1

225 12 0
                                    

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_

        *🅿️1*

Shimfida..!

Shekara ta alif dubu biyu da goma
2010

*BIRNIN KEBBI..*
_jega local goverment_

"Cikin wata Anguwa da ake kira Sabon gari dake cikin Babban garin jega local goverment dake Cikin Babbar Jahar nan ta Birnin kebbi,acikin Shekaran ta Dubu biyu da goma.

Wani matashin gida nagani ginin Kasa,Wanda akama Shafen Fentin Farar kasa Daga gaban Gidan zuwa baya,gidan bashi da girma Sosai Daga yanayinsa zaka Fahimci mazauna gida dai suna Fama da Rayuwa sai dai godiyar Allah.

Wata yar Tsohuwa ce mai Akallah Shekaru 60 aduniya,Farace ammh ba Farin nan na Sosai ba yadda Duk jikinta yayi zaka Fahimci Tsufanta yayi Saurin bayyana sai kace yar Shekara 80 Saboda Wahala Zaune take atabarma a Kofar dakinta wanda keda labulen kaba kulle kullenta ne Data saba na yau da kullum agabanta irin su kuka,kubewa,Daddawa,citta kanunfari,komai dai na kayan mata na cikin gida,tsohuwa Bara"atu wacce Jikanta ke Kira Kaka tana saidawa Domin Rufama kanta asiri ita da marayan Jikanta wanda Iyayensa suka mutu suka barta dashi kwara daya Tal.

Ta Dukufa tana faman Kulle kullenta Lokaci daya tana Rera wakarta Ahhayye sama Ruwa...Ayyahhhe sama Ruwa kasa. Ruwa..Mata mata..,take fada Lokaci daya kuma takoma tana Fadin "Mata akama Sana"a mata Macen da bata Sana"a Saunace Lale lale maraba da lale Saunace.."

Take Fadi lokaci daya tana Bantalan Goronta datake lalubowa cikin Katon wani Yadi wanda aka mata katon Lalita nan take Zuba komai nata ciki kuma koda yaushe yana kugunta ko barci take Dashi takeyi Kaka bata da yarda ko kadan balle Sha"ani na kudi bata da Wasa kaka akwai neman na kanta.

AHMED yana daga cikin karamin Dakinsa Dake kallon na Kaka Zaune yake bisa wata yaloliyar katifarsa mai kama da Tabarma Dakin babu ko leda ammh yana Share Tsab Daga gefe sai Tarin Littafan karatun boko dana Arabi,Daga yammah kuma Wata jakace karama wanda kayansa ke ciki  sai gefe kuma Takalmansa ne Wadanda sukaji jiki guda uku ke Da mazauni awajen.

Karatu yake ammh Sam Hayaniyar kaka ya hanashi Sukuni Gabadaya Dagulamai Lissafi take kamar wata budurwa yar Shekara goma ta Zauna tana Wani Rera waka Tsaki yaja kafin ya mike Lokaci daya yana kwafa Kansa ya Dafe saboda Atsarinshi bayason Hayaniya gashi ita kuma kaka yar Hayaniya ce yafi kowa sanin yana mata mgana Sai dai karshenta ya bar gida nan in kaka ta Fara mita har gobe da Safe ajiyar zuciya kawai ya Sauke  lokaci daya ya karisa kofar Dakinsa yana kokarin Sakin Labulen kaban dake Daure asama.

Kaka ta dago ido tana kallonshi Baki Ta tabe kafin tace"Kai dai Wlh Ahmadu kaji Haushi ko Mace bata kai ga gulma da Tsegumi ba.."yana jinta ya mata banza sai ma Sauke Labulen kaban dayayi ya koma ciki da Harara ta bishi tana Fadin"wlh naso kayi mgana daka ga Tijarata Sabuwa acikin gida nan Dan Kusan Uwa...Yaron nam sam Bansan meke damunsa ba na Lura matattaciyar Zuciyar Uwarsa Zaliha ya gano domin dai  Sama"ila irina ne akwai Zuciyar neman na kai..."Tafada Lokaci daya tana saka gora abakinta ta gatsa yana jinta ammh ko Niyyar Fitowa baidashi saboda Sanin Hallin kaka ba bakon Abu bane Shekaru fin Ashirin yana Tare da ita yafi kowa sanin Halinta Shigen son ta Tara kudi ko ta halin kakane Mganar neman nakai bazai karyataba Kaka akwai zafin nema Domin dashi take ci dasu tasha dasu kuma acikin neman natane ma Ya samu ya Shiga Kolejin Horas da malamai ta Burnin kebbi Wato Federal Collage of Education Birnin Kebbi.

"Kaka..Wayyo Kaka na Shiga uku..."Wata Budurwan yarinya ta Fada wacce ta Fado Gidan kamar Daga sama a kallah bazata Haura Shekara 19 aduniya ba Ammh Daga yanayinta zaka Fahimci ta Fito Daga gidan Jin Dadin,Tundaga kayan alfarma dake jikinta na wata Doguwar Rigar kirar Armani wanda ta yafo karamin mayafin kayan Doguwa ce mai matsaikacin jiki,Tana da kyau daidai Gwargwardo,Zabura kaka tayi tana Binta da kallo lokaci Daya tana Fadin"Ke SAMIHA lafiyanki kuwa kika Fado man gidan kanki Tsaye ba Sallama ko wannan Tsohon naku ne ya sheka wanda bai fittar da Zakka balle Hakkin Makota ka.."?

SILAR HALACCIWhere stories live. Discover now