JUYIN KWAƊO
Shin kun taɓa tunanin cewa wata rana rayuwa za ta muku juyi, irin juyin waina a tanda?. Tamkar yanda rayuwar kwaɗo kan yi juyi daga ruwa zuwa ruwan zafi?. Wani hali za ka tsinci kanka a sanda ƙofofin mafita suka kulle gareka, yayin da kake tsaka da buƙatar hanyar kuɓuta? Yaya za ka yi a sanda kake ji da ganin mutuwa n...