💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
2⃣9⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
*_wannan page tamu ce nida kawayena, sisters na, mu 7 kawayen asali, Allah ya barmu tare , nida ku (Fatima, Nana Aicha, Charifa, choukouriya, Mardia, Marie, Rafia), kun zama wani bangare na jiki na yan uwa na, je vous aime beaucoup mes trésors cheries_*
A gidan inna kuwa bayan an dawo daga damu su gwaggo suke fada mata yadda sukayi da dangin Habib, kuma ta nunawa inna abinda suka basu suma , inna tayi godiya sasai ga gwaggo tana cewa
" gwaggo su ban san kalmar da zanyi anfani da ita ba wajen yi maki ba sai dai ince ubangiji Allah ya biya ki da alkairi, "
Gwaggo tace
"haba suwaiba godiar ta isa hakanan , ai samira diya take a waje na"*TUNA BAYA*
bayan an daura auren samira an ba kawu sadakin ta, da suka dawo gida sai ya bawa samira sadakin ta da hannun ta , ita kuma sai ta ba inna kudi tace ta fita bukatar su, sai kuma kawu ya bada jikka 50 yace ga gudummuwar mu, mu duka dangi dayake jiya sai dare yazo kuma bai samu damar kebewa da inna ba, shiyasa saida aka daura sannan ya bata su, kusan kudin ma duka shine ya bada su saboda kawu sanusi da yawale jikka biyar biyar ce suka bada , da yaga basu bada abun kirki ba sai shi ya bada jikka 40 saboda yanada rufin asiri shi amma da ya ba inna kudin sai yace na su duka.
Sai inna ta fiddo kudin da ta raga cikin abinda gwaggo ta bata sai tace da su
" yanzu abinda za'ayi ku tafi kasuwa ku sayo shinkafa, da masara, da sauran kayan miya, sannan sai a ba ango jikka 100"
Sukayi na'am da shawarar ta sannan suka tafi sukayo mata siyayyar , da suka raga sauran kudi sai suka yiwa Samira sayayen abinda ba'a saye mata ba, wannan kenan.*Cigaban labari*
Rabi diyar gwaggo ce zata komawa gidan samira saboda da suka tafi dazu gidan mancewa tayi bata dauki material in cockatail ( diner party) wanda samira ta dinka mata ba , shiyasa ta dawo gida ta dauka , sai tace da gwaggo
"inna ni zan wuce Allah ya sa in kai kaina gidan ma"
gwaggo tace
"to hanzarta ,ai dayake ba wani nisa ne ba , kuma dazu kinga hanya da kyaw ai , su kayan ankon ba'a sanya su ne ? Na gan ki da wasu kaya kuma ba ankon ba "Rabi tace
"a a inna Samira tace kar in sanya su , in dai d'auka su , wai hada kwalliya za'a mani ma"Gwaggo tace
"to shikenan, kuma ki dauki diyar ki. Ki tafi da ita naga kina shirin bar mani ita"Sai a sannan inna suwaiba tayi magana tana cewa
"haba gwaggon su, diyar da an yaye ta , ki bar ta tafi mana , ba sai ki rike ta ba"gwaggo tace
"to shikenan se kin dawo, Allah ya kiyaye hanya"
Ta amsa da amin sannan tayi gaba.Aiko bata sha wahala ba sai gashi ta kai kanta a gidan , tana zuwa ta tarda yan matan amarya sun dawo daga wajen angaye suna rabon katin shiga wajen cockail , tana zuwa itama suka bata nata katin , ta sanya shi cikin jaka,
A bangaren uwar gida kuma itama Habib ya aiko mata da nata katin shiga , amma tace babu inda zata tafya, juyin duniya yayi tace bata zuwa ,
Karfe 9 na dare tuni mutane sun fara shirin zuwa wajen cocktail, wasu na wanka, wasu na makup, amarya ma tana can ana tsantsara mata kwalliya , bayan an gama yiwa amarya ,tace da ayi ma Rabi itama amma kadan za'ayi mata , simple makup akayi mata , sannan ta sanya material in ta na anko , aka daura mata dan kwali , ta yafa mayafi hada takali masu kyaw, ba za'a taba cewa ba ita ce Rabin gwaggo ba , tayi kyaw sosai , qurciyar ta, ta fito , yaw da mijin ta ya ganta cewa zaiyi an canja mashi mata lol😂 , aiko saida akayi mata hotuna ta wayar Samira sanan mai hoto ma yayi mata shima saboda ta kaiwa mijinta,
YOU ARE READING
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomanceSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...