FARRA'U

5 2 0
                                    

*FARRAƘU...!*

_MALLAKAR:HAUWA S ZARIA_
                         *(Mman Uswan)*

*Arewa writer's association📚✍️*

_*Wanan page Sadaukarwa ne ga mummber's na arewa writer's*_

~*FREE PAGE  1*~

     """Dukan kofar boysquaters da akayi ne ya zaburar da ita, duƙe take malale aƙasa ga yaranta guda biyu *MUHAMMAD* wanda sukai wa alkunya da *FAISAL* ita kuma *AISHA*   alkunya ne sukai mata da *FARHANA*,sun zagayeta kowanne na mata kukan yunwa"
Tun tana lallashinsu har ta haƙura saboda itama bata da wani ƙarfin jiki,saboda yunwa in bazata manta ba rabonta da abinci tun Shekaranjiya"
"Su Farhana Tun jiya da dare gashi yanzu har gari ya waye rana ta dago ammah babu wani labari muguwar bata  ga dama ta basu ba".

"kallo daya tayi musu tana kwancen takoma ta kwanta tana maida Numfashi"Su Farhana suna ganinta suka ƙara rakubewa jikin Mamansu suna Fidda Numfashi jikinsu na rawa sabida tsoro da razana"

  *KHADIJA...*  Ta gyara tsayuwa wacce ke Sanye cikin wata doguwar rigar shadda gezner,mai ruwan ƙasa wacce taji aiki,ga zinare suna kyalli kunni da hannayenta,ta yafo wani ƙaramin vail,hannunta wata karamar jakace tana kallonsu a yatsice tana taunan cimgam yana bada sautin kas..ƙas!kamar wata karuwa,kallo ɗaya zakamata ka fahimci mummuna ce ta ƙarshe domin a kallon farkon zaka ci karo da wani katon hanci daya kusa cika rabin fuskarta,bayan wani lafcecen baki,da ya kusa yagemata fuska sabida daɗi da to"
"Ga idanunta chan ciki kamar an sakawa fura hannu,a kallo da zaka mata zaka fahimci duniya tare da bariki sun zauna da gindinsu wajenta sabida yanda ta chanza launin fatanta daga baƙi zuwa fari"
"Ga hujin hanci,ga hakoran makka,har guda biyu sabida hauka,bakinta yanadi wani pick din jan baki,kamar wata karuwa gata gajera ga ƙiba,sai tayi wani shirim da ita"

"Banji mamaki ba sai da na kalli wanda ke tare da ita lokacin take cemai.."Honey don Allah ka yankemana wannan wahalar,wai zaman uban me wannan matar take ita da mayun ya"yanta..?Tafada tana saka kanta a kafadansa bayan ta sanya hannu ta shafo kwantattacen sajensa"
"murmushi yai yana kallonta kai tsaye yace"Zaman wa ko takeyi? zaman kanta take babe na,Umarninki kawai nake jira,in yau kika gaji da ganinsu to yau din zata bar min gida basai gobe ba.."Yafada yana manna mata kiss agoshi yana sakin mata wani kayataccen mirmishi.

Kata'i...Nafada ina binsa da kallon Kurrillah,Fari ne dogon Namiji mai cikar zati da kamala,very young domin wannan a shekaru bazai gaza 33 a duniya ba dara daran idanuwansa masu dauke da kwayan idanu Farare,su suka dau hankalina akansa,karamin bakinsa ya dace da wani Siririn bakin saje dake Fuskarsa doguwar Fuska gareshi mai dauke da dogon hanci kamar biro,yana da yalwar gashin ido daga kallon Farko zaka gane yana da Natsuwa da hankali ga kuma kwarjini da wani salo na cikakkun maza masu Duniya,shima irin Shaddar jikinta itace ajikinsa,alamu anko ne sukayi,hannusa sanye da wani shegen agogon Silva mai kyau da yarari,kansa kuma yasha zanna bukar yana wani Fitar da Annurin kamshi kamar wani ango sabon Aure.

Jin a binda yace ne yasa *FATIMA ZAHRA* dake kwance ta dago da daradaran idanuwanta tana kallon *NASEER* ,sarare nayi ina binta da kallon mamaki ganin yanda take kama da Naseer kamar har ta baci,sai dai ita ba Fara bace black beauty ce,ammh hatta idanuwansu da fuskarsu iri ɗayane,sai da ita ta fishi Fadin Fuska kallo daya zakamata ka fahimci yanda wahala tayimata zaman dirshan a rayuwarta sabida ganin yanda kayan jikinta suke,duk sun yake,ga bakinta ya bushe,ga 'ya'yanta dake rabe da ita,kamar 'ya'yan almajirai,macen dai tana ta wani abu kamar mara hankali,kanta ƙaramin yana wani rawa kamar dai yarinyar ba lafiyanta kalau ba"

"Bata samu zarafin mgana ba khadija ta tsaida ita da hannu tana fadin"Ke rufewa mutane baki,yanzu zaki fara kukanki na munafunci kina kiran *YAYA NASEER* yanyan..Na gulma to yau dai ta kare,sai kin bar min gidana da mijina.."Tafada kafin ta kalli Naseer tana fadin"Plz honey saketa yanzu don Allah..'"Kallonta yayi kafin yace"Hakan yayi miki.."Kai tsaye tace"Yes yayi..."Tafada tana ƙureshi da ido ,kamar wata mayya"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 16, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

FARRA'UWhere stories live. Discover now