4
SUHAILAHNA NANA DISO
https://arewabooks.com/u/nanadiso10
Rigar jikinta ya fizga ta yage sannan ya cillata kan gadon dakin yana kokarin rabata da bra din jikinta...
Wani kuka gimbiya suhylah tasaka mai cike da tashin hankali da damuwa hankalinta gaba daya yatashi yadda take tureshi tana cizonshi yasa hankalinsa yakara tashi.....
" cikin yanayin da shi kansa shareef yakasa fahimtar sa yakai bakinsa kan nata yafara sumbatar ta cikin yanayin da bai taba tsintar kansa ba ...
Wani cizo gimbiya suhylah tayi masa tanata kokarin tureshi amma ina ta kasa yana kokarin kai hannunsa kasan mararta kenan sai gashi anbude kofar dakin...
Babu abunda yarima khalid yafara ambata sai innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Kalmar da yafara ambat kenan sannan yaja kofar ya rufe...
Shareef ne ya mike tsaye idanuwan sa sunyi jajir sannan yace nasan wannan dan iskan mutumin sakin ki zaiyi na aureki ko yanzu burina yacika amma duk da haka sai na rabaki da budurcinki...
Wani irin kuka suhylah tasaka sannan tace Allah ya'isa tsakanina dakai ban yafemaka ba kuma yadda kayimin Allah sai ya sakamin...yaya shareef ba haka kake ba me isa bazaka yarda da kaddarar rabuwa dani ba? Mai martaba yazaba min miji an dauramin aure shine wannan tukwuicin da zaka bani kenan? Wannan itace soyayyar dakakeyi mini?
Kofa ya bude tare da jan tsaki sannan yafita yabar harabar gidan...
Khalid ne yasa kuka yana fadin yaaAllah ka yafemin ya Allah duka matan biyu babu tagari ya Allah wannan itace zabin baffa wannan mara kamun kai jiya aka daura mana aure yau da idanuwa na naganta tana zina da wani!!! Wani kuka yasaka wanda kowanene yaganshi yasan yana bukatar taimako bai idda hawayen sa nafarko ba wayar yazid amininsa ta shigo cikin kasallaliyar murya yace abokina mun shirya komai na dinner fa...
" yarima khalid ne yace yazid na fasa dinner!
"Haba yarima kada kace haka kasan fa munada baki daga garuruwa fa kuma mai martaba sarki mahaifin amaryar ka ance ya shirya walima shima..
" To yace tare da kashe wayar...tunda yafara ganin suhylah yaji tashiga ransa sannan irin matan da yake bukata kenan cikin matsanancin damuwa ya dauki mukullin motarsa yasanar da jakadiya tayiwa suhylah magana don yanzu zasu huce...
Jakadiya ce takara bangaren su gimbiya suhylah tasanar mata da sakon mijin nata...
Gimbiya suhylah cikin rashin karfin jiki da damuwa ta wanke fuskarta wacce tayi jajir kana ganinta kasan taci kuka hijjabin ta tasaka sannan tafesa turarukanta tafita zuwa gurin mai martaba...
Tana shiga ta hangi khalid a zaune gabanta ne ya buga sannan takarasa tace Allah yaja da ranka babana gani...
Mai martaba cikin fara'a ya kalli yarima khalid yace kai yarima wannan diyata ce suhylah kamar yadda nasanar maka amana ce agareka ban yarda ka rabu da ita ba ko bayan raina kuma ban yarda ka wulakanta ta ba kayi musu adalci azaman su sannan ka kula dasu suhylah yarinyar kirki ce kuma mai hakuri ce...
" khalid ne yayi dogon numfashi aransa yace hmm bakasan ma zinaciya bace shiyasa kake fadar haka akanta...
Mai martaba ya kalli yarima yace ina kuma nemar mata alfarma taciga da makaranta...
Cikin ladabi irin na yarima khalid yace duk yadda kace haka za'ayi mai martaba nakuma gode da kabani diyarka Allah yasaka da alheri yakara girma...
"Cikin isa yace ameen..
"Suhyla dai babu abunda takeyi sai kuka ta tunanin irin sabuwar rayuwar da zata fara dashi...
YOU ARE READING
GIMBIYA SUHAYLA
RomanceWANNAN LABARI YANA MAGANA AKAN KALUBALE NA MA AURATA AWANNAN ZAMANI TARE DA KAUNA DA HADARIN MUGUNTA GA TSANANIN SOYAYYA GA KUMA RUDIN SHAIDAN DA KUMA ILLAR RASHIN SAUKEWA JUNA HAKKINSU DA MA AURATA SUKEYI..