page 09

177 11 0
                                    

Dr. Laylah.

09.

Mafarin rigimar Maimunatu dani shi ne sanadin komawana kauye da zama, ta yi ta masifa akan me zan koma zaman k'auye alhalin na taso a birni. Gwaggo na nuna mata aure ba inda bai kai bawa amma ta rintse ido ta zo har kauyen nan akan sai na bita na dawo birni da zama ta yi alk'awarin zata siya mana gida domin lokacin ta soma kama kudade masu kauri, Malam ya ce ya gode amma ba zai koma Zaria ba sabida umurnin mahaifiyar sa yafiye masa komi na duniya, ta kuma hasala ta ce in taho mu tafi ta maka shi a kotu a raba auren nikam na ce ina son mijina ba zan bita ba, a karshe dai ta bar garin tare da cin alwashin bata kara zuwa daga ita har yayanta. Hakan kuwa ya faru Maimunatu bata kuma takowa zuwa gareni ba har na shekara uku a garin sai dai ni na kanje gareta dik in na kaiwa Gwaggo ziyara ko in ta sami k'aruwa dik da ban ganin fuska a wurinta hakan bai tab'a damuna ba domin nasan ladana na ga Allah na sada zumunta. Lokacin dana samu shekara biyar da aure Allah ya bani rabo wato nasamu cikin Baban Maryama sai na dawo wurin Gwaggo sabida ina shan wuya to a wannan zuwan ne Kakarki yaya Abba ya kawo ma Gwaggo ziyara kamar yarda ya saba yaga halin dana ke ciki a ta ke ya daukeni bisa amincewar Malam ya maidani Kano ya samarmin da likitoci na musanman suka rik'a kula da ni har tsawon wata uku zuwa lokacin na sami lafiya domin da kaina na nemi zan koma d'akin mijina ba tare da komi ba ya shirya min shatara na arziki ya kawo ni wurin Gwaggo ita kuma ta maidani d'akina hankali kwance. Zamana a Kano ya sanya mun shak'u da mahaifiyarki dama sauran yaran domin Yaya Abba ya nuna musu muhinmancina sama da nasa kuma sun amince bisa jagorancin iyayensu masu biyayya ga abinda mijinsu ke so. Ban k'ara shiga farin ciki ba saida naga Yaya Abba tare da Hafsatu ya kawo ta wurina musanman hutu, tayimin sati d'aya ya zo ya d'auke ta, wannan zuwan da Hafsatu ta yi gareni ya k'ara hura wutar tsanata ga Maimunatu domin a she Yaya Abba ko Gwaggo bai sanarwa ya kai Hafsatu wurina ba sai ranar da yazo d'aukan ta suka gansa tare da ita, na samu labari Gwaggo har da kuka ta yi sabida jin dadin ziyarar da Hafsatu ta kaimin yayin da maimunatu ta yi ta yada magana har saida Yaya Abba ya ci mutuncinta sannan ta yi shiru.

Bayan wasu watanni na sauka lafiya, Yaya Abba ya tattaro ilayinsa dika suka zo suna, kwanarsu d'aya suka koma sabida karatun diyoyinsu ya yin da 'yar uwata Maimunatu ko lekau batayi ba hasalima tana jin na haihu ta san Gwaggo zata ce sai tazo ganin jariri sai ta yi hanzarin yin visa ta tafi Umrah da yaranta kafin zuwa ranar suna. Zuwa lokacin tana da yara hud'u, uku maza, mace d'aya. Bayan ta dawo ne Gwaggo ta sanyota gaba zuwa inda na ke, na yi murna sosai da sake ganin ta a muhallina sai dai Maimunatu ta saccemin guiwa inda ta k'i cin komi hatta da ruwa bata sha ba wai k'yan-k'yami ta ke ji, na zubda hawayen takaici ya yin da Gwaggo ta fusata ta soma yi mata fad'a mai makon ta gane kurenta sai ta sa ke hawa ta yi inda ta dau alk'awarin ita da ta sa ke takowa inda na ke sai wani ikon Allah, a ranar Gwaggo ta yi da ta sanin tursasa mata tazo ganina domin iya kunya ta bamu ga ban al'umma.

To kinji dalilin da yar uwata ta gujeni ita da zuri'arta amma ni har kwanar gobe ina zuwa gareta haka yaranta na kan lek'a gidajensu lokaci zuwa lokaci domin inayin komi dan samun lada ne ba dan arzikinsu ba wanda ban shaida ba tunda daga ita har su ba wanda ke iya bani kudin mota balle tallafi a matsayina na wacce ke zaune a karkara alhalin dik shekara suna fidda zakka, idan sun kaiwa Gwaggo ta kan debomin dik da bana so amma ban tab'a kin amsa ba sai dai idan na zo gida in rabawa jama'a ko da kuwa ina son abin ban taba yarda inyi amfani da shi sabida ina ganin kamkar na je maula ne gareta abinda na roki Allah da ka da ya bani damar aikata wannan kaskancin gaban Maimunatu, kuma alhamdulillah tunda dan uwana wanda muka hada uba d'aya ya sharemin hawayen kukan babu ta ko wani fuska tare da d'iyarsa da jikansa."

"Ikon Allah, yanzu Mama akan abinda bai kai ya kawo ba ta zab'i b'ata lahirarta tana sa ne?"

"Uhm ke kenan Laylahtu da ki ke da hankalin nunanin hakan domin Maimunatu ta wuce tunaniki indai akan lamari na ne."

"Amma banji dadin abin ba musanman akan yarda ta dora su Murjana a wannan hanya mara b'ullewa."

"Wallahi ba komi Laylatu sabida ina da zuri'ar Yaya Abba musanman Hafsatu wacce ta dauko komi na mahaifinta ga shi ta nunawa zuri'arta inda ni ke har gashi yau kina zaune  dani na lokaci mai tsawo batare gajiyawa ba, hak'ik'a ina alfahari da hakan kuma zan kasance cikin alfahari da shi har zuwa karshen rayuwata."

"Mama ai da kauye da birni dik abu daya ne sai dai bambancin wayewar kai sannan ita birnin da asalinta kauye ne."

"Tabbas haka zancenki ya ke Laylatu."

"To Mama me yasa ta ke yawan yiwa Momy fada wai tana nuna bambanci tsakaninku? alhalin ke din kinfita buk'atar kulawa domin tafiki dukiya da komi na more rayuwa sai na ke ganin dan Momy ta baki kulawa sama da ita ai bakomi ba ne domin ita din mai baki ne kuma murna ya kamata ta yi ba nuna bakin ciki ba."

"Ai wannan hassada tsaka ni na da Maimunatu halittacce ne domin tun kafin muyi aure ta kance Gwaggo tafi sona sannan lokacin da Yaya Abba ya biyamana hajji ni da Malam itama saida ya biya mata sabida zaman lafiya domin tana samun labari ta soma ruwan bala'i shi kuma yana ji ya aiko da sakon itama ya biya mata sannan lokacin da aka haifeki ni na zauna da Hafsatu har aka yi arba'in, to tukuicina wurin mahaifinki shi ne ya biyamin Umrah kinji dalilin da na ke kiranki da hasken alkhairi domin a wanna zama jego naki mahaifiyarki ta mallakamin dukiya wanda na sai shanu da shi sukayi ta hayayyafa har gashi yau kina shan madararsu."

"Ikon Allah kenan." Laylah ta ambata cikin murmushi sabida lamarin ya faranta mata rai ainun.

"Laylatu dole Maimunatu ta yi ta maganganu akan mahaifiyarki sabida mahaifinki bai tab'a yi mata kyauta ba dik kuwa da shi din hannunsa a sa ke ya ke, ta kan cewa Gwaggo asiri na yi muku ku ka fi sona, Gwaggo kan amsa ta da cewa ta yi din kema ki tafi kiyi, mara godiyar Allah kawai, ke idan baki bawa Zainabu ba ai ba zaki zamo cikin masu yi mata hassada ba domin kina da kudin kaita makka da umrah amma kin k'asa hasalima ko kyautar dubu goma bai taba hadaku ba daga ke har yayanki kin nuna musu ita da banza dik daya alhalin tafi kusa da ke akan kowa na duniya.

Wadannan kalamai na Gwaggo sun kuma taimakawa kwarai wurin sa ke birkita zumuncinmu wanda har jikokinta suka maye gurbi, domin har yau ba wanda ya tab'a takowa inda na ke domin gaisheni cikin zuri'arta amma ina samun labari dik hutu sai sunje Kano da Abuja gidan Mariya."

"Allah ya kyauta kawai za'a ce amma gaskiya Mama Maimunatu bata yi ba sam."

"Ba komi Laylatu ina fatar ganin wata rana mun zamo abin kwatance tare da koyi da mu akan rik'on zumunci."

"To Allah yaso hakan Mama."

"Amin."

Gyara zama Laylah ta yi cikin yar dariya ta ce "Mama idan zan koma ki bani Maryama mu tafi tare ta yi karatunta tunda na fahimci tana son yin ilimin boko mai zurfi."

"Kayya Laylatu ai Maryama aure zamuyi mata domin ita ce jigonmu na fatar samun zuri'a mai yawa, kinga tundaga kan mahaifinta ban kuma samun haihuwa ba, ita ma tundaga kanta iyayenta basu sa ke samun rabo ba, to muna burin a tsatsonta mu sami zuri'a da yawa kinga kenan rayuwar birni banata ba ne aure zamuyi mata da zarar ta kammala k'aramar secondary."

"Wato dai Mama yarda bakiyi zurfi akaratun boko ba shi ne itama Maryama kike son ta tsaya iya inda kika tsaya?"

"A'a Laylatu, ki fahimceni mana."

"Nikam na fahimce ki kuma ni sai na tafi da ita wurin Momy dan Malam zan tambaya da Uncle Kasim, suna amincemin magana ya kare."

"Ai ko su sai sunyi shawara da ni tunda ni ne jigon amincewar."

"Oh Mama shugaba kenan, to da Dady zan hadaki kinga dole ki bari in tafi da ita ko dan kunyar surukinki." Ta ambata cikin dariya.

"Amsa na ki na ce, yar nema kawai, wallahi kika kuskura kikayimin wannan ta'asar ba ruwana da ke."

"Oho dai na dai kusa komawa kisha ke wata ba mai tayaki."

"Uhm ke dai bari kawai Laylatu wallahi har ban son na ji kina ambatar tafiyan nan."

"Bakomi Mama ai muna tare zan dinga zuwa ganinki akai-akai tunda gashima na hango karuwa a garin dan ya kamata a samar da masana'anta wanda za'a rik'a sarrafa rake zuwa mazar kwaila, insha Allah za'a sami alkhairi a cikinsa, sai Kawu Kasim ya rik'a kula da wurin tare da sallaman ma'aitaka, kinga ya sami sauk'in zuwa gona sai dai ya biya ayi masa aikin gonar hankali kwance."

Shiru Mama ta yi ta tsirawa Laylah idanu wanda suka kawo ruwa ganin haka yasa Laylah ta mike ta fice tana kiran Maryama dan ta zo su fita bayan gari sabida ta kan sami nutsuwar ruhi tare da koyon wasu lamuran rayuwa wanda ada ta ke d'aukansu da gidadanci."

Doctor Laylah.Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz