MAHAUKACI

1.5K 27 16
                                    

[9/25, 10:20 PM] MAMAN NOORUL HUDAH: 👄👄👄👄👄👄
*Mahaukaci*
💋💋💋💋💋💋
By maman noorul hudah

Wanan labari kagagen labari ne banyi shi Dan cin zarafin kowa ba

Ban Yarda wani ko wata ta juya min labari ba ta ko wace tsiga
Please a Fara daga farko bana son sai nayi nisa mu takura juna,duk group din da ba a comment zan daina posting

Gabad'aya wanan littafin sadaukarwa ce ga ya'ta *Rahmat* (Nazeera)Allah ya albarkaci rayuwarki ya rayaki ya kare ki daga sharrin makiya (Amin)

🅿1⃣-2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim..

Yau ma Kamar kullum  Suna fitowa ya taso da sauri yayi ta binsu,ummi sai matsifa takeyi tace" nazeera ke Kika Saba me toh gashidai sai binmu yake nidai wanan abin ya fara isata a ce mahaukaci yayi ta bibiyar mu,gaskiya ni na kusan daina tafiya dake wallahi"sai fad'a take kamar me magana da kanwarta bazaka tab'a tunanin yayarta bace nazeera

Itadai wacce aka Kira da Nazeera batayi magana ba saima juyawa da tayi ta kalleshi

Kallonshi nayi da kyau sai na gan wando shadda ne jikinshi milk colour ya Sha datti sai wani Jan t-shirt da wuyar ya yage,miyau ne ke siyaya a bakin shi infact he is the real definition of an inbecile,kallonta yake Yana murmushi bakinshi a gefe

Nazeera ta sakarme murmushi tace"ka koma gida sauri Nike zanje makaranta na makara"

Make kafada yayi alamun ah'ah,kafin Nazeera tayi magana ummi tace"nidai na tafi sai ki tsaya kiyi ta shashanci da wanan mahaukacin dama Abba zai bi shawarata ne da ya had'aki aure Dashi tunda kin rasa mashishini,Haka za a Kare ba saurayin kwarai sai kame-kame"

Dukda maganarta ya d'an sosawa Nazeera rai be hanata murmushi ba cikin sanyi irin nata tace"please ummi ki tafi ba sai kin jirani ba"

A fusace ummi daje sanye cikin uniform din government day  tace"ai dama ko Baki ce ba tafiyata zanyi in badan abba da ya nace muyi ta tafiya tare ba ni me zai kaini tafiya da Mai bakin jini irinki salon a shafa min bakin jini"

Nazeera ta kalleta kawai sai tayi murmushi ta Mika mata d'ari biyun da Abba ya Basu tace"gashi je malam idi yayi Mana canji ki kawo min d'ari"

Fisgewa ummi tayi ta ja saki ta tafi sai gata ta dawo ta wurgawa Nazeera hamsin ta ja saki ta wuce nazeera ta bita da kallo

Mayar da kallonta tayi kanshi tace"boy kayi hakuri in naje na dawo zamuyi hira sosai,wallahi Ina da test"

Juya mata baya yayi alamun fushi ta dawo gabanshi tace"boy please da wuri Zan dawo inshaallah dama akwai Wanda Mukayi dashi zai zo zance in na dawo Zan baka labari"tana Gama magana ta juya zata wuce sai ta gan Yana binta

Juyawa tayi ta kalleshi  tace"boy yanzu baka jin magana nace in na dawo  zamuyi magana"

Da k'yar ya bude bakin shi dake zubar miyau abin kyama yace"yun-yun-yunwa Ni----nike ji"

Hamsin hanunta ta bashi tace"gashi je wajen malam idi ka siya biscuit in na dawo yau zan dafa maka taliya"

Dariya yayi cikin irin maganar su ta inbecile yana Susa Suman kanshi ga fuskar nan baki "yak" so iritating yace"toh sai kin dawo"

Da sauri ta Karasa bakin hanya ta shige keke napep Yana ganin shigan ta ya kalli naira hamsin Yana Susa kai kawai sai yayi murmushi ya karasa shagon malam idi Yana fidda yawun kazanta

Tana kaiwa school ta tarar har an shige an Fara test ga lecturer ya kulle kofa,wani fad'iwar gaba ta ji domin dama ita da lecturer sai a hankali niman dalili yake yayi failing dinta,cikin karfin hali ta tura kofar ta shiga gabanta na fadiwa

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 01, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAHAUKACIWhere stories live. Discover now