muwaddat
hauesh
- LECTURAS 151,926
- Votos 4,233
- Partes 15
"auwal ni ko sai nake ganin kamar kayi kankata a batun soyayya balle kuma akai ga batun aure ,yanzu fa kake shekara 22 a duniya , ba soyayya ce ta dace da Kai ba, karutu ne ya dace da rayuwarka, bugu da k'ari ita wacce kake so din ta girmeka .
ya dubi mahaifiyarsa kamar zaiyi kuka yace" ni kaina nasan soyayya bata dace dani ba, ban san ya'akayi zuciyata ta afka wannan lamarin mai wuya misaltuwa ba ,zuciyata bata yi shawara da ni, na dauki abun amatsayin wata jarabawa ce daga Allah,.. ki yarda ummi ki amince ki bani auren diyarki muwaddat, ni ita kadai nake so,duk rayuwar da babu ita to babu auwal ..
faiza idanunta taf da ruwan hawaye ta dubi auwal cikin muryar kuka tace " in har zaka iya son yayata data girmemaka ,ni mai zai hana ka so ni, tunda nima jininta ce uwa daya uba daya, gashi Allah ya jarabeni da matsanancin soyayarka, nice daidai da kai ba yan'uwata ba, ni yafi dacewa kaso takarasa mgnr tana kuka..
auwal batare daya dubeta ba yace "nayi rantsuwa da Allah har yau sama da shekara sha takwas kenan ban taba kaunar wata diya mace ba sai yayarki muwaddat, ban taba jin sonki na daidai da second daya ba, ni matsayin k'anwata na d'aukeki, amman batu na soyayya babu shi atsakaninmu, muwaddat ce acikin kokan raina, ina sonta tamkar raina ,ita kad'ai ce macen da nake jin zata kashe iya kashe min ki shi ruwan danake d'auke dashi na tsawon shekaru.......