👸🏻👸🏻
GIMBIYA SUHYLAH👸🏻©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers*MALLAKAR:- NANA DISO*
*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*
*8*
Tunda suka dawo khalid yashiga dakin gimbiya suhylah ya shiga toilet yayi wanka yafito dauke da towel ajikin sa..
Suhyla dake kokarin idar da sallah tana daga kanta taganshi sai da jikinta yayi wani yar amma sai ta sunkuyar da kai...
Yarima khalid ne yayi tsaki yace da ace haka kike a gaske da kinji dadi mutane dayawa suna miki kallon mace kamammiya basusan kin zubda mutunci a waje ba har mahaifina kin yaudara da wannan ladabin naki...
Suhylah da fuskarta ta cika da hawaye tace banyi tunanin zaka jefeni da wannan kalmar ba wallahi ni ba 'yar iska bace ban taba zina ba wallahi allah..
Wani irin tsawa yayi mata sai da hantar cikinta ta kada yace ni zakiyiwa karya? Nagani da idona sannan ki tsaya zakiyimin wata karya..
Yayana wallahi baka aure mutuniyar banza ba ni mutuniyar kirki ce kuma kuma...
Ya isa haka bana bukatar jin komai daga gareki yajaa tsaki ya kwanta akan gadon...
Shi kansa jikinsa sai dayayi sanyi saboda bayason wulakanta ta ko don mai martaba amma abunda yagani bazai taba gogewa acikin ransa ba...
Suhylah da tafashi da wani matsanan cin kuka tana fadin yaaAllah kanagani kuma kanaji Allah kadubini yaaAllah...
Har ta kwanta akan dadduma sai ta tuna fadan mumy na cewa kada ta sake ta raba shinfida da mijinta komai fadan kuwa da zasuyi domin yawan jin dumin juna yana kara kauna da shakuwa ..tashi tayi ta Cire rigarta ta kwanta..
Tunda suhyla ta kwanta khalid yaji gaba daya hankalinsa na kokarin gushewa don gabansa ya riga ya miki..
A hankali ya sauka daga kan gadon yasamu guri ya kwanta a kasa..
Suhylah da zuciyarta ke harbawa tasa kuka har lokacin da bacci ya kwasheshita...
Yarima khalid ya matsa gaban gadonta yana binta da kallo cikin ransa yace baki kyautamin ba suhylah na dade inasonki tun kafin shareef yasan dake agidan...
Shareef dake juyi akan gadon idanunsa sunyi jajir ga zuciyarsa cike da kaunar suhyla yarasa yadda zaiyi da ransa can kuma yace wannan abun da nayi miki nasan khalid bazai taba kusantarki ba kuma nasan komai daran dadewa zai sakeki na aureki suhylah ke tawa ce har abada bazan taba rabuwa dake ba...
Wata zuciyar tace amma baka kyauta mata ba da har kayi kokarin tozartata... tsaki yaja sannan ya kwanta..
Da safe mai martaba sarki farouk yatara dukkan iyalan nasa hajiya babba daman yaranta uku..hajiya fatima datake amarya daman bata taba haihuwa ba,shiyasa hajiya babba take abunda taga dama acikin masarautar don tana tunanin ai yaronta ne zai gaji sarki farouk..
Sarki ne yayi gyran murya inda kowanne ya nutsu sannan yace yarima khalid shine babban dana kuma shine magaji na...
Hajiya babba ce gabanta ya buga..
Sannan yaciga da cewa kamar yadda kuka sani matar dana fara aura tun mahaifina sarki ado yana kan mulki ita ta haifa min shi sannan na kaishi garin binne inda yarayu da baffan mahaifiya kuma shi na aurawa gimbiya suhylah
Gimbiya Fatima diyar sarki tace amma suhylah..
Aka dakatar da'ita da magana sannan yace suhyla ba diyata bace ba kuma ba jina bace ba nan yabasu labarin komai da komai...
Bai karasa magana ba hajiya babba ta suma ba'a tsaya ko'ina ba sai asubuti..
*FITATTU BIYAR NA KUD'INE.*
*FEEDOHM - SILAR WAYE?*
*ZAINAB BAWA- YARIMA FAYAD.*
*ZEE YABOUR - DR MUHRIX.*
*HAJJA CE - ANNURIN ZUCIYA.*
*NANA DISO - GIMBIYA SUHAYMA.*LITTAFI BIYAR AKAN___500,
IDAN HUDU KIKE SO___450,
IDAN KUMA UKU NE___400,
IDAN BIYU KIKE SO___350,
IDAN KUMA D'AYA KIKE SO 200.!TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT D'IN.
3126584401 FIDDAUSI MUSA FIRST BANK TARE DA SHAIDAR BIYA A 08036953516
KO KUMA.
ACCOUNT NUMBER:-0003075326 ZAINAB M BAWA
Jaiz bank SHAIDAR BIYA TA 08161146563.*KO KATIN MTN TA WANNAN LAMBAR 07065283730 TARE DA SHAIDAR BIYA.*
*SANNAN MUYI ADDING D'INKI A FITATTU GROUP🌹...*
NANA DISO
YOU ARE READING
GIMBIYA SUHAYLA
عاطفيةWANNAN LABARI YANA MAGANA AKAN KALUBALE NA MA AURATA AWANNAN ZAMANI TARE DA KAUNA DA HADARIN MUGUNTA GA TSANANIN SOYAYYA GA KUMA RUDIN SHAIDAN DA KUMA ILLAR RASHIN SAUKEWA JUNA HAKKINSU DA MA AURATA SUKEYI..