Mutuwar masoya

19 2 0
                                    

birnine mai dauke da Kauyuka da dama wadanda wazirin garin ke azabtar dasu ba tare da sanin sarkin garin ba daga cikin kauyukan nan akwai wani kauye wanda ake kira MIRAD akwai wani yaro shi yaron Nan yakasance baya jin magana Yana cikin tafiya Sai ya hango wata babbar masarauta kawai sai ya tunkareta Kai tsaye amma masu gadinta suka hanashi shiga kullum haka yake kokari wajan shiga Amma su hanashi watarana Allah ya taimake shi yasamu ya shigaKinsan abinki da mutumin da baitaba kallon Abu ba kawai yashiga yawo a cikin wannan masarautar Yana kewayawa masarauta ce wacce aka mata ado da kyawawan fure masu kamshi Yana cikin tafiya sai ya hango wata kofa Kai tsaye ya tunkareta cikin nutsuwa yashiga cikin Yana shiga sai yayi karo da wani babban lambu mai dauke da kayan marmari kala kala ya cigaba da tafiya a cikin wannan lambun Wanda ya kasance yana dauke da ciyayi koraye masu kada wata iska mai sanya nutsuwa .A Cikin wannan yanayin ne ya hango wani Abu sanye da fararen kaya gashi Yana dauke da haske tsaye yake gaban wani korama Wanda ruwa ke gudan tsakanin duwatsu shi kansa ya tsorata Amma yayi karfin Hali yakarasa domin Ganewa idanuwansa kafin yakara sai yaga abin yatashi tsaye alamun yaji motsin wani Abu Nan yasamu bayan wata bishiya ya buya domin ganin zahirin abin mamaki sai yaga Ashe macace bawani Abu ba domin Tana gama tashi yaga gashinta ya bayyana cikin mamaki yayi a jiyar zuciya sannan a cikin zuciyar sa yace Kai Amma wannan aljanar kyakkyawa ce Ina ma zata juyo Naga fuskarta Yana cikin wannan tunanin kawai sai yaji wasu manyan mutane sun rufemasa idanuwana sannan suka daukeshi ihun da yayi shiyasa ta sake zabura ta juyo cikin hanxari ta karaso tacewa fada wanta wato mutunan da suka kamashi waye wannan din jin muryarta dayayi yasa yayi a jiyar zuciya yace Kai wannan muryar tamkar sautin sarewa take da ita kadai ma ai mutum zai iya rayuwa ba tare da yane mi wani abinci ba .shi kansa baisan bakinsa ya furta hakan ba Nan fa fadawan Nan suka haushi da duka tamakar zasu kashe shi Amma duk dukan da suke Masa shi burinsa kawai a bude Masa idanuwansa yaga wannan mai daddar murya haka.

mutuwar masoyaWhere stories live. Discover now