WATA ƘADDARA

124 9 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
          
   
         *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

*FREE PAGE*

 
  *page: 2*
   
   
              .......Da gudu ya danno waje ɗauke da ita tana kwance saman kaffaɗarsa, lokacin har motocinsu sun fara tafiya da gudu ya daka yana binsu har suka fice daga gidan batare daya samu nasara shiga cikin motar ba, ƙara harbin ƴan sanda ne yasanyasa  duƙewa, ihu yarinyar ta sanya tana kuma ƙanƙamesa, shima ɗin gam ya ƙanƙameta bindigarsa ya zaro dake saƙale aƙugunsa gami da toshewa yarinyar kunne suna musayar harbi da ƴan sanda, yana cigaba da gudu, ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya ce, "shit me SHAHEED yake aikatawa haka yarinyar mutane ɗauke ahannunsa baki ɗaya ya watsa mana komai" cikin ɓacin rai da hausarsa da bata fita kasancewarsa iyamuri ne Ogan su ya ce, "rabu da ɗan iska mana Allah yasa ƴan sanda su kamasa shege, ko me nufinsa na ɗaukota.! ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya leƙa ta windown mota ciki ɗaga murya cikin fulanci yana cewa, "SHAHEED kayi sauri ƴan sanda sun kusa cin ma.! ya faɗa yana buɗe murfin motar yana miƙa masa hannunsa ɗaya yayinda yake musayar wuta da ƴan sanda dake bin SHAHEED abaya, hannunsa SHAHEED ya kama ya shige bayan  motar yana maida numfashi da sauri-sauri yana kallon baby girl ɗin dake lafe jikinsa tana tsotsar hannu, hankalinta kwance earphone ɗinsa ya cire ya sanya mata kunne ya kunna mata waƙa, ya leƙa ta windown yana musayar harshashi da ƴan sanda har ya samu nasara fasa masu bututun mai da tayar mota, sama-sama motar ƴan sandan tayi  tare da faɗowa ƙasa dam tana ci da wuta ganin haka ƴan fashin suka kwashe da dariya ganin yarda mota ɗaya taci ƙaniyarta, yau kaɗai SHAHEED ya koyi harbi amma har yafi ƙwararin su duk da yarda suka naƙasa mota ɗaya da mutanan ciki hakan bai sanya ƴan sanda sarewa ba cigaba da artabu sukayi  motocin na shararawa aguje kan titi masu mugun tsada jeep-jeep guda uku baƙaƙe, ƴan sanda na cigaba da binsu ciki motocinsu na ƴan sanda jiniya na tashi suna musayar wuta.
              
            
                Titin Batsari motocin sukayi shantal suna tsula gudu waya ogan ƴan fashin ya ɗauka ya kira bugu ɗaya aka ɗauka cikin ɗaga murya ya ce, "ku saki shanaye da tumakai mun kusa isowa" suna sulalowa cikin batsari buzayan dake ɗaure da abu a fuska suka saki tumakai da shanaye sukayi kan titi  suka tare motocin ƴan sanda DPO ABUBAKAR steering motarsa ya duka da ƙarfi ya ce, "shit.!  ƴan sanda ne suka fito suna koran shanayen suna kaucewa daga kan titi, har suka samu hanya suka koma cikin motocin su.
                      Kutsawa cikin garin ƴan sanda sukayi har lokacin basu sare ba yayinda motar ƴan fashin ta masu mugun nisa, ganin sun cin masu suka ƙarawa motarsu gudu wayarsa SHAHEED ya ɗauka ya danna kira ciki hausa yana cewa, "mun taho runhu ku saki dusar masara" ya faɗa yana datse kiran suna isowa runhu yaran hausa dake wajen fuskarsu ɗaure da ɗankwallin atamfa suka saki dusa masara dake wajen ta rufe wajen motocin ƴan fashin ta shige cikin jejin sauke ajiyar zuciya sukayi a tare ganin sun sha, atare suka ɓale murfin mota suka fito fuskarsu ɗauke da murmushin samun nasara  SHAHEED kuwa ɗauke da yarinyar ya fito da bacci ya ɗauketa.
   
   
                       ******
               Wani irin ihu HAJIYA ta saki tana furta "innalillahi wa'innailaihi raju'un shikenan sun tafi da  ILHAM na shiga uku wayyo Allah na..!  yayen ILHAM ma kuka suke tun karfin su yayinda ALHAJI ya haɗa kai da gwiwa ya rasa wama zai taro yana zubar hawaye, domin yasan rayuwar ƴarsa ILHAM ta salwanta  dan yayi imani yan fashi basu da imani komai suna iya aikatawa saboda son zuciya.
             Kukan HAJIYA ZALIHA ne ya ƙara ƙarfi wanda ya maido da ALHAJI KHABIR daga duniyar tunani, miƙewa HAJIYA tayi cikin kiɗima tana cewa, "na shiga uku ABBAN ILHAM shikenan sun tafin mun da ƴa kana kallo, kayi wani abu kana gani sun tafi da ita.! HAJIYA ta faɗa cikin sakin kuka tana jijiga ALHAJI KHABIR tana furta, "innalillahi wa'innailaihi raju'un shikenan sun kashe ni, shikenan sun kashe mun ƴata ƴar shekara uku aduniya, me ta sani arayuwa wayyo Allah ƴata" kamo HAJIYA ABBA yayi dake kuka kamar ranta zai fita shima ALHAJIN addu'a kawai yake cikin zuciyarsa cikin dakiya ya ce, "insha Allah ƴan sanda zasu ƙarbo ILHAM cikin daren nan da yarda Allah, don Allah ZALIHA ki daina kukan nan ko dan lafiyarki dobi yarda sauran yaran ke kuka suma" cikin shasheƙar kuka HAJIYA ta zauna tayi jigum idanunta sunyi jawur tana kuka mara sauti tare da sauke ajiyar zuciyar, tashin hankali gami da tsoro, ABBA kuwa miƙa ma sauran yaran hannunsa yayi suka matso kusa da shi ma'aikatan gidan kuwa lokaci ɗaya suka faɗo parlour cikin jimami suna kuka, dan ILHAM yarinyace mai shiga rai dole zasuyi kewar ILHAM parlour tsit yayi sai sauti ajiyar zuciya dake tashi na kukan mutanan gidan.
   
                
                ******
   
            Cikin tsananin ɓacin rai PETER ya ce, "Wannan wani irin rashin hankali ne ka aikata SHAHEED, me zakayi da ƴar mutane me zakayi da ita daka ɗauko mana ita nan.? PETER ya faɗa yana mai cin kwalla SHAHEED dake ɗauke da ILHAM idanunsa sun firfito dan ɓacin rai kwacewa SHAHEED yayi da ƙarfi cikin hargagi ya ce, "ya kuke so nayi da raina ne.? yarinyar nan ita ta matsa ta biyo ni idan ban ɗauketa ba mun taho ba so kuke asirri na ya tonu saboda ita eehh.? akausashe PETER ya ce, "me yasa baka bari na kasheta ba me yasa.?
      "Saboda babu anfani kashetan kuɗi mukaje ɗauka ba zuwa kisa ba" cikin huci PETER ya daki ƙirjin SHAHEED ya ce, "to bari kaji ɗauko yarinyar nan daidai yake da tonan asirrin ka, domin mahaifinta ba zai taɓa rumtsawa ba sai ya gano inda ƴarsa take bama wannan ba ina zaka kaita ina zaka aje ta eh.? sanin kanka ne kowa cikin mu watsewa zaiyi da zarar ƙura ta lafa kowa zai kama gabansa, toh faɗa mun lokacin ya aza'ayi ka fita da yarinyar da ina da tabbacin kafin lokacin hotonta ya cika gidan tv da kafafan yaɗa zumunta na media kan ɓacewar ɗiyar babba ma'aikacin gwamnati toh ya zakayi lokacin SHAHEED tell me.? PETER ya faɗa yana kuma cin kwalla SHAHEED yana numfarfashi ɓacin rai janye PETER HAKIM yayi SHAHEED kuma ya ja gefe yana gyarawa ILHAM kwaciya dake saman kaffaɗarsa wani yunƙuri PERET yayi yana nuna SHAHEED da bindiga ya ce, "ji nake kamar na kashe ka dan takaici, midin asirrinka ya tonu SHAHHED ka nuna ka sanni sai na kasheka" PETER ya faɗa cikin wata irin kakkausar murya ririƙesa sauran yaransa sukayi yana fifincikewa,wani irin kuka ILHAM ta sakin jin hayaniyar mutane ta fara mata yawa cikin kunne tsaki PETER ya saki yayi tantinsa da sauri yayinda SHAHEED ya shiga shafa gadon bayan ILHAM dake kuka tun ƙarfinta yana lallashenta lokaci ɗaya ta rikita wajen, sauran ƴan fashin kuwa fashewa sukayi kowa cike da takaicin SHAHEED da yarinyar dan mindin asirrin SHAHEED ya tonu nasu ya tonu, dan haka takaici yasanya kowa fashewa aka barsu su uku kacal wajen kuma dama tare suka shigo harkar aranar dan shekarunsu zai zo ɗaya.
            SHAHEED sai HAKIM da RASHID sai ILHAM dake kuka cikin tsananin ɓacin rai SHAHEED ya dangwara da ILHAM dake kuka saman wani tabir cikin tsawa ya ce, "dalla yimun shuru kin biyo ni kuma kina damuna da ihu" ƙuri ta masa tare da sakin kuka tana kallon fuskarsa dake cike da damuwa ya ce, "ai saikiyi, kawai zaki ƙara jefani cikin WATA ƘARRADA..! miƙewa yayi da sauri zai bar wajen kuka ILHAM ta saki tana miƙa masa hannu alamar ya ɗauketa harara ya dalla mata ya miƙa hannu ya ce, "come here.! da sauri tayi jikinsa tayi shuru tare da tura hannunta cikin baki tana jan majina cikin ƙasa-ƙasa da murya SHAHEED ya furta, "munafuka.! ajiyar zuciya HAKIM ya saki shi da RASHID suka ce, "yanzu ya zakayi da wannan yarinyar SHAHEED.? HAKIM ya faɗa cikin jimami shi da RASHID rausaya kai SHAHEED yayi cikin wata irin murya me rauni ya ce, "nima ban san ya zanyi ba sai dai na maku alƙawarin ba zan tona kowa ba in dai hukuma ta kamani da yarinyar nan, ni dai fatana ku cika al'ƙawari da zarar an raba kuɗin ku kai kaso na gida ayima UMMA magani, kuma bana son kowa ya faɗi abinda ya faru kawai kuce mata na mutu akan hanyata na ƙwadago.! SHAHEED ya faɗa cikin raunin murya zai shige cikin tantinsa da sauri su HAKIM suka zagayesa tare da rungumesa cikin zubar hawaye kasancewar su masu saurin karaya suka ce, "insha Allah babu abinda zai samu ɗaya daga cikin mu kowa sai ya cika burinsa"
         "insha Allah.! SHAHEED ya faɗa yana shigewa cikin tantinsa aje ILHAM yayi da idanunta har lokacin biyu sannan ya gyara shimfiɗarsa ahankali ya ce, "zo ki kwanta" miƙewa tayi cikin tafiyar ta ahankali ta ƙaraso gabansa ta tsaya kallonta yake cikin ido ya ce, "kwanta.! jikinsa ta faɗa cikin turo baki ahankali ya ce, "baki jin bacci.? shuru tayi still tana raba ido jingina yayi jikin bango tare da miƙe ƙafafunsa ya kwantar da ILHAM saman jikinsa ya lulluɓa mata jecket ɗinsa daya zare daga jikinsa yana shafa gadon bayanta ahankali.
                 Sannu ahankali ya fara jin saukar numfashinta alamar ta fara bacci leƙa fuskarta yayi idanunta dake lumshe ya tsurawa idanu, hannu yasanya zai zareta daga saman jikinsa ganin alamun tayi nisa da bacci, kamar tana jira da alama kwanciyar ta mata daɗin a saman jikin SHAHEED zareta da yayi daga jikinsa, yasanyata fara ɓare baki tana son fashewa da kuka wannan dalilin yasakasa maidata saman ƙirjinsa ba shiri yana aika mata harara ƙasa-ƙasa ya furta, "jarababa yarinya kawai.! kawar da kansa gefe yayi yana mai shafa sumar kansa da hannunsa ɗaya, ciza leɓɓensa na ƙasa yayi  ya ce, "ya zanyi da wannan yarinyar me yasa tawa ƘADDARA ta zo da haka wannan wace irin ƘADDARA ce.? SHAHEED ya faɗa yana me rumtse idanunsa cikin ƙunar zuciya ya ware idanunsa wayanda sukayi jawur kamar garwashi cikin harshen fulanci ya ce, "Allah ka kawo mun mafita ya Allah nayi nadamar abinda na aikata tun kafin naje ko ina nayi gamo da WATA ƘADDARA...!
   

*Follow me on facebook page n group*:  *salma mas'ud nadabo*

*Follow me on IG*:  *Salmerh 777*

*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*

~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now