🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 5*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
.....Ƴar siririyar hanyar dake cikin gonaki ya ratsa yana tafiya da ɗan sauri yayinda ILHAM ke saman kaffaɗarsa lafe tana shara bacci hankali kwance, haka suka dinga ratsa gonaki SHAHEED na tafiya da sassarfa gudun kar asuba ta masa a hanya dan gidan su can cikin garin yake sosai.
Tafiya sukayimai nisan gaske sannan ya fara hango wani gidan ƙasa, wanda ke zagaye da sandina sai bishiyoyin mangwaraye dake kewaye da gidan, gidan shi kaɗai ne tal a wajen mai ɗan girma, ƙara sauri yayi da sallama ya shigo cikin gidan duk da yasan cewa suna bacci dan lokacin dare ya raba bana wasa ba, hakan bai hanasa yin sallama ba wani gefe ya kalla wanda da alama garken shanu ne, amma yanzu babu ko ɗaya sai ƴar ƙaramar tumkiya dake kwance.
Farfajiyar gidan yayi ƙwal da shi duk da babu wasu abubuwan kirki, ɗaki biyu ne duk girman gidan, dan akwai fili gidan sosai, ahankali ya ƙarasa wani ɗaki ya tura ƙofar ɗakin, wanda babu komai cikinsa sai ƴar yaloluwar tabarma wadda duk ta ciye tasha wahala, sai uwar ƙasa dake ƙasan ɗakin dan babu siminti ko ɗigo cikin ɗakin ko shafe, ILHAM ya kwantar bisa ya aje jakarsa gefe ya miƙe zai ƙarasa ɗaya ɗakin, zumbur ILHAM ta tashi tana raira kuka cike da tsoro ganinta cikin mugun duhun daya mmmaye ɗakin, ɗan siririn tsaki ya saki yana kallonta shi kam ya rasa wannan fitina sam bata barinsa ya ji da kansa, miƙewa tayi da sauri ta dawo wajensa ta riƙe masa ƙafa, duk da irin duhun daya mamaye ɗakin haka bai hanata ganosa ba, saboda yarda ta ƙwalafawa ranta shi, ɗan kawar da kansa yayi ya ce, "menene.? shuru tayi ba tare da ta tankasa ba amma tana rumgume da ƙafarsa hannunta ɗaya cikin baki, zare hannunta dake cikin baki yayi gami da kama hannunta suka fito tare ya ƙarasa ɗaya ƙofar ɗakin, ahankali yake knocking ƙofar ɗakin duk da yana da yaƙinin cewa sunyi bacci amma ya kasa haƙurin sai gobe da safe yaga UMMA da jiki, ƙara knocking ƙofar ɗakin yayi yana cewa, "NABIL UMMA AMMIE..!
Ƴar datijuwar dake zaune dan sam bacci baiga idanunta ba saboda jikin UMMA da yayi mugun tsanani dan baki ɗaya daran suma take tana tashi sam bata san inda kanta yake ba, shima NABIL gyangyaɗi na ɗibarsa yana tashi firgigit yana cigaba da dannawa UMMA tsumma da ruwa, AMMIE na bata ciƙe-ciƙe na hausa wanda rabi na shiga rabi na fita, jin muryar SHAHEED ya sanyata miƙewa tana goge ƴan hawayen idanunta tana fatan Allah yasa SHAHEED ya samo wasu ƴan kuɗin da za'a maida mahaifiyarsa asibiti dan SHAHEED mutum ne mai zafin nema, duk da yana matashi mai ƙarancin shekaru baya raina sana'a duk ƙanƙantarta dan tun bayan rasuwar mahaifinsu shine faɗi tashi a gidan ana samun na kaiwa bakin sallati, harma ya je makaranta secondary dake ƙafur yaje a ƙafa ya dawo a ƙafa, wani lokacin ma can yake tsayawa sai ya nemo yan kuɗi ya dawo gida dan SHAHEED akwai himma ga ƙwazo da ƙoƙari, gama secondary ɗinsa ke da wuya mahaifiyarsa ta faɗa ciwo wanda a yanzu yana shekara goma shatakwas a duniya ƙaninsa nada shekara goma, wanda ya kamala karatunsa na primary tsakaninsa da SHAHEED akwai tazara wanda sai da UMMA ta cire ran haihuwa Allah ya bata NABIL bayan shekara bakwai, tunda Ummansa ta kwanta ciwo babu irin faɗi tashi da bai ba dan ganin cewa ya sama mata kuɗin magani amma abun ya gaggaresa da ciwon UMMA na buƙatar maƙudan kuɗi yabi dangi yabi ƴan uwa amma babu wanda yabi ta kansa, bayan baki ɗaya dokiyar mahaifinsa su suka bi suka lamushe, kawunsa na ƙarshe ma da kora kare ya koresa har yana ce masa ai shi namiji ne ya fita ya nema kota halin ƙaƙa mana amma zai zo masa gida yana zarya safe rana dare, haka ma aminan mahaifinsa duk yabi na birni dana ƙauye amma babu wani labari haka suma dangin, kakarsu ce kaɗai ta wajen uba ke iya bakin ƙoƙarinta itama ɗin tayi iya yinta amma ƙanan mahaifinsa sunfi ƙarfinta, sun gwada mata basu dashi bayan suna dashi ɗin ƙarshe ma gwada mata sukayi nauyinta kawai zasu iya ɗauka, a ƙarshe da takaicin su ya cikata ta dawo gidan su SHAHEED ɗin baki ɗaya da zama tana jinyar UMMA, tofa shine dalilin AMMIE suke samun kwana abinci shima jefi-jefi ba kullum ba, sai ganin dama dan acewar su ba uwarsu suke cidawa ba su SHAHEED ke ci, dangi Ummansa kuwa basa kusa dan fulanin yawo ne ita kanta UMMA bata iya cewa ga inda ahalinta suke, wannan dalilin yasa SHAHEED faɗawa FASHI WATA ƘADDARA ta faɗa masa na tahowa da ILHAM.
Buɗe ƙofar ɗakin AMMIE tayi cike da mamaki dawowar SHAHEED cikin wannan tsohon daren ya kasa haƙurin gobe yayi, koda yake idan zata tuna dama yace aikin ƙwadago zai je na safara shinkafa daga NIGER zuwa NIGERIA, da kallon mamaki ta bisa ganinsa ɗauke da yarinya ƴar kimanin shekara uku a duniya cikin mamaki take kallonsa da alamar tanbaya cike akan fuskarta tare da tarin tanbayoyi cikin harshen fulanci ta ce, "MAGAJI Ha toy a hebi bingel debbo do be saka jemma do.? (MAGAJI ina ka samo wannan yarinyar cikin wannan daren.!) kallonsa ya maida kan ILHAM data shige jikinsa sosai ya ce, cikin fulanci, "idan mun shiga ciki AMMIE na faɗa maki" hanya AMMIE ta basa ya shigo har lokacin hannunsa riƙe dana ILHAM wajen UMMA yayi da sauri dake kwance tana wani irin nishi wadda mutum ke jinjiki muryarsa na rawa ya kama hannun UMMA ya ce, "UMMA..! idanunta da sukayi nauyi jin muryar SHAHEED yasata buɗe idanu tana kallonsa shida ILHAM da itama ta mata ƙur da manyen idanunta tana sauke nishi mai ƙarfi dan ko magana bata iyawa SHAHEED ya ce, "Mi warti UMMA.! (sannu UMMA.!) SHAHEED ya faɗa cikin raunin murya ya cigaba da cewa, "insha Allah zaki samu sauƙi UMMA lokacin warkewar ki yayi da izinin Allah UMMA.! SHAHEED ya faɗa idanunsa cike da hawaye NABIL ne ya matso kusa da shi yana kallon ILHAM data bi ta shigewa SHAHEED hannunta a baki sosai yarinyar ta masa kyau, dama ya jima yana cewa UMMA ta masa ƙanwa jikin SHAHEED ya shige shafa kansa SHAHEED yayi ya ji da zafi cikin harshen fulanci ya ce, "NABIL bandou ma do wouli ko an fou a satay on.? (NABIL jikin ka zafi kai ma baka jin daɗi ne.?) girgiza kai NABIL yayi ya ce, "hamma SHAHEED tun jiya raban mu da abinci sai ruwa muketa sha, shiyasa jikina yayi zafi, yunwa nake ji hamma, na cewa AMMIE mu saida tumkiyata mu sai abinci taƙi yarda" shafa kansa SHAHEED yayi ya ce, "insha Allah daga yau ka gama kukan yunwa NABIL duk wata damuwa ta ƙare daga yau ka ji"
"Da gaske Hamma muma zamu dawo rayuwa kamar su BAFFA JOƊA.?
"Eh mana har ma mufi su, kaɗan ƙara haƙuri gobe sai ka faɗa mun duk abinda kake son ci sai na siya ma ka ci ko" washe baki NABIL yayi yana cewa, "yaya wannan yarinyar fa ƴar ƙarama mai kyau" NABIL ya faɗa yana washe baki yana kai hannu kan na ILHAM kaɓe hannunsa ILHAM tayi tana hararasa harda murguɗa masa baki, sosai abun ya ba SHAHEED dariya wato ita duniya babu wanda ta yarda dashi sai SHAHEED, fito da ita yayi sosai daga jikinsa dan ta shige masa ya ce, "kalli wannan.! kallon NABIL tayi wanda yake fari tas kamar ita sai dai SHAHEED yafisa kyau duk da yana baƙi, dan kyakyawan bakin namiji ne wanda zai iya karawa da farare har na ketare a gasar kyau ya ce, "daga yau shima yayanki ne hamma NABIL ne kina jina" jinjina kai tayi tana kallon NABIL sai kuma ta faɗa jikin SHAHEED abunta tana kallon UMMA dake kwance tana numfashi sama-sama AMMIE na gefen UMMA tana bata magani SHAHEED ya ce, "ni kam AMMIE bana son jiƙe-jiƙen nan suna iya taɓa mata wani abu acikin ciki ta saboda suna da ɗaci" aje ƙwaryar hannuta AMMIE tayi ta ce, "toh MAGAJI ya zamuyi dole tasa ake bata kar ta zama biyu babu" jim tayi ta ce, "har yanzu dai SHAHEED baka faɗa mun ina ka samo yarinyar ba" jim SHAHEED yayi yana tunanin abinda zai faɗawa AMMIE duk da cewa ya tsamaci tanbayar dama, duk da cewa shi ba ma'abocin ƙarya bane amma ya zamar masa dole ya fara yau AMMIE ta ce, "kayi shuru.?
"Dama ahanyar mu ta dawowa mun tsaya cikin garin katsina idan muke aje shinkafa, to fa shine muka tsinci yarinyar nan munyi cigiyar duniyar nan mun rasa ƴan uwanta, har gidan tv da redio mun kaita amma babu labari gashi yarinyar taki amincewa da kowa sai ni, toh shine hukuma ta amince na dawo da ita gidan mu tunda dani da amince idan an samu iyayenta zasu nemeni, yanzu haka tare da ƴan sanda muka zo sun ga gidan mu" AMMIE dake saurara SHAHEED ta ce, "Allahu akhabar yaro kenan ƙila ka mata kama da wani nata cikin dangi, Allah ya bayana iyayenki wannan yarinya.! ta faɗa tana ƙarewa ILHAM ɗin kallo SHAHEED ya amsa da "amin.! can ƙasa AMMIE dake kallon ILHAM sosai ta ce, "ikon Allah yarinyar kamar ƴar dangi.! ɗago idanu SHAHEED yayi da sauri wanda hakan yayi daidai da kiran sallah asuba yana kallon AMMIE da ILHAM ɗin ya ce, "kawai dan tana fara ne AMMIE, ni zan wuce masallaci sallah.! SHAHEED ya faɗa yana miƙewa itama ILHAM miƙewa tayi riƙe da ƙafarsa ɗan rankwafawa SHAHEED yayi yana kallon cute face ɗin ILHAM ya ce, "BABY ki zauna nan tare da UMMA da AMMIE sallah zamu tafi ni da hamma NABIL yanzu zan dawo kin ji.! ya faɗa yana jan kumatunta turo baki tayi kamar zata fashe da kuka tana raba ido tana kallon SHAHEED ɗan murmusawa AMMIE tayi ta ce, "ikon Allah, Allah ya baka yarinya daga sama" ɗan murmushi SHAHEED yayi yana kama hannu ILHAM ɗin ya ce, "je ki wajan AMMIE.!
"zo nan kin ji yanzu zai dawo," cewar AMMIE tana kama hannun ILHAM ta zaunar da ita saman cinyarta ɗan siririn kuka ta saki tana kallon SHAHEED dake tsaye AMMIE ta ce, "yi tafiyarka sallah baza ka biye mata ba zata daina kukan da zarar ta fuskanci baka kusa" kallon NABIL SHAHEED yayi ya ce, "taso mu wuce masallaci kayi wani zaune" SHAHEED ya faɗa yanayin gaba.
Alwala suka ɗaura suka wuce masallaci kusan ma dangin su duk nan kusa suke, koda suka fito daga masallaci nan suka shiga gagaida manyan su da filaci suna amsawa yayinda dangin mahaifinsu ke amsawa ciki-ciki wasu har sauri suke su gudu gida, gudun kar SHAHEED ya tanbaye su kuɗin abin kari ko na magani mahaifiyarsa kasancewar sun ji labarin ta dawo daga asibitin birni saboda rashin kuɗin magani.
Hannu NABIL SHAHEED ya kama yana tanbayarsa me yake son ci cike da murna ya ce, "Shayi da biredi hamma.! wajen mai shayin unguwar sukayi SHAHEED ya siya bread da ruwan tea aka ƙula masa ruwan shayin a leda, kwai bakwai yasa aka fashe masa aka soya masa mai shayi sai washe baki yake yana cewa, "yau Allah ya buɗa kenan malam SHAHEED to Allah ya cigaba da buɗawa muma mu samu ƙarƙashin ku" ba tare da SHAHEED ya tankasa ba ya zaro 2k ya miƙa masa, ya miƙawa NABIL ledoji ya riƙe sauran har yayi gaba mai shayi ya ce, "baka amshi canjin ka ba" ahankali SHAHEED yace, "ka mun sadaka da canjin" ya faɗa gami da yin gaba suna isowa gida da sallama ILHAM dake takure kusa da AMMIE tana jin muryar SHAHEED ta miƙe tayi hanyar waje tana kwaɓe fuska kamar zata fashe da kuka, ɗan duƙawa SHAHEED yayi ya buɗe mata hannayensa da gudu ta danno tayi jikinsa cike da tsantsar farin ciki da zalla yarinta, kanta ya shafa yana cewa, "iya rigima baby" ya faɗa yana ja mata kumatu ya kama hannunta suka ƙarasa ciki AMMIE ta ce, "madallah daka dawo da wuri dan sam taƙi yarda ta saki jiki sai ɗan siririn kuka take" ledojin hannunsa ya miƙawa AMMIE ya ce, "ga wannna ku samu ku ci wani abu, ni fita zanyi yanzu"
"ina kuma zuwa da sasafen nan SHAHEED bayan jiya ka dawo cikin tsohon dare.?
"Ina son nayi wasu shirye-shirye ne, dan wannan karan tare da su UMMA nake son tafiya sai na nema mata magani acan tunda Allah ya buɗa mana acan munfi samun kuɗin shiga" jikin AMMIE ne yayi sanyi ta ce, "yanzu da jikinta haka zaku tafi har wata ƙasa SHAHEED.? kallon AMMIE SHAHEED yake galala ya ce, "ke baki bin mu"
"a'a SHAHEED ni ina nan tunda akwai sauran yara nan" ɓata fuska SHAHEED yayi ya ce, "amma.! katsesa AMMIE tayi da cewa, "ku dai ɗin ku tafi dan hakan ma sai yafi tunda su ASHURU sun kasa riƙe amanar da uban ku ya bari nima sunfi ƙarfi na" AMMIE ta faɗa idanunta cike da hawaye ta ce, "Allah ya gani yaran nan nayi iya bakin ƙoƙari na baki ne kaɗai ban masu ba" AMMIE ta faɗa tana share hawayen takaici dana baƙin ciki SHAHEED ma kasa magana yayi....*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...