page 04

290 17 0
                                    

Dr. Laylah.

04.

Tafiya mintoci goma sha biyar ya kawosu bakin babban kogin mai suna Mashaya. Hak'ik'a kogin abar kallo ce, mai tsawo da fad'i ce wanda iya hangen Laylah bata hango karshenta ba, samanta babban gadace wacce ta ginu da kankare tare da manya duwatsu daganin kasan aikin turawa ne na dogon zamani dubi da yarda salon ginin ya bayyana kansa cike da fikra. Gefenta gonaki ne suka kewayeta wanda suke cike da shuke-shuken kayan lambu da rake ga kuma bishiyoyi manya masu yalwar ganye sai kadawa suke yi sai wurin ya k'ara fidda ni'ima na musanman.

Iya burgewa kogin Mashaya ya burge Laylah musannamn ganin yarda da ta ke hango k'asar ruwan dauke da yashi mai haske da kananun tsirrai, sauke numfashi ta yi cike da jin natsuwar huri, dik zuwar da ta keyi garin bata tab'a ziyartan wannan kogin ba sabida lokuta da dama bata kwana.

Zama ta yi a gefen ginin gadar ta zira gafafu ciki amma bata tabo ruwarba sabida inda ta zauna ya yi nesa da ruwan amma tanajin motsin gudun ruwar hakan ya kuma jefata cikin nishad'i.

Hargowar matasan yanmatan ya ja hankalinta, dik sun tubo kayansu sun koma daga su sai shimi da gajeren wando wanda faruwar hakan ya tabbatar wa da Laylah sun shiryawama yin wanka tundaga gida. Ihun fadawarsu cikin ruwan ya tsorata ta ta mik'e da sauri Maryama ta kyalkyale dariya ta kalleta cikin watso mata harara ta ce "Ka da ki sa ke inganki cikin ruwarnan."

"Ai bazan shiga ba dan tsoro na keji ban iya iyo ba."

"Gara haka suma zanyi masu nasiha da su daina bai da kyau shiga irin wannan kogin mai girma."

"To Allah yasa su ji dan anyi fad'ar har nagaji sunki dainawa."

"Zan jaraba tawa sa'ar nagani."
Gyad'a kai Maryama ta yi cikin maida hankali kan kawayenta da ke ta wasa cikin ruwa kamar kifaye.

Fidda wayarta Layla ta yi ta kunna tare da sanya plane mode gudun ka da akira ta, video tasoma yi musu suna ta iyo cike da kwarewa lamarin ya kuma daure mata kai ganin yarda su ke abin tamkar suna gasar tseren ruwa. Bayan wani lokaci biyu suka fito sunayiwa Maryama dariya itama tana yi musu cikin bazata suka tura ta ciki ta kwalla ihu Laylah ta zabura jikinta na rawa su kam sai dariya suke yi Maryama na son fitowa suna kuma janyota ciki hangowa da Laylah ta yi yarinyar na fidda numfashi da kyar yasa ta daka musu tsawa.

"Ku sa ke ta na ce! Ka da ta mutu."

Sa kinta sukayi ta fito jikinta na rawa ta fashe da kuka suka kuma sanya dariya tare da cigaba da wasaninsu cikin ruwar cike da nishad'i.

Hijabin daya daga cikinsu Laylah ta daukowa Maryam ta rufe jikinta tana kallon fuskanta ta ce "Sorry dear da fatan ba kiji ciwo ba?"

Da kai ta amsa lamarin da ya bawa Laylah dariya ta musmusa tare da lumshe idanu tana hasko wani lokaci da ya shude kwatan- kwacin hakan yafaru da ita a swim pool din hotel din da ta gabatar da bikin murnan zagayowar ranar haihuwar ta inda Saifuddeen ya turata cikin ruwa tanemi mutuwa sakamakon fadawan bazata da ta yi saidai ita shi ya cirota da kansa sannan zaratan samari uku ne suka cire jacket nasu suka rufe mata a jiki cike da nuna kulawa

Girgiza kai ta yi tare da sa ke fad'a d'a murmushinta domin ji ta yi tamkar yanayin ya dawo wannan lokacin.

" Yaya Laylah ta shi mu tafi gida zazzab'i na son kamani." Maryama ta ambata hakoranta na had'uwa da juna.

Numfashi ta sau ke ta mik'e a hanzarce tare da rik'o hannun Maryama suka soma tafiya ganin haka 'yanmatan suka fito da sauri suka maida kayansu suka rufa musu baya Indodo wacce Maryama ke sanye da hijabinta ta yafa gyalen Maryama da ya jike.

"Baku kyautawa kawarku ba, kun san bata son ruwa tsoro kogin ke bata me ya sa zaku turata ciki?"

Shiru sukayi cike da nadama ganin yarda ta ke rawar sanyi, tafiyama da kyar ta keyi.

Doctor Laylah.Where stories live. Discover now