Liste de Lecture de MahamadouMimi
36 stories
NANA AMINATU 2022 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 15,185
  • WpVote
    Votes 912
  • WpPart
    Parts 56
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
ASEELA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 22,449
  • WpVote
    Votes 1,704
  • WpPart
    Parts 52
Ƙwarangwal ɗin suna tafe wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga gaɓɓan jikinsu tamkar waɗanda aka kunna fanfo ajikinsu, daga kowanne ɓangaren hallita akwai shugabansu wanda shi ne yake kan gaba su kuma suna biye dashi abaya, hannu kowanne shugaba ɗauke yake da wani farin ƙyale da jikinsa yake da ɗishi-dishin jini, ahankali ta fara ɗaga ƙafarta tana ƙoƙarin ja da baya da niyyar guduwa sai dai nauyin jikinta shi ya hana ta gudu har suka ƙaraso inda take, mararta ce ta ɗan karta mata bayanta ya riƙe sannu ahankali ta tsugunna ta duƙa agurin wani irin azababben ciwo na cinta, jeruwa suka yi sahu-sahu sannan suka fara zagaye ta suna faɗin wasu kalmomi da sam bata fahimtar mai suke faɗa, " YAMDUMISA! YAMDUMISA!! YAMDUMISA BISRATIK KUZAR!!!, KIMBASA MIN! KIMBASA MIN!! KIMBASA MIN MAR FAZKINBAT!!! " ( BARKA! BARKA!! BARKA DAI SHUGABA!!!, DAWOWARKU NASARA CE! DAWOWARKU NASARA CE!! DAWOWARKU NASARA CE TARE DA FANSA!!! ) haka suka dinga zagayeta suna maimaita kalmomin bakinsu shugaban ɓangarori biyun masu ɗauke da farin ƙyallen nan suna zazzaga mata wannan kyalen akanta, ciwon da take ji ƙara tsananta yake banda ihu ba abinda takeyi sai kiran sunan KABEER take tana maimaitawa, idan abun ya kuma tsananta ta kuma kiran Kabeer ko Habeebee amma ko gezau basu fasa wannan surutan nasu ba kuma basu fasa zagayeta ba suna yarfa mata wannan farin ƙyallen ba, wani lokacin ma wannan ruwan mai yauƙi na ɗiga ajikinta, ita bata ma san suna yi ba saboda azabar ciwo fatanta kabeer ya kawo mata ɗauki. Ta ɗan ɗauki lokaci ahaka kamar minti talatin ahaka sai ji sukayi kukan jariri alokacin ta galabaita sosai amma ahaka take yunƙurin ɗaukar abinda ta haifa dan neman tsira daga garesu, sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni shugaban ƙwarangwal ɗin nan ya kai hannu yayin da shima shugaban mai mummunar hallitar shima ya kai hannunsa, atare suka suka ɗago jaririyar kowanne ya riƙe hannunta ɗaya yana faɗin, " KAGARSIN BIDA, KAGARSIN BIDA LANBISMA GIRUS " ( KA
kotu by sulemankaudi
sulemankaudi
  • WpView
    Reads 14
  • WpVote
    Votes 1
  • WpPart
    Parts 1
Wata Kotun shari'ar Musulunci da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta bayar da umarnin tono wani mutum daga kabarinsa bayan mako daya da binne shi. Mataimakan shugaban hukumar Hisbah ta jihar mai kula da ayyuka na musamman Sheikh Muhammad Al-bakri ne ya tabbatar wa BBC wannan lamari a ranar Talata. Kotun karkashin jagorancin Mai shari'a Sani Yola ce ta bayar da umarnin a yi wa gawar sutura kasancewar hukumar Hisbah ta roki kotun da ta bai wa asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano umarnin bayar da gawar wani mai suna Abdullahi Obinwa ga iyalansa domin binnewa kamar yadda addinin musulunci ya tanada. Da gaske Kungiyar Amnesty ta ce za ta ceci Maryam Sanda? Hukumar yaki da rashawa tana binciken ma'aikatan Masarautar Kano Muna kokarin sasanta Ganduje da Sarkin Kano -Ibrahim Shekarau Bayan wannan umarni ne kuma aka samu akasi aka musanya gawar da ta wani dan kabilar Igbo mai suna Basil Ejensi. Hakan ya sa wasu 'yan kabilar Igbo garzayawa kotun Ustaz Ibrahim Sarki Yola inda suka bayyana wa kotun cewa an yi musu musanyar gawa. Bayan ta saurari jawabinsu ne kuma, kotun ta bayar da umarnin a hako gawar da ta bayar da umarnin binnewa mako guda da ya gabata. A cewar Al-bakri, janyewar da shaidu suka yi ne ya sa kotun ta yanke huku ok ncin bayar da gawar. Sai dai kawo yanzu, ba a san inda gawar wancan mutumin da hukumar ta Hisbah take da'awar cewa ya musulunta ba. Amma tuni hukumar ta Hisbah ta ce sun fara bincike kan lamarin saboda akwai 'alamun lauje cikin nadi'. Wasu bayanan kuma na cewa matar mutumin da aka ce ya musulunta wanda kotu ta yi umarnin binne shi bisa tanadin addinin musulunci, ta yi batan dabo
MAKIRCI KO ASIRI  by _bambiee
_bambiee
  • WpView
    Reads 63,988
  • WpVote
    Votes 6,193
  • WpPart
    Parts 26
Suna zaman Amana da matarshi babu wanda ya taba jin kansu, daga shigowar Mufeedah gidan ta wargaza masu zama ta raba kan ma auratan ya tsani Ramlah ko sunanta bai san a fada gabanshi.
SAKAMAKO by SURAYYAHMS
SURAYYAHMS
  • WpView
    Reads 848,806
  • WpVote
    Votes 44,309
  • WpPart
    Parts 48
Ya zatayi da Yarinyar da bata kai ta goge mata takalmi ba amma ta kwace mata miji?...... #Suhan #captain majeed # Zarah
Mai Tafiya by donutfairy
donutfairy
  • WpView
    Reads 199,263
  • WpVote
    Votes 20,125
  • WpPart
    Parts 29
Labarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeria mu ga yadda za ta kaya! Mai tafiya..wani guzuri ka tanada??????
KURUCIYAR JIDDAH by asykhaleel
asykhaleel
  • WpView
    Reads 58,562
  • WpVote
    Votes 3,213
  • WpPart
    Parts 26
Labarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.
MIJIN ALJANAH by Kingboyisah
Kingboyisah
  • WpView
    Reads 3,112
  • WpVote
    Votes 124
  • WpPart
    Parts 3
Labarin Al'ameen da matarsa Yasmeen shahararrun 'yan boko wanda basu damu da addini ba. Garin shige-shigen Al'ameen daga karshe ya auri Aljana ba tare da ya sani ba kuma ta tare a gidanshi a matsayin amarya. Yayin da taci gaba da gana wa matarsa Yasmeen azaba tana firgitata a ko wane lokaci. Shin ko zaku iya bamu lokacin ku ta hanyar bibiyar wannan littafi mai suna Mijin Aljana? ga masu bukatar Audio na littafin zaku iya ziyartar channel din Mamaki Tv a youtube a can zaku sama full dinsa
AKASIN ZUCIYA💔 by Aishadaleel2
Aishadaleel2
  • WpView
    Reads 831
  • WpVote
    Votes 95
  • WpPart
    Parts 5
Qaddarar zuciya; a rayuwa za ka iya son wani a yayin da shi kuma bai da buqatarka, hakan kuma ba yana nufin ya tsaneka bane, dalili kuwa shi SO mai duka ne ke ɗarsawa a zuƙatan bayinsa, babu wanda ya isa ya saka wa wani son wani ba tare da ubangiji ya rubuta hakan ba. So kan komawa ta zamto kiyayya a inda kiyayya ke koma wa ta zamto soyayya, shi yasa ma Manzon Allah ya ce " kaso masoyinka kaɗan kaɗan don watarana zai iya dawowa maƙiyinka, sa'annan ya ci gaba da cewa ka ƙi maƙiyinka kaɗan don watarana zai iya zamto masoyinka" Labarin dake tattare da tausayi, ban takaici, maida alkairi da sharri, son maso wani, kiyayya, nadama, tsantsan talauci, arziki, biyayya, sadaukarwa. Duk a cikin wannan littafin mai suna AKASIN ZUCIYA! Makaho ne shi, baya gani ya samu wannan lalurar ne tun haihuwarsa. Da zuciyarsa yake ganin komai, Allah yayi masa muguwar fasaha da basira. Talakawa ne su sosai wannan dalilin ya Sanya iyayensa kasa sama masa lafiyar idanunsa. Tun ganin sa da tayi zuciyarta ta kamu da tsananin kaunarsa, ta taimakesa ta kasance da shi, itace kawai ke masa san so, ita ce kawai ta nuna masa so da kauna duk da kasance warsa makaho (nakasaishe). Tana taimaka masa amasa aiki a idanuwansa har ya soma gani, tun budewar idanuwansa ya ji duk duniya babu Wanda ya tsana sama da ita. Amma yana kunyar maida alkairi da sharri. Shin ya zai tunkareta da batun nan? Shin ya kyautata mata kuwa?. Just relax and find out in this hilarious story where haterate turns to love, love turns to pure haterate find out in AKASIN ZUCIYOYI BIYU Shin Ya zata kaya tsakanin waanan bayin Allah biyu? Zai SO ta? Ko zai ki ta?. Ku biyoni don jin yadda zata kaya.
 (GYARAKANKI) by ummuelham
ummuelham
  • WpView
    Reads 23,443
  • WpVote
    Votes 1,157
  • WpPart
    Parts 35
wanna litafi me suna GYARAKANKI litafine da zai kawomiki magunguna da Suka kasance masu kyau da inganci Wanda Suka kunshi abubuwa kamar haka. Gyaran jiki wande yashifi bangaren kamshi da gyaran fuska d gyaran gashi da dai sauran su. Bangare nabiyu Kuma yashifi bangaren ni'ima na mata matsi magunguna masu inagan ci Wanda Zaki had da kanki batare da kinsha wahalaba Kuma basuda matsala ga lafiyarki Bangare na uku kuma bangarene da Zaki samu addu'oi dasuka shifi sihiri,janyo hankalin megida ,mallaka, addu'a domin rinjaye akan abokin gaba ,janyo hankalin saurayi,fahintar karatu,neman kasuwanci da daukaka ,d samun sa'ar jarabawa,Ina masu samun matsala da kishiya kizo ganaki,da wace uwar miji Bata santa ,Ina wace miji ke juya mata baya saboda abokiyar zamanta,ina iyayen da yaransu basa fahintar karatu ,Ina iyayyen da yarasu keyawan sasu magana Suma ganasu,kubiyoni domin samun dabaru da salon janye hankalin megida.