AbdulSudeis's Reading List
3 stories
WANDA BAI JI BARI BA.... by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 3,936
  • WpVote
    Votes 275
  • WpPart
    Parts 22
Iska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin sautin na matsowa. Kamar yanda ya bayyanar mata a karan farko wannan karan ma wata zabgegiyar Abaya ta hango baƙa, tsawon abayar ya kece tsawon bishiyoyin dake cikin dokar Dajin sai da ta ɗaga kanta sama sosai sannan ta hango dai-dai kansa sai dai kansa ne amma babu alamar fuska ajikinsa. Ƙarasowa yayi gabanta ya tsugunna cikin murya mara daɗin sauraro ya fara magana, " Bingirsima baguar kinbasu wakisfatminar, kisasu biragu kilbasu tattarakimbas wajihagar, farafafus bintigad gurmanas YUSRA? harbaskila mindadu bar washbasbismas shizas kima bu warsa? " ( A karo na biyu ina ƙara miki barka da zuwa cikin daularmu nida ahalina, da sannu zan gabatar da ke ga sauran iyalaina domin kusan juna keda su ina fatan kina jina YUSRA? Ga ƴaƴana nan sun fara zuwa gaisheki ina fatan zaki basu kulawa ? ) Wannan zabgegen Aljanin ya ƙarasa maganar yana nuna mata waɗannan hallittun masu fasalin Maguna da fukafukai. Yusra da tuni hawaye yake wankewa fuska ta ƙara durƙushewa ƙasa cikin sigar magiya tana faɗin, " Ka dubi girman Allah da Annabi ba dan ni ba, ba dan halina ba kayi haƙuri ka maidani cikin mutane dan Allah, wallahi bazan iya rayuwa cikinku ba na tuba dan Allah kamun rai " Miƙewa tsaye yayi sannan yayi taku biyu zuwa uku sannan ya waigo ya ce mata, " Hargigas markusa bayas tinga " ( Tashi tsaye kije jikin waccen bishiyar kukar ) Yusra har tuntuɓe take da sauri ta miƙe tsaye saura kaɗan Abayar jikinta ta kayar da ita, jikin bishiyar taje ta tsaya tana sauraron abinda zai sake faɗa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin. " YUSRA Lilbas faragaras binsafa walgibas zalzulfat kinari " ( YUSRA kalli Abayar jikinki da kyau, idan har kin iya cireta daga jikinki
JARUMAI 2021 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 1,264
  • WpVote
    Votes 133
  • WpPart
    Parts 25
Su shida 6 ne suke tafiya cikin k'urmun bak'in dajin da baka iya hango k'arshen shi, kai sai kayi kwanaki kana zagaye dajin batare da ka fita ciki ba, daji ne dake da hatsarin gaske fiye da tunanin mutum, duk wani bala'o'i ba wanda be had'a ba, ga namomin daji da dodanni har aljanu akwai, fitintinu dai daban-daban, amma haka suke ratsa dajin batare da sunji tsoro ba Kasance dani don jin su wanene waɗannan mutanen.
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana) by Al_Ashtar
Al_Ashtar
  • WpView
    Reads 32,889
  • WpVote
    Votes 1,362
  • WpPart
    Parts 51
Labarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske labarin da ta kira da zanen ƙaddara. Mahaifiyar Amriya ce ke sanar da ita, ita fa ƴarta yau shekarunta huɗu da rasuwa bisa haɗari, Zahara ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na ban mamaki. Ita data haɗu da yarinya a yau sukayi hira, harma ta manta da gyalenta, yanzu gashi ta zo gidansu ana shaida mata ta yi shekaru huɗu da rasuwa. Ku biyo mu domin jin yaya zata ƙarƙare cikin wannan ƙayataccen labari.