page 12.

205 11 0
                                    

Dr. Laylah.

12.

Baiko ganin gabansa ya fice, a tsakanin sashin iyayen nasa ya tsaya yana bin ko wani part da kallo yarasa wanne zai shiga domin ba zai koma part din Baba Alhaji ba dan ya san b'acin randa Hajiya ta dasa masa ba komi ba ne akan wanda ya karanto  Baban zai shuka masa.

"Kai Muhammad."

Ya tsinkayi muryan Dady ya doki kunninsa. Kallon volcany ya yi ya hangosa tsaye hannayensa goye a bayansa, kallon a gogon hannunsa ya yi yanzu kusan k'arfe goma na dare.

'Tabbas Dady ni yafito nema.'

"Shigo ka sameni."

Maganarsa ya katse masa zancen zucci. Ba musu ya nufi k'ofar da zai sada shi da gidan Dady zuciyarsa na harbawa amma dik da haka yana jin kwarin guiwa.

Sallama ya yi a falo Momy ta amsa masa tana k'are masa kallo ya zube gabanta kafin ya furta kalma ta mik'e da sauri ta haye sama, zamewa ya yi ya zauna a saman rug wasu hawaye masu zafi suka biyo cheek nasa domin wannan alama ne na baida nasara ta ko ina domin dik wanda ke ganin zasu fahimce shi sun juya masa baya.

"Allah na tuba." Ya ambata cikin raunanniyar murya.

"Muhammad zuwa yanzu na amince ba ka san inda Laylah ta ke ba amma ina umurtanka da ka nemomin ita ba dan wani manufa sai dan kai din jininta ne, Yaya ka ke gareta, a kan wannan matsayi na ke son ka nemo inda ta ke ka dawomin da ita gida, idan kayi min haka k'ullin da ke tsakanin mu na kwance shi daga ranar zamu dawo fiye da can baya."

"Zan nemo ta Dady a dik inda ta b'oye daga nan kuwa har wajen Nigeria fatana ka fahimci dalilin faruwar lamarin."

"Nayima alk'awarin fahimtarka Muhammad, kuma zan saurareka dan jin dalilinka."

"Nagode Dady, yanzu zan dauki hanya, idan gari ya waye ka bawa Baba Alhaji hakuri wallahi bazan iya ganin b'acin rai a fuskansa ba kuma wai ni ne silar samuwan lamarin, itama Hajiya ka bata hak'uri zan cika umurninta insha Allah bazan dawo gidan nan ba sai da Laylah. Kai da Momy ina neman gafararku na tarin laifukan da aikata muku bayan haliccinku gareni, zan gyara ko ma ince na gyara, su Baba K'arami dik a ce su yacemin natuba."

Yana gama fad'ar haka ya mik'e ya fice jiri na dibanda. Da ido Dady ya raka shi yana mai jin tamkar ya dakatar da shi amma ya kasa samun kuzarin yin hakan domin fuskan d'iyarsa kawai ya ke muradin gani.

Ta k'aramin gate ya bi ya fice bai bi ta kam motocin da ke harabar gidan ba haka bai damu da ya kira Saifullah ba balle ya koma ya dauko motarsa burinsa ya bar garin Kano ciki daren nan. Yana jin maganar Baba Ali mai gadi da ke yi masa ya ki kulashi wanda hakan ba halinsa ba ne share na gaba da shi, yana isowa bakin titi ya hau napep ya sauke shi a tasha drop na taxi ya dauka sabida babu fasinja ko daya a cikin motar kuma ba zaiyi iya zaman jira ba. Ba b'ata lokaci driver ya ja shi suka dauki  hanyar Zaria sai dai Abuja suka nufa wanda a k'iyasi nan da zuwa k'arfe ukun dare zasu shiga garin Abuja.

Sun isa lafiya sai dai suna isa bakin  gate din gidan Mama Mariya securities da su je wajen gate din suka sanar masa dazun da safe mutanen gidan suka wuce Kano, umurtan drivern ya yi ya kaishi hotel su kwana washe gari su juya. Washe gari da kyar Mahi ya iya shan ruwan tea shima dan jin yana shirin mutuwa ne, kafin su wuce sai da ya koma gidan Mama Mariya cikin sa'a saiga Asiya ta fito, ganinta ya tabbatar masa jiya raina masa wayau securities din sukayi.

"Mahi kai ne da safiyar nan?"

Lashe busassun lips nasa ya yi ya amsa "Ni ne aiki ya kawo ni, daren jiya na zo gidanku amma securities suka tabbatar da kuna Kano, babu kowa a gidan."

"Mamace ta tafi amma mu muna nan kuma ina jin sunyi hakan dan tsaro sabida kwanaki irin hakan yafaru cikin dare abokin Yaya Abdul ya zo neman shi a she had'a baki ya yi da yan fashi suka shigo Allah ya taimaka kafin suyi ta'asa cikin security d'aya ya gano su kafin a ankara suka gudu shi ne Abba ya ce ko waye ya zo da dare ka da abarshi ya shigo, ci kuwa har danginsa da mu yayansa sai gari ya waye sun tabbatar da gaskiya sannan subari."

Doctor Laylah.Where stories live. Discover now