'ko lawyer wanda ake k'ara Yana da abun cewa?" Guiwa a sabule Barr zailani ya mik'e yace "A'a ya mai girma mai shari'a" ya koma ya zauna a sanyaye yana jinjina lamarin Bar. Ummu lallai fafatawa da ita sai mutum ya shirya...
Alk'ali ya maida duban shi ga Barr Ummu Sulaim yace "Ko lawyer wacce ta kawo k'ara tana da abun cewa?" Mikewa tayi tace "eh ya mai girma mai shara'a, Ina so koto tayi la'akari da wani abu d'aya, ba Faruq kadai ne mai laifi ba har Mahaifiyar sa ma babbar mai laifi ce idan akayi la'akari da tasan d'anta bashi da gaskiya amma k'iri k'iri take goyon bayan shi har ma ta shige masa gaba ta nemo mai kare sa, da wannan nake rok'on wannan koto mai adalci da tayi gaggawar hukunta Hajiya Asabe akan wannan laifin sannan ayi ma Faruq hukunci kai tsanani nagode mai girma mai shari'a" bayan Alk'ali yayi y'an rubuce rubuce ya fara zartar da shari'ar "Kotu ta yanke ma Faruq hukuncin shekara 25 a gidan yari tare da aiki mai tsanani, sannan kotu ta yanke ma Hajiya asabe hukuncin shekara 2 tare da tarar million 3."
Nan aka kama Faruq da Hajiya aka tafi dasu, kotu ta watse.Cikin farin ciki Safara'u ta rungume Ummu Sulaim tana kukan farin ciki, d'an bubbuga bayan ta tayi tace "Is ok ya Isa haka" kamo hannunta tayi Tace"
Nagode barrister nagode bansan dame zan biya ki ba saidai nayi tayi maki addu'a Allah ya k'ara daukaka, Allah ubangiji ya tsare ki daga sharrin mak'iya da kuma mahassada nagode," Murmushi tayi tace "Haba ya isa haka, ba komai ni don Allah nayi maki, bake ba ma duk wacce aka cuta ta hanyar fyad'e sai inda karfi na ya k'are nayi ma kaina wannan alk'awarin inshaAllah, zan tsaya ma duk wacce aka cuta ta hanyar fyad'e da karfi na da kuma dukiya ta"
Ta k'are maganar cikin yanayi na 6acin rai da damuwa, idanuwan ta sun cicciko da hawaye, juyawa tayi cikin dubara ta goge su ba tare da Safara'u ta lura ba, ta k'ak'ulo murmushi tana duba agogon hannun ta, tace "Ok ni zan wuce gida" Daga nan ta nufi inda securities dinta suke....Haka dai kwanaki suka cigaba da riki'd'ewa su koma watanni, watanni su koma shekaru, haka rayuwa take ta cigaba da tafiya...
Bayan shekara 10.....
TEN (10) YEARS LATER
Firgit! Ta farka sakamakon ringing din da wayarta keyi dake aje kan side bed drawer.
Tsaki taja tace "Ohh myy Godd, waye ke kirana haka this early morning? ughhh!" A kasalance ta dauko wayar tana duba time karfe 8:51am ta gani, wayar ce ta sake ringing ta kalla screen din ganin Samra tace, "Ugh! This girl!"
"Hellooo!" Tace tana turo baki
"Sanahhh!" Ta fada cikin tsawa wane zata 6alla wayan
"Innalillah Samra am still sleeping fa!"
"Wharever! Ki shirya anjima zanzo na daukeki zamu fita..." Bata ma tambayeta why ba
"Kinjiii?"
"Naji"
Jawo bargo Sanah tayi ta koma baccinta.Karfe 11 daidai ta farka, a hankali ta mik'e tare da zuro kafafunta kan lallausan carpet din dake malale k'asa, toilet ta fad'a tayi brush, bayan tayi wanka ta d'auro alwala fitowa tayi d'aure da towel, shafa creams tayi masu matukar kamshi da sanyaya rai, body sprays ta fesa tare da roll on, comb ta d'auka tayi combing dogon gashinta bak'ik'irin dashi mai taushi da santsi sak irin na mamanta, can ta daure gashin into a bun.
Closet ta nufa ta tsaya kallon kayanta yanda kukasan shagon saida kaya ko wane da inda yake, tsaye tayi ta kasa zabar kayan da zata sa, Mama tasha fada mata ta cika ruwan idon tsiya well hakane, bayan ta gama 6ata ma kanta lokaci tayi deciding sanya English wears, wando da riga ta dauka tight ne kalar black da pink riga k'arama, favorite turarenta mai suna Oud ta fesa, kimono ta d'ora a kai tare da daura gyale kalar kimono din, ganin time d'in sallah yayi ta dauko hijab dinta ta gabatar da zuhr dinta a natse, bayan tayi addu'ointa ta shafa ta mike ta ninke sallayan da hijabin ta maida su mazauninsu, a hankali ta sauko downstairs hango Mama tayi gaban TV tana kallon hausa film ta duk'ufa sosai tana kallo, har gabanta taje ta gaida yar tsohuwar
'Mama ina kwana?" Ta d'an durkusa kasa. Mama ta harareta
"Gidanku! Kwana ne yanzu a garinku? Karfe 12 ta wuce kike ce mun ina kwana?"
Ware manyan idanunta tayi tana murmushi
"Aww yi hakuri Mama! Toh ina wuni?"
Ta kalleta na yan seconds sannan tace "Lafiya lau yal albarka kin tashi lafiya?"
"Fine alhamdullah, ya karfin jiki?"
"Alhamdullah"
D'an kalle kalle tayi "Mama ina Mummy?" Mama na murmushu tace "Tana sama d'akinta." Mik'ewa tayi tana murmushi ta koma sama bude dakin tayi a hankali ta shiga hade da sallama, zaune ta ganta bisa sallaya tana lazumi cike da farin ciki ta isa inda Ummu Sulaim take ta duka gamida rungumota ta baya "Mummy na!" Juyowa Ummu tayi tana kallon Sanayah tana murmushi "Ke! Ikon Allah zaki karyani ne?" Maimakon Sanah ta bata amsa sai kawai ta mata peck a kumatu "Mummy toh in ban karyaki ba wazan karya?" Ta fada tana turo dan bakinta, dariya taba Ummu ta shafa fuskanta "Toh naji, kinyi sallah?" Sanah ta gyada kai "Nayi..." Ummu tace "Toh tunda sai yanzu kikaga damar tashi sai kije kici abinci" Sanah tayi y'ar dariya "Kai Mummy yau fa weekend sheyasa nak'i tashi" Ummu ta kalleta "Jimun yarinya ke dama kullum ay weekend ne a wurinki, tunda kika gama WAEC sai kace makaranta kike zuwa, islamiyya ma kin sauke, toh mey kikeyi da har zaki wani ce ay yau weekend...?' Dariya sosai Sanah tayi "Toh am sorry Mummy na, dana shiga university ay zan daina baccin safe ko?" Ummu ta girgiza kai tana murmushi, Sanah tace "Yawwa Mummy daman Samra ta kirani wai na shirya zamu fita..." Cike da damuwa Ummu tace "Ina zakuje?" Sanah tace "Wallahi I don't know Mummy, kuma ban tambeyeta ba."
"Ikon Allah, toh Allah ya tsare a kula don Allah Sanayah, kuma ku dawo da wuri please..." Sanah tayi releasing d'inta daga hug din data mata tace "Inshaa Allah Mummy na thank you." Mikewa tayi tana shafa shafaffen cikinta tana turo baki "Mummy am soo hungry bari naje k'asan" Ummu tace "Better kam."
YOU ARE READING
AKAN Y'ATAH. COMPLETED
General FictionAKAN Y'ATAH LITTAFI NE DA YA KUMSHI ABUBUWA DA DAMA, AKWAI DARUSSA A CIKIN SHI DA, DANA SANI AKWAI RUDANI DA FIRGICHI DA BAN TAUSAI. BA KARAMIN ABU BANE BA LOKACIN GUDA KA GANO WANI BABBAN AL'AMARI GAME DA RAYUWAR KA, WANDA LOKACI GUDA YA TARWATSA M...