GaskiyaWritersAsso
- Reads 1,038
- Votes 14
- Parts 2
yarinya kinyi tafiya mai tazarar gaske tun daga k'asarki Nigeria izuwa wannan k'asa ta India, ko da kika zo Indiar mah sai da ki kayi tafiya mai tsayin gaske gami da had'ari mai girman gaske, k amma kika murje ki kayi fuska duk akan muguwar buk'atarki, kin taho tundaga Mumbai izowa garin Banghulu sannan daga nan kika kutso kanki cikin wannan jejin sanda ki kayi tafiyar kwana d'aya da yini d'aya kafin isowarki nan.
Batare da gazawa ba ko wani tsoro kika zuba gwiwyoyinki kika tan k'washe k'afa gaban bokan da Aljanun duniya ke gwabzawa dashi kuma da yawan wasu aljanun ke shakkarshi gami da mugun tsoranshi dan dayawama akwai Wanda suke kamar bayi a gareshi sabo da k'arfin Pawer shi."...
Dariya ya k'ara bugewa da ita saida yayi mai isarshi sannan ya d'ora da.
" madalla da wannan k'wazo naki, madalla da wannan Jan aiki naki, hak'ik'a Boka FURTAB ya amshi buk'atunki, ki fad'o sunan mahaifiyar yarinyar wacce ta haifeta da ranar da aka haifi yarinyar."...ya k'arashe magana still yana dariya.
Wani irin farin cikine ya rufeta tare da fara magana baki na rawa.
Wata razananniyar tsawa Aljanin Boka Furtab yayi wacce duk da k'arfin hali da rashin tsoran yarinyar saida ta razana, nan ya gargad'eta dayin abin da aka umarceta na fad'in iya sunan Mahaifiyar yarinyar da ranar haihuwarta dansu basa wani buk'atar sunan yarinyar.