𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮Bismillah Rahmani Raheem
#Ruwa a jallo.
1️⃣8️⃣Cikin mintinan talatin suka isa inda ake zanga zangar, tare da niman shi tare da yan sanda, a kai kai suna waya da Mom din shi, tare kuma da P.A ɗinta.
Shiru Allison yayi bai fita ba, sabida kar fitar shi ya kuma haifar da rudani, zurfaffa bincike yake sosai, tare da nazarin me yasa Mom ta rud'e?
.... Me yasa ta damuwa, yanzun haka takira waya na biyar kenan, meye matsalarta da son sai an kama me kama dashi? Duk da kuwa bata ƙasar. Akwai abinda take boye mishi na tsawon shekaru masu yawa. Toh meye abin da bata son ya sani.
Toh meye ne wannan abun? Shiru yayi na wani lokaci, kafin ya dauko laptop din shi, yana duba wasu hannayen jarin da kuma adadin kudin su da yake banki, bai fahimci kome ba. Haka ya ture laptop din, sannan ya kuma kiran P.A ya shigo da sauri, tunda yaga yadda Allison ya tsume fuska, tare da daura daya akan daya, ya shiga nutsuwar shi.
"Har yanzun baku same shi bane?"
Ya wurga mishi tambaya, girgiza kai yayi sannan yace mishi,
"Yallabai.""Ku cigaba da niman shi, kuma, wannan ya zama sirri a tsakanin mu, bamu son mutanen gari su san da batun, ba iya nan ba."
Kasa yayi da muryan shi, ya cigaba da Magana.
......
Aamil kuwa, ba kome ya sanya shi barin gurin ba, sai hango wasu fusatattun kartin maza, suna d'aga mishi rigar su, ya hango bindiga, murmushi yayi sannan ya juya tare da barin gurin.
Aikuwa suka rufa mishi, mutum kamar iblis, jan su wani lungu yayi. Suna shiga suka hango shi yana cin pizza, cikin kwanciyar hankali, gefen shi kuwa karfe ne da ya b'alla na (tap) wato panpo.A hankali suke takowa inda yake, kallon su yayi sannan yace musu.
"Kunga nasan a fusace kuke! Kuma nasan ba zaku kyale ni ba,mai zai hana ku barni na ci abinci na koshi, sai na mika muku kaina salin alim."Cikin hargagi suka yo kanshi, ajiye kwalin pizza yayi tare da rike karfen hannun shi, dayan na zuwa kafin ya kamo shi ya buga mishi karfen a kafad'arshi, sai da hannun shi ya kwab'e.
"Cewa nayi ku jira ni na gama cin abincin ko? Idan kuka hana ni, cin abincin Uwar me zaku nan bani? Jakuna kawai."Ya kuma ɗaukar kwalin ya cigaba da ci, ga mutumin akwance kasa, bindiga daya daga cikin su ya dauko,.kafin yaja kunamar shima, ya jefa mishi kwalin pizzar, tare da ɗaukar karfen ya shiga rufe su da duka.
. "Zaku gaya min meye nayi muku? Waye yake son kashe ni? Zaku gaya min ko sai naci ubanku." Sosai yake dukar su kamar Allah ya aiko shi, da gudu suka bazama, ya kuwa bi bayansu, jifar su yayi da karfen sai kan Glass din motar Allison.
Sai da tayi tsawa, ta rugugguge, tsoron yasa Allison ya kare fuskar shi da kan shi, yayin da yaji babu wani abu ya d'ago kan shi, ido biyu suka yi da juna.
Kowanne sun ya firgita, cikin wani irin yanayi suke kallon juna, kuma a lokaci guda suke shafa fuskar su. Bude motar Allison yayi zai fita gurin Aamil. Shima kuma burin shi ya isa gare shi, sabida bai tab'a jin ko a tarihi akwai me kama da shi kwaf daya haka ba, hango guard din Allison ya sanya shi juyawa da gudu ya bar gurin.
"Kubi bayan shi yayi gaban?"
Allison ya faɗa da ƙarfi, aikuwa suka bi bayan shi dan banza me zubin almatsutsai ya gudu, dawowa suka yi aka canzawa Allison mota, rike kan shi yayi tabbas sunyi ido biyu dashi, idan haka ne toh waye shi.
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
RomanceThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...