Empathy

501 71 10
                                    

𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

     ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
      
        ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮

Bismillah Rahmani Raheem
 
https://chat.whatsapp.com/GIIFqCembtoD3Bp6yWve7C

Don Allah idan kana Groups dina karka shiga wannan na masu bukatar Free Pages ne! Please karku shiga 🙏🏼

#Juyayi
0️⃣7️⃣
         Babu wanda ya kuma bi ta kan Aamil, sabida sun fahimci fitinar shi yake kawai, dan haka babu ruwan kowa da damuwar shi auren babu fashi. Ya buga ya buga aure babu fashi.

.... Dan haka ya shiga daki ya zauna na wuni guda yana nazarin abinda zai aikata. Bayan kwana biyu, Hajiya Uwani da Kawayenta tare da Ya Hindatu suka kai kayan auren Aamil Hadeja, bayan an Baje kayan. Tana can  bakin rijiya, tana jan ruwa, da wani mummunan kayan jikinta, riga da zani ce, zanin an mata sanda, amma bai hana tsakiyar zanin darewa na.

         Gashi kwana biyu tana fama da kasuwa, dan haka idan ruwa ya tab'a jikinta susa take har tana zubda kwallar dad'i, gashi ciwon ya kama duk wani gabb'a na jikinta, sosawa take kawai. Bata san me ake ba, dan haka ta tsayar da Mati ya daura mata bokitin paint.  Ta nufi hanyar shiga shashin su, taga mutane, dan haka ta karasa da sauri, tacewa.
"Altine sauke ni don Allah!"

   Tsaki yarinyar ta mata tare da cewa.
"Toh ki dawamma da ruwan a kanki, banza kawai."ta fadi haka cikin jin haushin Sidrah,
"Toh don Allah ku sauke ni, wuya na!" Ta faɗa tare da fashewa da kuka, mik'ewa Hajiya Uwani tayi ta hango ta kanta yana rawa zata sake bokitin.
"Lantana Sirikar tawa aka bawa wannan katon bokitin, baku san yana maida mace baya ba?  Yarinya karama an daura mata wannan bokitin, ku matsa min na wuce, baku da amfani" haka ya bangaje yaranta yi ta saukewa Sidrah bokitin, a ranta tana cewa.
*Insha Allah ƙarshen wahalar ki tazo!*  Yanzun ta kuma yarda da hadin domin ko babu kome yarinyar zata samu kulawa.
"Hajiya Uwani! Ina in-law din mu take?" Inji Hajiya Ubaidah, murmushi tayi sannan tace musu.
"In-law na me tsada ce, idan kuka ganta prize d'inta ya sauka ku bari sai nan da wani lokaci zaku ganta! Idan kun gama kuyi min magana."

Riko hannunta tayi suka fita, tare da nufar shashin Baba Mamman, tana kallon Yadda matan gidan suke hararar Sidrah, shimfid'a mata taburama aka yi, ta zauna tana murmushi. Tana kallon yarinyar tare da tausaya mata, a ranta. Tabbas idan Sidrah ta samu kulawa, mace ce sosai ta bugawa a jarida.
"Shekarunki nawa?"
Ware idanun tayi tare da d'aga kanta tace mata.
"Ban sani ba"
"Yayanku Aamil ya? Me yace miki?"
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace mata.
"Bai ce min kome ba!"
"Bai miki barazana ba?"
Sunkuyar da kai tayi kasa, sannan tace mata.
"A'a bai ce min kome ba!"
D'ago kan yarinyar tayi, tana yabawa da zurfin cikin ta, tace mata.
"Toh babu damuwa! Kina zuwa boko?" Ta kuma tambayarta.

      "Eh kafin kayan makaranta na su yage, ina zuwa amma yanzun Baba yace min ba zan kuma zuwa ba." Ta fada a sanyayye,
"Toh!"  Kar'ar wayar ta ya katse mata maganar da zata yi, ta dauki wayar a sanyayye ta saka a kunne, "ok!" Mik'ewa tayi sannan ta fito ta samu har sun fito.
"Uwani wai boye mana Sidrah kike?" Inji Ya Hindatu,

"Sidrah!" Ta kira sunanta, a sanyayye yarinyar ta fito tana rab'ewa da bango, har ta iso gabansu, cikin wani irin soyayyar da ita kanta Hajiya Uwani bata kawo Kawayenta zasu yiwa Yarinyar ba, wanda tafi zaton tausayi ne.
    "Zo nan Ƴa guda ba bari ba, sannunki Yar mu!" Nan suka shiga janta a jiki kamar babu wani abu a tare da ita,  nan bakin cikin ya kuma rufe yan gidan, suna jin ina ma da Yar su ce ta samu kanta a cikin surukar Alhaji Ma'aruf, sunyi imani za a fifita ta sama da yadda ake fifita kowa, sai wancan bakar me munin kamar zunubin. Haka suka mata kyaututtuka masu yawa, sannan suka fita daga gidan.
Kamar jira ake subar gidan, kuwa aka kwace kome tare da mata shegen duka. Sannan aka korata sai kallon kayan suke.
"Wallahi idan nice sayar da kayan zanyi, makira ai ta samu"
" Amma baki da hankali, Lamiyo, waye ya aike ki, baki ga sun tafi da wasu abubuwan a cikin yar karamar akwati ba, toh wallahi, kome na su a kirge yake babu ruwa na."inji Lantana, sanan suka kwashe kayan aka kai dakin ta.
     A hanya suke jajjanta yanayin da suka ga Yarinyar, cikin jin haushi haushi Hajiya Sakina tace musu.
"Wallahi yana cikin dalilan da yasa bana son family house, ina dalili yarinya mareniya an maida ita baiwa, wallahi ta bani tausayi sosai, aurenta da Aamil shine mafita a rayuwata."

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now