RaheenatuHud's Reading List
9 stories
JARUMAI 2021 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 1,264
  • WpVote
    Votes 133
  • WpPart
    Parts 25
Su shida 6 ne suke tafiya cikin k'urmun bak'in dajin da baka iya hango k'arshen shi, kai sai kayi kwanaki kana zagaye dajin batare da ka fita ciki ba, daji ne dake da hatsarin gaske fiye da tunanin mutum, duk wani bala'o'i ba wanda be had'a ba, ga namomin daji da dodanni har aljanu akwai, fitintinu dai daban-daban, amma haka suke ratsa dajin batare da sunji tsoro ba Kasance dani don jin su wanene waɗannan mutanen.
K'ORAMAR AJALI by ayshart647
ayshart647
  • WpView
    Reads 1,187
  • WpVote
    Votes 111
  • WpPart
    Parts 26
Labarin wani kyakkyawan ne saurayi wanda a kullum burinsa bai wuce ya ga anyi mutuwa ba, duk ranar da ba ayi ta ba, zai kasance cikin bakin ciki da 'bacin rai, saboda wannan dalili ne mutane suke masa lakabi da suna Dangin Mayu duk inda ya wulga mutane sai sun zubar da hawanya.
SAMIMA (MACIJIYA CE)🐍🐉 by fateemah0
fateemah0
  • WpView
    Reads 7,333
  • WpVote
    Votes 315
  • WpPart
    Parts 9
LITTAFIN SAMIMA (MACIJIYA CE), LABARI NE AKAN WATA YARINYA KYAKKYAWA DA AKA MAI DATA MACIJIYA, KUMA DUK WANDA YA TABATA KO YA BATA MATA RAI SUNAN SA GAWA, BAZAN IYA CIKAKU DA SURUTU BA, KU BIBIYE LABARI, PLS VOTE AND FOLLOW ME TNCU DEAR FANS
ƊAN BA ƘARA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 7,422
  • WpVote
    Votes 750
  • WpPart
    Parts 15
Salati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema Goggo Banda abinki kifin k'afa garshi da zai shigo cikin gida bama nan, idan nace kinfiye rigima kice zan gaya miki magana " ganin kifin na yi Mata murmushi yasa Goggo ta K'ara rafka wani salatin tana sakin tunkunyar tana yowa gaba, mejidda dariya takewa Goggo harda rik'e ciki tace, " Goggo wai me yake faruwa ne Dan Allah ko kunyar gudu bakiji ba? gudu kikeyi amma kamar me rawar Etigee" Goggo Bata bi ta Kan mejidda ba ta rabe ajikin katanga tana leken tunkunyar data jefar ,wani Kan kifi ta hango suna had'a ido ya K'ara kashe Mata ido daya😉 sannan ya washe Mata baki😃, daskarewa Goggo tayi cikin tashin hankali ta mik'a hannu tana nunawa Mejidda kifin, da saurinta Mejidda ta K'arasa gurin ba shiri ta dakata musamman yanda taga Kan kifin Yana wangale Mata baki, k'ank'ame Goggo tayi tana ihu cikin tashin hankali Take Fad'in, " wayyo Goggo Kan kifi Yana wangalen Baki zai cinyeni, ki taimake ni Goggo na yi gamo da Aljanin kifi ". Ita kanta Goggo abun tsoro yake Bata Amma sai ta D'an dake ta K'ara lek'awa Amma ga mamakinta sai taga tukunyar wayam, ko irin alamun jinin kifin babu. Goggo ta Jima tana kallan tukunyar Amma ko d'ishin kifi Bata gani ba, zame mejidda take Shirin yi daga jikinta caraf ta Kara k'ank'ame Goggo kamar za'a k'wace Mata ita, itama goggo Bata gama sake wa ba suna cikin Haka ba zato wani almajiri ya rafka ba ra, " Waaahiiideeeeeee " Me jidda ce ta Fad'a aguje cikin d'aki tabar goggo jikinta sai rawa yake ta Mara Mata baya, kafarta D'aya d'ingisa ta takeyi Amma alokacin Nan tuni ta take ta bata sani ba, Almajirin shi dariya ma abin ya bashi yi yake yana k'yak'yatawa, goggo dake d'aki ta cika fam Dan Jin yanda Almajiri ke b'ab'b'aka dariya, lek'awa tayi Dan tayi Masa magana
DUNIYAR FATALE by ayshart647
ayshart647
  • WpView
    Reads 1,186
  • WpVote
    Votes 172
  • WpPart
    Parts 21
Labari ne mai sarkakiya gamida rud'ani na wasu masarautu da wata basadaukiya kuma mayakiya.
MARWAN COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 21,733
  • WpVote
    Votes 2,356
  • WpPart
    Parts 35
Safwan yace, " dama inasan ganin Nazir akwai muhimmiyar maganar dana zo da ita nake san mu tattauna " yana gama faɗa mahaifiyar su Nazir ta rushe da kuka sannan tace, " Nazir baya magana hasalima baya cikin hayyacinsa baisan waye ma akansa, kallan yayan Nazir tayi ta ce, " kai je kaxo mai da Nazir " nan take ya tashi ya fice sai gashi da wheel chair da Nazir aciki sai kallan mutane yake yana zubda hawu hannuwansa da ƙafafu gaba ɗaya sun shanye, Safwan na ganinsa cikin tashin hankali yace, " Wannan ne Nazir ɗin mai ya sameshi? " wani sabon kukan mahaifiyar su Nazir ta ƙara sawa, cikin ƙarfin hali yayan Nazir ya fara magana, " aranar da mahaifinmu ya rasu Nazir yace mana zaije gidansu Maryam, to bayan y dawo muna zaune sai gani mukayi ya zabura yana ihu yana cewa bazai kuma ba, sai kuma muka ga yana ta surutai daga haka kawai sai gani mukayi ya yanke jiki ya faɗi, shikenan har yau ka ganshi ahaka kullin magani ake bashi amma ba sauƙi kullin ciwon gaba yake yi. " gaba ɗaya jikin Safwan ne yayi sanyi cikin sumutar baki Safwan yace, " tabbas Marwan ne " karaf yayan Nazir yace, " wai waye Marwan ɗin nan naji lokacin da yake ta sumbatu yana cewa Marwan kayi haƙuri, ko kuma abokin aikinsu ne dan wannan ciwon ba tantama sihiri ne. " Safwan gaba ɗaya tausayi da tsoron halin da Nazir ke ciki ya kama shi.
MAMAYA by HauwauSalisu
HauwauSalisu
  • WpView
    Reads 28,084
  • WpVote
    Votes 2,181
  • WpPart
    Parts 37
MAMAYA labari ne na wata yarinya Bilkisu da wani babban sadaukin Aljani, ta aikata masa laifi batare da tasan shiɗin waye ba ,shi kuma ya lashi tabokin sai ya kasheta ƙarshe ɗaukar fansa ta kaishi ga aurenta aka wayi gari sun dulmiya ga son junansu . ko shigo cikin labarin dan jin yanda zata kaya.
GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?) by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 160,462
  • WpVote
    Votes 19,531
  • WpPart
    Parts 55
Haka rayuwarta ta kasance tsawon lokaci a cikin kwalbar sihiri. sai dai kuma a lokaci guda BOKA FARTSI ya yi watsi da alkawarinsa da KURSIYYA, ya fiddo ta tare da umurtar ta kan cewa ta ci gaba da bibiyar rayuwar KURSIYYA domin ta kwato wa kanta da kuma shi kanshi fansa. Ko wace ce wannan Kursiyyar? Wace ce wannan daga cikin kwalba? Wace irin fansa ce za ta kwatar wa kanta da boka FARTSI? Ku biyo ni a cikin labarin GIMBIYA SA'ADIYYA don jin bayanai game da abubuwa da dama.
ASEELA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 22,465
  • WpVote
    Votes 1,704
  • WpPart
    Parts 52
Ƙwarangwal ɗin suna tafe wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga gaɓɓan jikinsu tamkar waɗanda aka kunna fanfo ajikinsu, daga kowanne ɓangaren hallita akwai shugabansu wanda shi ne yake kan gaba su kuma suna biye dashi abaya, hannu kowanne shugaba ɗauke yake da wani farin ƙyale da jikinsa yake da ɗishi-dishin jini, ahankali ta fara ɗaga ƙafarta tana ƙoƙarin ja da baya da niyyar guduwa sai dai nauyin jikinta shi ya hana ta gudu har suka ƙaraso inda take, mararta ce ta ɗan karta mata bayanta ya riƙe sannu ahankali ta tsugunna ta duƙa agurin wani irin azababben ciwo na cinta, jeruwa suka yi sahu-sahu sannan suka fara zagaye ta suna faɗin wasu kalmomi da sam bata fahimtar mai suke faɗa, " YAMDUMISA! YAMDUMISA!! YAMDUMISA BISRATIK KUZAR!!!, KIMBASA MIN! KIMBASA MIN!! KIMBASA MIN MAR FAZKINBAT!!! " ( BARKA! BARKA!! BARKA DAI SHUGABA!!!, DAWOWARKU NASARA CE! DAWOWARKU NASARA CE!! DAWOWARKU NASARA CE TARE DA FANSA!!! ) haka suka dinga zagayeta suna maimaita kalmomin bakinsu shugaban ɓangarori biyun masu ɗauke da farin ƙyallen nan suna zazzaga mata wannan kyalen akanta, ciwon da take ji ƙara tsananta yake banda ihu ba abinda takeyi sai kiran sunan KABEER take tana maimaitawa, idan abun ya kuma tsananta ta kuma kiran Kabeer ko Habeebee amma ko gezau basu fasa wannan surutan nasu ba kuma basu fasa zagayeta ba suna yarfa mata wannan farin ƙyallen ba, wani lokacin ma wannan ruwan mai yauƙi na ɗiga ajikinta, ita bata ma san suna yi ba saboda azabar ciwo fatanta kabeer ya kawo mata ɗauki. Ta ɗan ɗauki lokaci ahaka kamar minti talatin ahaka sai ji sukayi kukan jariri alokacin ta galabaita sosai amma ahaka take yunƙurin ɗaukar abinda ta haifa dan neman tsira daga garesu, sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni shugaban ƙwarangwal ɗin nan ya kai hannu yayin da shima shugaban mai mummunar hallitar shima ya kai hannunsa, atare suka suka ɗago jaririyar kowanne ya riƙe hannunta ɗaya yana faɗin, " KAGARSIN BIDA, KAGARSIN BIDA LANBISMA GIRUS " ( KA