shafi na ashirin da d'aya

141 7 0
                                    

*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

*OUM MUMTAZ*

             *21*

********Washe gari da safe bayan Nuraaz ya gama shirinsa na tafiya wurin aiki ya fice daga gidan ba tare da yabi ta kan Janan ba,wanda itama a dai-dai wannan lokacin ta farka daga baccinta,wanka ta fara yi kamin tayi shirinta cikin wani plan riga da zani na atamfa ta yane kanta da k'aramin mayafinta kamar ba matar aure ba,a parlo taga tea plast wanda haka yasata had'a shayin tasha a gaggauce ta d'auko key,lapcod da dai sauran kwamut'santa ta fice abinta!

Daga ta gefen motarta ta hango Mufy da Hanan t'saye cikin uniform nasu alamun zasu tafi makaranta, wani malolon takaici ya t'saya mata a wuya idan ta tuno da cewa wai Mufyda kishiyarta ce, wacce a da ace auren sha hudu akayi mata ta haifi mai kama da ita,kuma wani k'arin takaicinma ta auri wanda ta girme masa da kusan good 7yrs,itakam dai ba tayi sa'an aure ba take gani kamar hakan ci bayane a gareta.

Hanan da itama ta hango yayarta sabida tayi missing nata kwana biyu amma babu halin zuwar mata sabida su Abbi ta sake mata murmushi daga inda take,harara mai kyau Janan ta wat'sa masu baki d'ayansu sabida haushinsu daya cika mata zuciya ta shige motarta ta fara danna horn tin daga nan wurin da wani mugun k'arfi har hakan yakusa rikita mai gadinma.

A wani mugun fusace ta fice daga cikin gidan nasu kamar zata bangaje mai gadin zuciyarta na tafarfasa kamar hayak'i na takaicin wannan abu da aka mata (kaman ba ita ta jawo ma kanta ba).

Abba da Mammi ne suka fito daga part nasu bayan fitar Janan d'in, sabida yadda sukaji horn d'in bana lafiya bane,anan su Ameen ma suka fito cikin nasu shirin drivern su ya wuce dasu school.

Abba da Mammi kuma suka koma ciki suna sake maida magana akan Janan din,amma zuciyar Mammi cike take taf da t'soro sabida yadda taji k'aran motar janan d'in,ta kuma san halinta komai zai iya faruwa da ita cikin wannan motar.

Wajen k'arfe hud'u na yamma yau Nuraaz ya dawo sab'anin k'arfe biyar d'in da suke dawowa,wanka yayi bayan ya gama kint'sawa ya zauna a parlo yana binsa da kallo sabida yadda ya had'a uban datti tinda Janan ba share gidan take yi ba,sannan kuma wanda yake gyara masa tin asali Abba ya sallamesa yace sai dai shi ya nemo da kansa yanzu ko kuma matarsa ta gyara.
Atunaninsa janan tana bedroom sbd ko k'yalllinta bai gano ba a asibitin.
Bacci ne ya fara fusgarsa sama sama,yaji ana knocking,da mamaki ya mik'e domin bud'e k'ofar na ganin ko wanene.

Mufy ya gani sanye da wani doguwar rigarta daya matik'ar fiddo mata da shape nata kanta lullub'e da kallabinta,hannunta kuma rik'e da wani babban tray dake d'auke da kuloli kala-kala tana zuzzumb'ura baki,ga dikkan alamu dai ba'ason ranta tazo part d'in Nuraaz d'in ba,tilasta ta Mommy tayi.

kallonta yayi daga sama har k'asa a t'sanake, bata hanya yayi ta shigo da abincin zuwa kan dining area bayan ajiye ta juyo da niyyar ficewa taga mutum yayi mata k'ik'am akai yana binta da wani mayataccen kallo,take gabanta ya yanke ya fad'i sabida ita bata saba ganin hakan ba,ta chanza hanya jikinta na rawa zata fice yasa hannun ya kamo hannuwanta a hankalli ya fara murzawa yana kallon t'sakiyar idanunta shima idonsa sosai ya kad'a yayi jazur itakuma tafara k'ok'arin kwacewa tana sakar masa kuka sbd t'soratar da tayi.
Cike da muguwar jarabar sa dake cinsa ya janyota jikinsa ya rungumeta t'sam daya sa takasa zille masa daga rik'on da yayi mata.
Iskar bakinsa ya fara hura mata a kunnuwanta daya sa jikinta fara d'aukan rawa sabida bak'on yanayin dake ziyartarta.
wani abinda ya fara mata ne yasa ta sake fashewa da kuka tana turesa daga jikinta amma ko gexau Nuraaz bayyi ba, saima d'aukarta da yayi cid'ok zuwa cikin bedroom nasa....

*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@ Oum-Mumtaz123🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️*

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now