AishaBadamasiUsman's Reading List
7 stories
GADAR ZARE by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 402,272
  • WpVote
    Votes 19,018
  • WpPart
    Parts 85
A firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu yana yarfa hannunsa, zumbur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko robar ruwa ya bulbulawa kansa "Akan ido na suka k'one gidan mu, mahaifiya ta, mahaifi na, k'anne na duk suka mutu akan kunne na ina jiyo ihun su *************** "Cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan wanda yayi min ciki nan ba. Kanta tayo gadan-gadan tana nizaki rainawa hankali, ta shak'e ta idonta suka kakkafe ************** A cikin gidan yarin yake ihu yana kuka yace " sunci Amana ta, sunyi min butulci, na yarda dasu amma sun ci min amana sun had'a min GADAR ZARE Amintattu nane suka yi silar zuwa na gidan yarin, sun raba ni da kowa nawa sun raba ni farin cikina,cikin matsanancin kuka yace " wallahi koda zan rasa komai na rayuwata bazan kyale su ba. Sun mun sharri, sun had'a man makirci da GADAR ZARE ************* "Koken a cikin kayana kuma, kafin ya k'ara sa maganar dubbun police sun kewaye shi da bindugogi, Ana cikin haka wayarsa ta fara ringing, dakyar ya samu ikon d'agawa, ji yayi muryarsa ta tintsere da dariya yace " nine, d'an uwanka, kaga yadda nayi wasa da hankalinka ko, na nuna maka halin 'yan Adam Cikin rawar murya yace " mai yasa kaci amanata? " saboda ina santa, ita rayuwa tace kuma mallakina , Wani irin mahaucin ihu ya saki tare da buga wayar da k'asa .
K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER) by Nuceeyluv
Nuceeyluv
  • WpView
    Reads 9,837
  • WpVote
    Votes 315
  • WpPart
    Parts 18
Littafin KASAITA littafi ne dake dauke da labarin SARAUTA, Wanda shi Yareema NASEER ya Shiga kalubale dayawa na rayuwa a dalilin sarauta, a gefe guda kuwa ya fada makauniyar soyayyar ta batare daya ankare ba, dukda yanada wata masoyiyar a gefe wacce yake ganin itace sarauniyar birnin zuciyar sa sai gashi zancen yasha bambam a Inda beyi tsammanin Hakan ba, shin Koh ya labarin zai kasance? Koh wanne kalubalen yake fuskanta? wacece Wannan daya fada makauniyar soyayyar tata? Mu hadu tsundum a cikin littafin KASAITA domin... ILMANTUWA NISHADANTUWA A cikin kayataccen littafin KASAITA, taku a koda yaushe NUCEEYLUV 😘.
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,505,682
  • WpVote
    Votes 121,610
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum
MUTUM DA DUNIYARSA...... by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 130,323
  • WpVote
    Votes 9,459
  • WpPart
    Parts 41
Wannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magidanta da yawa basa son a haifa musu ƴaƴa mata, abin kuma zai baka mamaki idan zaka tarasu wajen buƙatar jin dalilinsu, musani UBANGIJI ya fimu sanin mu su wanene? miyasa yayimu jinsi-jinsi, yare daban-daban, zuri'a daban-daban. kai dai ka roƙi ALLAH ya baka mai albarka kawai shine magana.
Bakuwar Fuska by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 41,807
  • WpVote
    Votes 3,872
  • WpPart
    Parts 50
"Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al'arshi mai girma." Cewar Ishraq Sulaiman, hannunshi dafe da zuciyarshi da ke bugawa da sauri.
ZABEN TUMUN DARE by maryamtalba
maryamtalba
  • WpView
    Reads 17,555
  • WpVote
    Votes 3,310
  • WpPart
    Parts 47
Mafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga cikinmu kyau shine abin so , komi mai kyau mukeso ba ruwan mu da badinin abin, tuhume tuhume sunyi yawa kan ya'yan masu kudi, da dama ana ganin basu iya komi ba! Daga kan darajta dan adam, tsoron Allah su, zaman aurensu da mu'amalarsu da tarbiyarsu, ko kunsan dan talaka yafi Dan maikudi iya izza da wulakanta dan adam idan ya samu ko duniya a hannunsa, ba duk abinda ka gani bane yake zama dai dai da ko tunaninka. Dayawanmu ZABIN ALLAH bashi bane abinda mukeso, mukanso ra'ayin zuciya da abinda ta kullah, har ya kaimu ga ZABEN TUMUN DARE! Zabi mafi muni a rayuwa.......... Ku biyoni dn jin yadda ZABIN MUHAMMAD KABEER yake kasancewa cikin duniyar tunaninsa.
Zanen Dutse Complete✓ by Aysha-Shafiee
Aysha-Shafiee
  • WpView
    Reads 185,372
  • WpVote
    Votes 25,414
  • WpPart
    Parts 35
#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wane yanayi zata zo? Mai kyau? Ko akasin haka? Wad'annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk'alami ya bushe akansa. Don wata k'addarar tamkar ZANEN DUTSE ce... Babu wani abu da ya isa ya canja ta!