Lawalzaenab9's Reading List
113 stories
Al-Mustapha  by Nooriyamustafa
Al-Mustapha
Nooriyamustafa
  • Reads 5,820
  • Votes 44
  • Parts 5
Al-Mustapha bashi da wani abu da ya sa gaba sai neman matan aure da yan-mata, sai kashe kudin da mahaifinsa ya mutu ya bar mishi.
A JINI NA TAKE by Aishatuh_M
A JINI NA TAKE
Aishatuh_M
  • Reads 64,437
  • Votes 3,049
  • Parts 12
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu? Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.
zuciyar masoyi  by hauesh
zuciyar masoyi
hauesh
  • Reads 114,508
  • Votes 4,766
  • Parts 63
zuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
RAYUWAR BADIYYA ✅
Aishatuh_M
  • Reads 265,592
  • Votes 21,150
  • Parts 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
NAILA  by HafsatMohdArabi
NAILA
HafsatMohdArabi
  • Reads 64,666
  • Votes 5,277
  • Parts 70
A Story about a young girl NAila who has a gift of seeing the unseen things and who has to fight for her real identity......and also the evil forces who are against her can NAILA really make it.......
YA JI TA MATA by miss_untichlobanty
YA JI TA MATA
miss_untichlobanty
  • Reads 85,362
  • Votes 8,151
  • Parts 63
Wannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsira ba domin kuwa babu wacce take iya zaman sati biyu dashi tsanani kwana 10 sai su gudu. Toh fa an Sami matsala domin reshe ta juye da mujiya inda Allah ya hadosa da Wanda ta fisa jaraba toh yanzu kuma shi ke gudu. Wai ya za'a kwashe ne a lokacin da iyayen sa sukace bai isa ya saketa ba kamar yadda ya dafa kur'ani cewa bazai saketa ba? KU BIYONI CIKIN WANNAN LABARI NAWA DAN JIN YADDA ZA'A KAYA. SAURAN LABARAI NA: 1.KURUCIYAR MINAL 2. YARINYAR CE TAYI MIN FYADE AND NOW 3. YAJI TA MATA.
KAUNACE SILA by hauesh
KAUNACE SILA
hauesh
  • Reads 94,908
  • Votes 3,118
  • Parts 62
kaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.
AMINATU (COMPLETED) by munariii
AMINATU (COMPLETED)
munariii
  • Reads 34,812
  • Votes 4,465
  • Parts 25
A story in both english and native hausa language: Aminatu is a girl who loves money more than anything. She'll do anything in her power to marry a rich man. Luckily for her she got a job as a secretary to the most influential man in the city. But will she be able to accomplish her dream and her only life goal?? follow me and add the book to your reading list, i promise you won't regret it.
BABBAN GORO by KhadeejaCandy
BABBAN GORO
KhadeejaCandy
  • Reads 274,458
  • Votes 21,558
  • Parts 62
NOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da gaske babu sona a cikin zuciyarki!" Kasa ɗago kai tayi ta kalleshi balle har ta iya furta abunda ya bukace ta dayi. Hakan yasa shi yin murmushi mai sauti, "You see ba zaki iya ba, kin cutar dani Kairat da kika karkata zuciyata zuwa ga Minal bayan kinsan halinta kin kuma san bata dace dani ba, i hate you but i hate her more" Yana kaiwa nan ya kaɓe mata rigarsa ya juya a fusace ya bar mata falon, Sai da taji tashin motarsa sannan ta share hawayen dake idonta ta nufi kofar cikin gida, tana buɗe kofar taga Minal tsaye a bakin kofar da hawaye shaɓa-shaɓa a fuskarta. ®2017 ****************
KHADIJATUU by KhadeejaCandy
KHADIJATUU
KhadeejaCandy
  • Reads 281,068
  • Votes 24,676
  • Parts 66
NOT EDITED ⚠️ Yayi kyau matuƙa, yadin ya fito da farinsa da kuma kyaun fuskarsa, Idan ka kalleshi, sai ka ganshi kamar mai cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, al-halin sune abubuwan da suka masa tawaye. A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana lasa lip ɗinsa. Juyowa yayi yana wani taku da idan baka karance shi ba, zaka iya cewa na wulaƙanci ne da nuna isa, al-halin babu hakan a tare da shi ko kaɗan, ƙarasowa yayi gun da Khadijatu take kwance ya duƙo daidai ita, ya hura mata iska a fuska kamin ya kai hannu ya taɓa jikinta. Hannun yasa ya tallafota ta dawo saman cinyoyinsa, fuskarta na fuskantar tasa, ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, a hankali ya kai hannun ya shafa gefen fuskarta, tausayinta ne yake ƙara shiga zuciyarsa. Shi kansa yana ji a jikinsa akwai wani sirri dake tsakaninsa da haɗuwarsa da Khadijatu, sirrin da har yanzu bai san na minene ba, yana jin shi ɗin wani bangone a shafin rayuwarta, lallai idan har babu shi a ƙaddarar Khadijatu toh babu wanzuwar labarinsa a doron ƙasa, yana ji a jiki da kuma ruhinsa domin ita akayi shi, kamar yadda yake jin da a'ace ya rabu da ita tsakanin jiya zuwa yau da bai san yadda rayuwarsa zata kasance ba, bai san wane irin hali zai samu kansa ba, dan baya taɓa rasa natsuwarsa idan yana kusa da ita, idan tayi nisa dashi ji yake kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa. Ba sonta yake ba, dan baya tunanin zai iya buɗewa wata ƴa mace zuciyarsa, tun bayan abunda Malak tayi masa, sai dai kuma yana jin fiye da yadda yake ji idan yana tare da Malak, yana jinsa cikin wani yanayi wanda bai taɓa ji ba idan yana tare da Malak. ® 2018