𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>
https://my.w.tt/pvpSrJ4R5abℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮Bismillah Rahmani Raheem
_Dedicated to all Black beauty🙍🏿♀️
Daga manyan har kananun idan ke baka ce Wannan shafin naku ne!🤩😍😘_0️⃣3️⃣
Ball yayi da wani jug wanda yake dauke da kunu. Yana huci tare da kallon Hajiya yace mata."Wallahi sai na karya kafarki, munafukar mata, kamar yadda kuka rabani da uwata, Allah sai na rabaki da naki d'an."
Ya juya tare da barin gurin su. Yana jan tsaki, tun da ya shiga shashin sa, me dauke da dakuna biyu da kuma kitchen sai dan tsakar gida, da baranda, tare da kitchen ɗin waje, da kuma wani a cikin falon gidan, sai dan gurin wanki da wanke wanke a waje, sai kuma dan backyard da yake dan bayan gidan inda zaka ayi shanya idan aka yi wanki.
Gidan zaman mace daya ce, babu wani abu da za a kara bayan haka. Gidan yayi kyau sosai, domin na yaran da ake ji dasu ne aka mishi. Tsaki yayi tare da kaiwa bangon, yana kuma jan Allah ya isa tsakanin shi da mutanen da suka raba shi da mahaifiyar shi. Dan haka yayi wanka ya shirya tsaf, sai ɗaukar kamshi Oud 24hrs yake, cikin Izzah y kalli madubi yaga yadda Allah ya zuba halittar shi bai san lokacin da ya sake wani irin murmushi ba, dan yayi imani kaf Jigawa babu hadadden gaye irin shi, most ontop population guy, in Jigawa. Penny loafer shoe kiran kamfanin vinci ya saka,. takalmin da shaddar sunyi match yayinda hular shi zanna bukar ya tafi da zaren aikin rigar shi.
Wani sarka ya saka a hannun shi kamar kaca, bayan ya ya saka agogon shi. Cikin kuzari irin ta jajjurtacce namiji yake tafiya tare da cilla key din motar shi sama, yana cafkewa. Turuss ya tsaya dai dai lokacin da ta bude mishi zig din rigarta.
"Aamil! Sai yaushe zaka dai na guduna? Yanzun duba fa, ina haukar ka, baka ciwo na. Ina matuƙar kaunarka" takowa yayi ba laifi yace a ranshi. Kallonta yayi sama da kasa, yarinyar tana wuta. Kallon boons ɗinta yayi wanda suka ƙasance kamar an hura balloon, sun leko daga kayan jikinta suna mishi wani blush! Fincikota yayi cikin nutsuwa yana kallon fuskarta! Kashe mata ido yayi sannan yace mata.
"Gaskiya bazan auri yar Hindatu ba. Da dai kin nemi muyi Shagali ne zan iya gayyatar ki d'akina, amma aure." Hade bakin su tayi tare da saka hannu a keyar shi,yana kaunar shagali. Rike bayanta yayi. Tare da gyara mata tsayuwa, sannan ya rungume ta suka fara takawa bata san inda yake kai taba, har sai da ya dangana da cikin gidan, Ana gulmar Hajiya Uwani suka hango Aamil rungume da mace.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Amma wannan yaron anyi kwasa she. Yar waye ka samu zaka lalata musu ita, shine dan ka cika dan isk..." Ture Hasnah yayi tare da takowa gaban Hindatu yace mata.
"Idan zan yi Shagali da Yan mata, Yaran manyan nake nima. Wacce Ubanta zai boye abin kunyar da tayi dan kare martabar ba yar da babu wanda yasan inda dangin Ubanta yake! Ke kuma na kuma kama ki!" Shafa wuyar shi yayi alamun babu abinda ba zai faru ba.
Daga haka ya bar musu gidan, karshe gulmar da aka rufe kenan, daga hmm sai hmm yar me gulma tayi ciki.
***
Hadeja
Unguwar Gandun Sarki.Babban gida ne mai dauke da tarihi, kuma me dauke da mutane kusan dari da wani abu, maza da mata yara da manyan, a takaice family house ne nasu Alhaji Ma'aruf, gidan Sassa ne daban-daban, gida ne da yake dauke da matan aure sama da arba'in da uku. Domin kowani shashin ba zaka raba shi da mata uku zuwa huɗu ba.
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
RomanceThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...