AKAN Y'ATAH

61 1 0
                                    


                           

Sorry please, wannan na kawo" ya Rabb his voice.... Sanah meye haka wai? Tama kanta fada, ta dago taga ya tsareta da ido, tayi saurin kar6an cups din dake hannunsa ta juya a hankali ta nufi kitchen, tana ji a jikinta kallonta yake sai kawai ta tsaya sink tana wanke cups din, tana tsakar wankewa ne taji mummy na kwala mata kira ta juya taga baya nan ta fito da sauri daga kitchen.din, "zasu tafi kizo ki kar6a number Hafsa ko?" Tace toh sukayi exchanging numbers sannan suka fito a tare, har bakin mota ta rakasu, Bilal ne ya tuk'o su Hafsa na gaba Hajiya Rabi na baya, sukayi ma juna bankwana sannan Bilal ya danna horn aka wangame masu gate suka bar gidan....

GOMBE STATE

Zaune take bakin gado tana share hawayen dake ta zuba a idanunta, in banda ajiyar zuciya babu abunda take, idanuwanta sun kumbura sunyi jawur don tsananin kukan da tasha, bata ta6a tunanin zata shiga irin wannan halin ba a rayuwa, babu k'asar da basuje neman haihuwa ba amma abun ya gagara, da ace kudi na siyen haihuwa toh tabbas da yanzu gidan su ya cika da yara, saidai kash! Allah ne ke bada haihuwa yana ba wanda ya ga dama, ya kuma hana wanda ya ga dama ba kuma don baison bayin shi ba, duk yanda Allah ya tsara ma bawa rayuwar shi toh yana da dalilin ba kuma don baya sonshi ba, sai dai don ya jaraba shi ne.

Sallamar da akayi ne ita ta dawo da ita daga tunanin data fad'a, ya dad'e tsaye yana nazarinta kafin a hankali ya tako zuwa cikin d'akin , kusa da ita ya zauna ya kamo hannuwanta cikin damuwa yana kallon ta, ko bai tambaya ba yasan kwanan zancen a hankali ta fad'a jikin shi ta fashe da wani irin kuka, hannuwan shi  yasa ya rungume ta yana bubbuga bayan ta na ban hakuri, saida tayi mai isarta tayi shiru don kanta sannan ya dago ta cikin muryan lallashi yace, "Hakurin nan dai da na saba baki shi zan sake baki Zaliha, kiyi hakuri ki daina saka damuwa a ranki, duk abunda Hajiyata zatayi maki ki daina sakashi a cikin ranki, kinji?"

A hankali ta fara magana cikin muryanta da ta shak'e don kuka tace "Alhaji kaima kasan Ina hak'uri, amma Hajiya kullum sai tayi min gori akan abunda bani da iko dashi, shiyasa kaga na dage akan ka kara aure ko na samu sauk'in wannan bala'in, ko ba komai nayi zaton Hajiya zata d'aga man tunda mima ai diyar ta ce, amma ashe abun ba haka bane. Kana gani saboda rashin haihuwar nan zumuncin mu ya lalace, shiyasa koda yaushe zuciya ta take cikin tsoro, Ina tunanin alhakin Ummu ne yake bibiyar mu." D'ago kai tayi tana kallon mai gidan nata bayan takai aya, wata irin zufa ta shiga tsattsafto mashi tare da wani irin mugun tsoro da ya bayyana akan fuskarsa, hulan kanshi ya cire yana fifita da ita dukda AC din dake aiki a d'akin, dukkan su sukayi shiru na yan seconds kowa da abunda ke damun shi a zuciya...
Mik'ewa yayi a sanyaye yana kallon matar tasa yace
"Ki dinga sa ma ranki cewa Allah ne mai yin komai, shine zai bamu haihuwa a lokacin da yaso sannan ya hana mu a lokacin da yaso, hak'ik'a ba wayon mu bane haka ma ba dubarar mu bace, hakurin nan da muka saba yi shi zamu cigaba da yi har sai yaga damar bamu..."
D'an murmushi tayi
"Alhaji kenan meyasa idan nayi maka maganar Ummu sai ka dinga son basar da zancen a cikin hikima?"
Ya koma ya zauna a sanyaye gabansa na dukan tara tara... "A...a'a...Zaliha ko kusa ba haka bane, Ummu tana nan mak'ale a cikin raina sannan duk sadda na tuna ta na kanji zuciyata na rad'ad'i, ina mata addu'a idan na tuna ta..." ajiyar zuciya ta sauke sadda taji kiran Hajiya har wani d'an razana tayi, da sauri ta mik'e ta fice gabanta na fad'uwa hakan take tsintar kanta a duk sadda Hajiya ta kirata... A parlor ta iske Hajiyar zaune da kaganta kaga yanayin bacin rai shimfid'e a saman fuskarta, d'an russunawa tayi alamar girmamawa tace, "Hajiya barka da hutawa, gani..." 
Wani kallo ta watsa mata sannan tace
"Sannu Gimbiya! Ah nace sannu Gimbiya! Wato dai na lura kwanan nan kin k'ara zama fitsararriya marar kunya ko? Bakida aiki daga ki shige cikin d'aki sai kici kisha ki kwanta kawai kika iya ko?" A hankali tace "Kiyi hakuri Hajiya wallahi ba haka bane yanzu na shiga ciki, cikin ma ban dad'e da shiga ba naji kina kira na" wani mugun kallo hajiya ta watsa mata, "Ko dayake ba laifinki bane, mijinki ne keda laifin nan shine yake d'aure maki gindi har kika samu damar raina ni har haka, yanzu haka yana cikin d'aki yana jinmu amma bazai fito ya gwada maki mahimmancina ba... Yayi daidai tashi ki bani wuri." w
Wasu siraran hawaye suka shiga zarya a kumatunta.
"Kiyi hakuri hajiya idan har na 6ata maki rai, " Hannu Hajiya ta daga mata "Da Allah dakata! Saidai kar a kuma kawai ki tashi ki 6ace man da gani..." Hawayenta ta goge sannan ta mik'e a hankali ta bar parlorn inda tana ji Hajiya na cigaba da fad'anta.

AKAN Y'ATAH. COMPLETEDWhere stories live. Discover now