SaadatuDanfulotikad1's Reading List
4 stories
MIJINA NE! ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 106,230
  • WpVote
    Votes 6,614
  • WpPart
    Parts 27
Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana tare dasu? Amma tabbas mijinta ne, shine. Ta tabbata shi din ne. Ga murmushin shi nan, dariyar shi, yanayin yadda yake tafiya. Wallahi shine! Shin mijin nata ne ko kuwa? Da gaske shi din take gani ko kuwa? Amma ba'a mutuwa a dawo. Saidai a yanayin yanda rayuwarta take juyata, takan iya cewa ita a nata fannin rayuwar, kila mutum yakan mutu sai ya dawo. Mijinta ne, kome zasuce bazata taba yarda dasu ba. Aisha Malumfashi.
RAI DA KADDARA by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 78,048
  • WpVote
    Votes 7,816
  • WpPart
    Parts 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba. Yelwa.
RAWANIN TSIYA | ✔ by fadeelarh1
fadeelarh1
  • WpView
    Reads 89,845
  • WpVote
    Votes 8,418
  • WpPart
    Parts 47
Halinta na girman kai, rashin kunya da wulaqanci su suka sanya ya tsane ta.. baya qaunar ya bude idanuwa ya gan ta a gaban shi... she disgusts him!! the feeling is mutual domin kuwa ita ma ta tsane shi.. ta tsane shi tun ranar da ta fara ganin shi... ta tsane shi saboda tunda ya shigo rayuwarta ya hana mata jin dadi kamar yadda ta saba..!!
RAI DAI by cutyfantasia
cutyfantasia
  • WpView
    Reads 19,882
  • WpVote
    Votes 1,608
  • WpPart
    Parts 63
Rai dai kirkirarren labari ne na rubuta domin fadakarwa, ilmantarwa da nishadantarwa. Duk wanda yaji wani abu me kamanceceniya da rayuwarsa arashi ne kawai aka samu. Ban yarda a juya mun labari zuwa kowacce irin siga ba, ban yarda a kwafe shi zuwa kowacce kafar sadarwar ba ba tare da izini na ba.