shafi na ashirin da hud'u

149 7 0
                                    

*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

             *24*

******** Isowar su Mammi ma sun tarar janan d'in a aminity aka kaita d'aki mai cin mutum d'aya, sai faman bacci take tayi saboda alluran da akayi ta suburbud'a mata,had'i da drip,sosai hankalin su Mommy ya tashi na ganin yadda jikin Janan d'in yake fata-fata!
likitocin dake kan janan d'in kuwa sai basu baki suke ta famanyi na ganin yadda suke ta faman kuka,ga nan janan kuwa rai a hannun Allah,idan kuka ga yadda jikinta hatta ga fuskarta yakoma sai kun tausaya mata,wanda hakan ma wai da sauk'i saboda basu tarda ita a lokacin da aka kawota ba,yanxu an nannad'eta cikin bandeji an wanwanke ciwukan nata,
Abbi ma an shiga da shi emergency saboda a basu taimakon gaggawa domin kuwa  shima a sume aka iso dashi

Isowar su Abba ma har an shiga da Nuraaz accident and emergency! Banda zurga-zurga babu abinda Abba yake yi wannan mutumin nata faman bashi baki,d'aya daga cikin likitocin asibitin ne yakai Abba inda aka kwantar da Janan kaman yanda shi ya buk'aci hakan!

Ko da ya shiga,ya tadda Mammi da Mommy zaune sunyi jugum-jugum kowa da kalar tunanin da yake yi cikin zuciyarsa, ga Janan ma kwance sai sauk'e numfashi take tana bacci da kana gani zakasan cewa baccin bana dad'i bane!

*✅ote*
*comment*
*share*

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now