ƊANƊANO...

4.8K 205 29
                                    

Jihar Katsina jiha ce daga cikin jihohin Nijeriya guda talatin da shida (36), tana yankin arewa ta yamma na kasar Nijeriya. Ansamar da ita ne daga cikin jihar Kaduna, Mutanen jihar Katsina mafiya yawansu Hausawa ne, sai kuma Fulani kuma sana'o'insu noma ne da kiwo. suna da halsuna Hausa, Fulani, Turanci. Tana da kananan hukumomin 34 sune :-

Bakori
Batagarawa
Batsari
Baure
Bindawa
Charanchi
Dan-Musa
Dandume
Danja
Daura
Dutsi
Dutsin-Ma
Faskari
Funtua
Ingawa
Jibia
Kafur
Kaita
Kankara da sauransu, GARIN BANDALO (garin bandalo da sunan garin duka na kirkira ne) babban gari ne da ke cikin karamar hukumar Kaita, garin bandalo garin Fulani ne da ke da fadi da yalwan arzikin noma da kiwo. Ya wacin mutanen garin da suke kiwon shanu a yammacin gari da kewaye, wa su kan shiga birni yin fatauci, matan su kuma na shiga birane tallar nono da danyen manshanu, yawacin fulanin da suke garin ba asalin yan garin ba ne, irin fulanin nan ne makiyaya, masu yada zango a duk garin da suka tarar yana da albarka da ruwa. Wani abun da zai burge duk wani bakon garin shine yadda fulanin suka kawata garin da bukkaken fulani, a tsakanin wacan bukkar da wata akwai tazara sosai, domin kowa ya yi gidansa ne a cikin gonarsa, masu wadata da arzikin cikinsu ne suke zagaye gidansu da zana su killace kansu kamar masu babban gida.

MALAM JAURO SAMA'ILA Shine Sarkin Fulanin wannan yankin, sarki mai adalci da kamanta gaskiya a tsakanin Fulanin da yake mulka, sarki ne daya kafa tarihin da babu wani bafullatani a yanki da ya kafa irin tahirinsa, ta hanyar bawa yarsa Faɗime ilmin boko da na muhammadiya, shi ne kai da mutumen da yake daukar yarsa ya shiga da ita birni a duk safiya ta Allah idan zai je fatauci ya aje a makarantar bokon da ke garin Kaita shi kuma ya shiga cikin garin gurin harkokinsa.....

FAƊIME
Ya daya tillo a gurin Malam Jaure, kuma ya daya tillo a gurin Tumba, yar da ta kafa tahirin shiga makarantar boko a garin Bandalo. Yar da kowa ke gudu yar da kowa ke kyama yar da kowa ke fargabar arba da ita, yar da Tumba tai mata alkunya da FULANI.

FULANI POV

Hawaye ne ke fitowa daga lussasun idabuwanta da take sharar bachi da su, fuskarta kuma na kawatuwa da murmushin dalilin mafarkinta.

"Fulani Fulani Fulani"

Firgigit ta bude ido ta tashi zaune tana kallon mahaifiyarta wacce ke tsaye a sanye da riga da zane na Atamfa, kwayar nono a hannunta.

"Dun Allah Dun hanyar hillacin ki tashi ki kai shanun ga yamma su sha ruwa su yi kiwo, hay Fulani rana hwa ta na ga yi kuma kin san ba su ci komi da safe ba"

Wacce aka kira da Fulani ta saka hannunta na dama da na hagu ta share hawayen bachinta.

"Amman Inna yau ba Hajjo ce da zuwa daji ba?"

"To Inna Hajjo ta hana ta ta ce ba zata je ba, hadda ta turata bunni gurin talla dawo da nono tun dazun suka tafi tare da Mairo, dan haka ke sai ki tashi ki tahi kamin Malam ya dawo, kin fi kowa sanin cewar baya son a bar mai nagge da yunwa"

"To Inna zan tai yanzu"

"To tashi yar albarka, idan kin hito sai ki sha sabon kindiro yanzu na taso shi"

Inna Ladi na fadar hakan ta juya ta fice rike da kwayar sabon nonon da ta taso yanzu, nonon da ko manshanu ba a cire masa ba.
Mika Fulani tai tana sauraren busar Sarewar da take yawan jin a cikin bachinta, ba kuma dan ana burar a Sahiriba sai dan sabo da tai da ita a kowa wane bachi, ya'alan na safe ne ko na rana ko dare, indai har ta kwanta sai ta yi mafarkin wannan mutumen da ya bata baya yana ta burar sarewa a saman dotse, busar da ke sakata hawaye da murmushi a lokaci daya kuma a cikin duniyar mafarkinta, sai dai murmushin da hawayen har a zahiri ana ganinsu, yayinda busar sarewar kuma ita kadai take jin abarta a cikin bachinta. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin jakar kayanta ta dauki littafinta da buro ta zauna a gurin ta soma rubutunta kamar yadda ta saba.

FULANIWhere stories live. Discover now