Sifting

1.5K 134 9
                                    

𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

     ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...

Bismillah Rahmani Raheem.

https://my.w.tt/EcTsIaOy2ab

_Allah subhanahu wata'ala ya halicci d'an adam domin ya bauta mishi, kuma bawai zaka kare shi da kome bane! Sabida babu abinda zaka yi dan ka biya shi wannan kyautar da yayi mana! Koda miskala zarratin bazamu tab'a karen shi da kome ba! Haka zalika ba zamu rage shi da kome ba!  An karbo hadisi daga d'an Abbas, yace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya fada mana cewa! Da zamu hadu mutanen farkon mu da mutane karshen mu, mu roki Allah. Dukkan mu zai amsa bukatar mu! Ba tare da ya manta daya min mu ba! Ashe kuwa dole bawa ya kasance mai godewa Allah da ni'imar da yayi mishi! A duk cikin halittun da Allah yayi. Babu wanda Allah ya karrama shi kamar D'an Adam, a cikin Alqur'ani mai tsarki Ubangiji yayi batu da yawa akan Dan Adam!  Ya kuma bashi labarin kanshi a cikin Alqur'ani! Ubangiji yana sane yayi mu masu banbancin Halitta. Wasu farare! Wasu bakakke! Wasu kuma zabiyoyyi! Kuma yana sane da banbanta mana ra'ayin mu akan addini! Sannan ya kaddara wasu fararrun alamari zasu iya shigowa tsakanin mu!  Dan haka da wannan nake kuma godewa Allah da ya bamu ni'imar da bamu isa mu saya ba sai dai mu gode mishi!_ Alhamdulillah!

1989/ July/ 21
Jigawa state

Hadeja General hospital.
   
  0️⃣1️⃣

"Dan Ubanki idan kika kuma shigowa rayuwar Ma'aruf sai na saka an yanka min ke. Anyi min  Gunduwa Gunduwa da namarki, bake mayya ba sai na cofin Babanki yar shegiya, tsinaniya. Kai idan na kuma see you a najeriya, a go cofin kan uwarki bake magret ba toh ko markade kike babu sassauci a tsakanina da ke, yan banza me manyan idanu, maza take yor culot maki sakawa ki bar garin nan dan uwarki kar na kuma ganin yor lege, a garin nan yar banza me manyan idanu." Cikin shashekar kuka matar da bazata wuce shekaru ashirin da hudu ba, ta durkusa a gaban wata mata wacce idanunta Babu alamun rahama tace cikin bagwaren hausan da bai gama rike bakin ta ba,
"Riƙo yaro sai Maman shi don Allah ku bani baby na, i swear ba zan kuma came back to Ma'aruf ba, please baba"

Tauuu suka dauke ta da mari sai da ta dungura, dai dai shigowar Nurse dakin da aka kai Magret, cikin jin haushi Nurse din tace.
"Amma baku da imani, taya mace daga haihuwar ta ko hutawa bata yi ba, zaku zo ku sakata a gaba! Kuna cin mutuncin ta, haba ku kuwa!" Kallon jelar gashin Magret a hannun Surayyah tayi. Cikin mamaki take kallon tsantsar rashin mutunci a idanun su. Takowa ta yi tare da d'ago matar cikin tausayawa ta ce.
"Mutanen na basu da imani, kuma zasu iya cutar dake, idan kika tsaya sai sun baki yaronki. Kiyi hakuri kinji." Kallon kayan jikin jikin Hauwa. Riko hannunta tayi suka saka kai zata fita, ta kwace hannunta, tana kuka tare da fadin.
"Karku rabani da Yarona, ku bani Yarona." Haka Nurse Salamatu taja ta suka fita. Kuka take kowa ya ganta sai ya tausaya mata, har suka bar ward din, sannan ta kaita wani daki ta bata kaya ta saka, riga daban zani daban. Sai dan kwali, da ta daura. Hawaye na zuba mata. Ta ce mata.
"Please ga Yarona a hannun Allah yana kuma hannunki, ki saka ido akan shi, ki kuma bani layin asibitin nan zan tafi idan na isa, US zan kira ki. Don Allah karki cire idanunki akan shi yaro karami sun hanani shi." Haka ta riko hannun ta suka fita sai da ta samu wani a koru kura, ta sakata wanda zai kaita Kano.

      ***
Bayan tafiyarta Suka dauki yaron suna kara jin haushin Hauwa wacce yar asalin ƙasar Amurika ce, tafiyar Ma'aruf can karatu ya hadu da ita, inda suka yi aure sannan ya dawo da ita, Magret William yar wani shahararren attajiri ne  a garin newyork, ita kadai  ya haifa, uwarta ta mutu ta barta, shi ne ya dauki son duniya ya daura mata, ya nuna mata wata irin SOYAYYA kamar me, sai dai zuwan Ma'aruf Adamu Hadeja, ya sata juyawa Soyayyar Mahaifinta baya tace tana son Ma'aruf, duk yadda Uban yaso karta fada mugun rayuwa, haka taki fir. Sannan aka yi aure tsakaninta da Ma'aruf, sai da suka shekara biyu. Sannan Ma'aruf ya gama karatu, yace zasu zo ganin gidan zai dawo da ita. Tunda suka biyo jirgi suka dire a kano, taga yadda kasar Najeriya yake, take tsoron barinta ƙasar Iyayenta ya kamata, tunda suka shigo hadeja. Ta haɗu da Muguwar uwar miji, da yan uwan miji, tare da Yayar mijinta, da farko sun dawo da arziki me mugun yawa, wanda Baban Magret ya basu, kafin su koma, amma suna zuwa Yaya Hindatu ta kwashe kome hatta kayan sakawar Hauwa sai da suka kwace. Suka wurga mata wasu matattun kaya, haka ta yi ta rayuwa, watan su biyar aka daura mishi Aure da Surayyah. Yar mijin Yaya Hindatu, tunda ta shigo gidan suke. Mata cin mutuncin, tare da wulakantata. Sun dake ta, sun zage ta. Gashi Ma'aruf yana dawowa zasu fadi karya da gaskiya babu bincike zai hauta da duka, wahala tayi wahala. Tun bata jin Hausa har ta koya dan dole. Abin takaici da ban tausayi, tana samun ciki zasu zubda mata shi, shi yasa wannan cikin tana samun shi ta boye musu baya gayawa kowa ba, har ta fara zuwa asibiti a sace. Zuwa lokacin da ta haihu. Sun kwace yaron ne, wai dan karta tafi dashi dan burin su. Tayi nesa da Ma'aruf karta zauna dashi domin ko sun hada su, sukan shirya. Kuma sun san idan ta tafi da yaron Ma'aruf zai bita, idan kuma suka sake ya bita, sunce zata rike musu shi. Da wannan nazarin Yaya Hindatu ta zuga Baba Mero ta kora keyar Hauwa.
Dan haka lokacin da Ma'aruf ya dawo,  Baba ta fashe da kuka tana kallon shi tace mishi.

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now