https://my.w.tt/YlEwi83Nkbb
𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮Bismillah Rahmani Raheem
A wise woman wishes to be no one’s enemy, a wise woman refuses to be anyone’s victim.*Shin har yanzu kuna sayan data,airtime, TV subscription da biyan kudin wuta diga banki???*
Ya kamata ku dena *wadatar da bankuna kuxo ku sayi VTU portal a kudi kalilan (5k) sannan kudinga samun akalla 1k zuwa 20k a rana.
Mai buqatar karin bayani tayi min magana😃🤝🏽 ga masu bukata zasu iya tuntubar Mimiqueens ta wannan Number+2348036319148*
#Waye kai?
1️⃣9️⃣Cikin nutsuwa yake shiryawa, hankalin shi da nutsuwar shi yana ga shawarar da zuciyar shi ta bashi,kuma ya amshi shawarar hannu bibbiyu, domin yayi na'am da ita. Kara wayar shi yayi, cikin sanyi jiki ya ɗauka tare da sakawa a kunne. A hankali yace.
"Mom!"
"Allison! Naji ance an kama wannan mutumin! Shin da gaske ne?"
Ta tambaye shi a kage,
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya lumshe idanunshi kafin yace mata.
"Karya ne! Asalima nine na fita Zanga-zangar ""Allison!!" Ta daka mishi tsawa,
A shagwaɓe yace.
"Mom! Kiyi hakuri ba zan kuma ba."
Yadda yake maganar sai jikinta yayi mugun sanyi, nan ta shiga mishi nasiha, tare da mishi faɗa kamar tana gaban shi, lumshe idanun shi yayi cikin damuwa sannan ya bude baki yace.
"Nagode Mom!"Sannan ya kashe kiran, tare da fesar da iskan bakin shi, yana gyara neck tie din shi, yana gamawa ba, ya shiga saka links din hannun shi. Tare da makala agogon hannun shi. Daukar bluetooth speakers, ta manna a kunnen shi. Gyara gashin shi yayi tare da fesa turare.
A hankali ya saka cap toe Oxford shoe, wacce ta dace da suit din jikin shi, zama yayi a bakin gadon shi yana kallon closet d'inshi, cikin nutsuwa kafin ya mike daga zaunen ya nufi hanyar waje, a sanyayye yake sauka daga step din gidan, yana kuma kallon wayar hannun shi tare da tab'a bluetooth din kunnen shi.
Yana iso falon duk suka zuba mishi ido, kafin ya nufi hanyar waje, suka rufa mishi baya, idanun shi lumshe bayan ya zauna cikin motar yayinda zuciyarshi take tsananin Bugawa.Yau bai duba paint work din shi ba, amma tabbas yana bukatar hakan, lumshashen idanun shi ya kuma ware su akan fuskar Emily da bai san shigowar ta ba.
A ranshi yace..
"Wannan ba dai bakar naci ba,".Kallon ina zaki yayi mata, take ta shiga hankalin ta, tace mishi.
"Zan.."
"Sauka!"
Babu musu ta sauka domin ta san halin shi tunda yace mata sauka, matukar bata dauka ba, zai iya fidda ita da kanshi ba tare da yaji ko dar ba, haka halin shi yaƙe bai cika so ana mishi shishigi ba.Idan kuma zaka iya tafiya dashi babu kai babu gwatselewa, musamman ita yafi gwatsaleta, amma dake bata da zuciya, sam haka bai damunta, idan zai shekara yana ɓata mata rai toh ba zata tab'a nuna mishi ba.
Shi yasa wani lokaci, idan ya koro wulakancin shi, sai ta yi sati Uku bata leko gidan ba, sabida rashin mutuncin da yake mata, amma da kanshi zai je niman ta, idan kuma ya nimota ya shiga shareta, kamar ba shi yazo da kan shi ba.
Idan tayi zuciya zata bar gurin ya janyo ta jikin shi dan dole take zama, tunda shi dai idan yaso zai. Mata hira idan bai so ba kuwa, kirb'a mata wulakancin yake tana fara damun shi zai ce mata.
"Fita can kiyi surutunki, tunda ke hakan ba wani bakon abu bane a gurinki, ni kuma takurani yake."Idanun tane suke cika da kwalla, ta rike hannun shi sannan tace mishi.
"Nasan watan wata rana zaka so na zauna da kai, nayi ta maka."
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
Storie d'amoreThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...