ZakiyyaAuwal's Reading List
177 story
YARIMA JUNAYD بقلم Jiddasmapi
Jiddasmapi
  • WpView
    مقروء 40,729
  • WpVote
    صوت 463
  • WpPart
    فصول 59
Soyayya me zafi, haɗe da ƙauna
A Gidan Mami بقلم Miss_Leeymart
Miss_Leeymart
  • WpView
    مقروء 6,983
  • WpVote
    صوت 144
  • WpPart
    فصول 25
Labari ne mai cikeda kalubalen da mahaifiya(mami)ta ke fuskanta bayan rasuwar uban yayanta!yadda zata shiga wani sabon rayuwa wanda bata taba tsammanin ganinta a ciki ba,maimakon ya'yanta su kwantar mata da hankali sai sukeyin tsabanin haka,har suke daura mata laifin talauchin su,bakaken maganganu,da hantarar ta,da wulakanci!Shin yayan da suka wulakanta mahaifiyarsu zasu ga daidai a rayuwarsu kuwa? Ya ya rayuwar jamal,Afaaf,muneera da Faruk zai kasance? Ku biyoni domin jin sauran labarin!
TAFIYAR MU (Completed) بقلم suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    مقروء 27,093
  • WpVote
    صوت 1,159
  • WpPart
    فصول 20
Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?
MATAR AMEER بقلم PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    مقروء 38,338
  • WpVote
    صوت 1,353
  • WpPart
    فصول 71
'Ammi ya zan yi da rayuwata? Ya kuke so in yi da zuciyata? Ban taba ba...daidai da rana daya ban taba mafarkin yin rayuwar aure ba tare da Ameer ba. Na roke ku da Allah ku zuba idanuwanku kawai a kaina, ina ji da kun san yadda zuciyata ke tafarfasa a duk lokacin da kuka yi min zancen auren wani wanda ba Ameer ba da tuni kun daina...' Kuka sosai take yi, kukan da ke fitowa tun daga k'asan zuciyarta yana ratsowa tsakanin idanuwanta. 'Na sani akwai zafi da radadi Ameerah, na san miye so, na san gubarshi saboda ni ma na tab'a dandana. Sai dai Ameerah ba za mu zura miki idanuwa ba, shekarunki ashirin da takwas kenan babu aure, kina zaune jiran gawon shanu. Waye ya san inda Ameer yake yanzu? Wa ma yake da tabbacin yana da rai ko babu?'
MEEMA FARUKH بقلم UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    مقروء 9,713
  • WpVote
    صوت 486
  • WpPart
    فصول 66
tana ganin lokaci ɗaya Allah ya jarabbe su da matsaloli kala-kala har hakan yayi sanadin tafiyan mahaifiyar ta, ta kasa yarda mahaifiyar ta zata yi musu haka ita da mahaifin ta, duk rayuwar da suka gina tsawon shekaru amma lokaci ɗaya ta rushe musu, meyasa baza tayi haƙuri na ɗan lokaci Abee ya samu lafiya ba? Meyasa zata nuna gajiyawa da laluran Abee ɗin ta? Ashe dama ba son su take yi ba da har zata iya tsallake su tabar su a wannan duniyar? Haƙiƙa abin ya taɓa ta wanda lokaci ɗaya gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta sauya mata, wanda tana ji kamar gwara mutuwar ta da wannan rayuwar, ta rasa komi nata, ba ta da kowa sai ita kaɗai, taya zata iya rayuwa a haka? Komi nata na farin ciki ya wargaje ya barta. Mutuwa shi ne ya fi cancanta a gare ta. Sai kuma ga mummunar ƙaddara ya same ta wanda ya sauya mata gaba ɗaya rayuwar ta.
WASIYAR AURE😭❤❤complete بقلم Najaatu_naira
Najaatu_naira
  • WpView
    مقروء 49,198
  • WpVote
    صوت 8,797
  • WpPart
    فصول 55
Atsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa yagayamai duk halin da yake ciki, "Dakata kanatsu ingaya maka taimakon dazaka bata kan nazo", Hamza nashare hawaye yace "toh inajinka dan Allah gayamin ko numfashi batayi" "Okay compressing zakai mata sau talatin da biyu inbata farfadoba saika bata Mouth to Mouth respiration kanatsu kaimata dakyau dan Allah" "Toh saikazo", Hamza yafada yakashe wayar", Compressing yafara mata harya wuce 'ka'ida, ganin basauki sai Allah yadawo yarike haccinta yasa bakinsa cikin nata yahura, Agurguje yadago kai yana sharta zuba yakalleta ba labari, jiki narawa yakallah sama yatattaro duk wani nutsuwa yacire 'dar yarintsa ido yamaida lips dinshi yakafa kan nata yahurawa cikin kwarewa, 'Dago kan dazai yaduba yaga idonsa kwar cikin nata, Kasa magana yayi dan murna yarungumeta dasauri yana maida ajiyar zuciya yakira sunanta cikin muryar da batai tsammaniba, wani irin sexy voice maidadin saurare taji yace "Ushna", Yadda yayi maganar yasa takasa amsawa, tayi shiru tana 'ko'karin tantance duniyar da take, shin mafarkine ko wani irin al'amarine data kasa fahimta sai saurare?, "I was very scared! i thought i'll lose u too, banso nazam sanadin mutuwarki kamar yarda nayi na yarki Ushna, dan Allah kiyi hakuri sharrin shaidanne", Zata yun'kura tatashi taji anyi gyaran murya akansu, sanadin dayasa Hamza yai firgigi ya murguna atsorace kamar mara gaskiya yajuyo.
DARE DUBU بقلم PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    مقروء 39,166
  • WpVote
    صوت 2,424
  • WpPart
    فصول 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da ba ta da magani? Shin dukkanin mutane ne ke jingine mafarkai da burikansu, su sadaukar da duk wani farincikinsu domin aminnansu? Ba matsalarta ce kadai ta dauka matsala ba, har matsalar aminiyarta ta mayar da ita tata, yayin da ta ci alwashin daukar fansa , ta ajiye burinta a gefe. Ku shigo cikin labarin DARE DUBU, na muku alkawarin ba za ku yi nadamar bibiyarsa ba.
WANNAN CE QADDARARMU EPISODE 1 بقلم hauesh
hauesh
  • WpView
    مقروء 125,845
  • WpVote
    صوت 8,738
  • WpPart
    فصول 70
Wannan ce qaddararmu labari ne daya faru a gaske ,sannan labari ne dake tattare da nishadartawa fadakarwa ilimantarwa, uwa uba yarda da kaddamar da ta fadawa mutun, sannan yana tattare da tsaftacciyar soyayya ...
AURE UKU(completed) بقلم Chuchujay
Chuchujay
  • WpView
    مقروء 57,138
  • WpVote
    صوت 2,023
  • WpPart
    فصول 32
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimmanci kana yaranta wadda kaɗdarar samunsu ta rarraba mata Aure . Kalma ɗaya zaka faɗa ta bata mata rai shine kushe mata Aikinta ko nuna wasa a duk wani abu da ya shafi Aikinta . Ita ɗin kwarariyace kuma gogaggiya akan duk wani abu da ya safi surgery,ba kasar ta ba hatta a wasu kasashen tana zuwa aiki. Bangaren soyayya fa? Bata dauki soyayya a bakin komai ba tunda dukkan Aurenta guda ɗaya ne tayi na soyayya kuma shima bai karbe ta ba wanda hakan yasa ta yanke shawarar saka soyayya a ƙwandan shara duk da kuwa tayin da ake kawo mata ,ta gama yanke imani da soyayya akan duk wani ɗa namiji wanda haka yasa mutane da dama ke mata kazafi da mata take so duba da ƙin mazanta karara a fili. Amma menene dalilin tsanar tasu da tayi? Menene yasa ta cire mazan daga tunaninta da zuciyarta baki daya? Shin zata faɗa soyayyar wani ɗa namiji ko a'a? Idan zata faɗa wanenen wannan mai sa'ar?. DR IMAM MUKTAR PAKI, Saurayi dan kimanin shekaru Ishirin da tara ,bai taba Aure ba, Dalibi wanda yake neman sake gogewa akan Aikin surgery ,shekara ɗaya wadda kareta ne kaɗai zai bashi kwali da kuma lasisin Fara yin surgery ,kaddara itace tayi aikinta ta ɗauko sa kan kachakar ta kawosa CITY TEACHING HOSPITAL inda yake ƙarkashin jagorancin likitar da kowa ke tsoro da shakka, Mene zai faru idan shi bai ji wannan feelings ɗin ba sai wani daban wanda shi kansa bazaya iya fassarawa ba? Shin ya wannan kaɗdarar tasu zata kasance? Shin Wanne irin chakwakiya Imam ke shirin ɗaukowa kansa domin wannan likitar da ya ke kan giyar so AURENTA UKU ,Ƴaƴanta uku a yayin da shi ko na fari bai taba yi ba. Ku biyo ɗiya jamilu domin jin yarda wannan labarin na IMAM da UMAIMAH zai kasance !
NANA AMINATU 2022 بقلم UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    مقروء 16,495
  • WpVote
    صوت 916
  • WpPart
    فصول 56
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.