shafi na shida

196 15 0
                                    

*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

*©OUM MUMTAZ*

        *6*

********Ahmed saurayin Janan ma yazo ta'aziya,da yake shidin ma a cikin garin Kadunan dama yake a unguwar Malali, sosai soyayyar Janan d'in da kuma tausayinta ya k'ara samun muhalli mafi girma a cikin zuciyarsa, dik wanda yaga Janan a t'sakankanin way'annan kwanakin saiya tausaya mata, dama gata nan ne babu auki kasancewarta mai karamin jiki, sai kuma gashi ta k'ara zubewa sosai ba kad'an ba.

3ples Mammi ce taci gaba da kula dasu tare da taimakon Umaima, little Hanan dama kwata-kwata bata da hayaniya ko kad'an,masu yin k'ananun kukan dama yara mazan ne wato Ameen da Adnan. Y'an uwa da suka zo dik an wat'se tas,sai inna Zainaba da itama takan taimaka ma Mammi da kula da sauran yaran idan y'an rigimarsu ta mot'sa, gida dai kam gashi nan ya sake zama so silent,idan kaji d'an hayaniya to a shashen Mammi ne,kuma shima sai idan rigimarsu ta d'an mot'sa ballantana ma yanzu dasuke cikin watanninsu na takwas da haihuwa sunyi b'ulb'ul abinsu.

A yau da akayi kwana bakwai da rasuwar Mammi Abba ne ya aika direbansu mai suna Lamid'o kan yaje ya d'akko masa Nuraaz daga makaranta shi bazai sami damar zuwa ba sbd uzirirrika sun masa yawa kuma an masu hutu a wayewar garin yau d'in, zaune Mammi ,Janan ,Inna Zainaba da kuma 3ples da Umaima take ta faman masu wasa tare da Janan da take tayata yi masu wasa cike da k'arfin hali,sabida har yanzu mutuwar mahaifiyarta bai gama sakin jikinta ba, Mammi kuma suna d'an hira da Inna Zainaba irin na t'sakanin y'a da uwa.

Sallamar da suka ji daga bakin k'ofa ne yasa su maida attension nasu kan k'ofar baki d'ayansu had'i da ansa sallamar a kuma lokaci d'aya, d'age labulen parlon akayi,inda wata zuk'ek'iyar mata ta shigo fara tas da ita kamar ka tab'ata jini ya fito a jikinta, kallon farko idan mutum yayi mata zai tabbatar da t'sant'sar wayewa da kuma gogewa had'i da madarar ilmi tattare da ita.

Wani dank'areren les d'an ubansu da ak'alla kud'insa zaikai kimamin dubu tari da hamsi take sanye dashi, an masa d'inki na gani na fad'a d'inkin zamani na riga da zani, warwaro na gwal had'i da d'an kunne da sarka dake mak'ale a wuyanta ma ba k'aramin k'ara fito da t'sant'sar k'uriciyarta yayi ba, kyakkyace kam babu laifi bugu da k'ari hasken farar fatarta ya sake bayyanar da ita sosai,kunsan ance farar mace alkyabbar mata...!

A shekaru na haihuwa zatakai a k'alla 29yrs, *DR SALAME* kenan, wanda mai karatu idan bai manta ba na ambaci sunanta a shafi na hud'u, likita ce mai zaman kanta a wani katafaren asibitin had'in gwiwa da suka yi sa su biyar tare da wasu k'awayenta dasuma likitocinne,
sunan asibitinnasu *FIVE STARS✨ SPECIALIST HOSPITAL* .

Y'ar asalin garin taraba ce cikin garin jalingo, iyayenta kuma rufin asirin Allah ne yake rik'e dasu a lokacin baya,inda Allah yasa wahalarsu ba mai nauyi bace suka sami wani gawurtacce d'an siyasa a cikin garinnasu da dik shekara yake d'aukar emmata guda biyar had'i da samari guda biyar ya biya masu kud'in shiga jami'a har su kammala yana d'aukar nauyinsu.

Salame ma na d'aya daga cikin way'anda suke da k'ok'ari sosai,kuma sai akaci sa'a su biyar d'innan da aka deb'a k'awayene na k'ud da k'ud tin suna k'anana, dan haka suka maida hankulansu sosai akan karatunnasu da suke fatan ya zame masu wani katanga da zasu cika burikansu na rayuwar da zasu hau motoci,su saka gwala-gwalai da kumaa dank'ara dank'aran leshika.
Infact dai kawai su zama manyan mata abin kwatance cikin al'umma, kuma Alhamdulillah da suka maida hankulansu suna da shekaru 23 suka fito da kyakkyawan sakamako a k'ananun wannan shekarunnasu kuma suka samu aiki a hannun a cikin babban asibitin Kaduna tare da albashi mai sok'a, sosai sukayi farin ciki da hakan kuma,inda wannan alhajin daya d'auki nauyin karatun nasu ya nuna sha'awar yana buk'atar auren Salame, t'sunt'su daga sama gashashshe kuwa da gudu ma ta amince.
Inda akayi aurensu ya ajiyeta a cikin garin Kaduna, watansu goma da aure ta haifo kyakkyawar d'iyarta mai shegen kama da ita babu abinda ta bari na uwarta a fannin kamanni dakuma kyawun aka rad'a mata suna *Mufyda*, da wannan albashinnasu ita da k'awayenta wato su biyar kenan suka had'a hannun suka gina dank'areren asibitinsu wato 5stars cikin shekara biyu da fara aikinsu...!

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now