zainabmuhammadsani5's Reading List
2 stories
KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CE by miss_untichlobanty
miss_untichlobanty
  • WpView
    Reads 48,436
  • WpVote
    Votes 5,568
  • WpPart
    Parts 56
ASSALAM ALAIKUM! NAGODE SOSAI DA KUKA DUBA WANNAN LABARI FATAN ZAKU ILMANTU .WANNAN SHINE LITTAFI NA NA 4. LABARIN NAN MAI SUNA "KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CE" YARIMAN MA ME JIRAN GADO. TABBAS DA ANJI WANNAN ANSAN BA KARAMIN MAGANA BANE DAN KUWA SARKI YACE A KASHE YARIMA.. TA YAYA ZA'AYI UBA DA DA SU KASANCE DA MACE GUDA A LOKACI GUDA ? SHIN RASHIN SANI NE KO DE YARIMA NE YA CI AMANAR SARKI? KO DE SARKIN NE YACI AMANAN YARIMA? YA ABUN YAKE NE KUMA YA ZA'A FANJE? DAN KUWA DE WANNAN MATAR TANA DAUKE DA JUNA BIYU. NA SARKI NE KO NA YARIMA? DA NE KO JIKA KO KUWA KANI NE? SHIN ZA'A KASHE YARIMAN KO KUWA ZAI SHA DA KAFAR BAYA? WAI MA WACECE WANNAN YARINYA DA HAR TAKE HADA GURI HAKA BAIWA KO MAI YANCI? KU BIYO NI CIKIN WANNAN LABARI DAN JIN YADDA ABIN ZAI KASANCE. SAURAN LABARAI NA MASU ZAKI KAMAR ZUMA: 1. KURUCIYAR MINAL. 2.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE . 3.YA JI TA MATA. 4. KWARKWARAR SARKI, MATAR YARIMA CE DAN ALLAH A TAIMAKA AYI FOLLOWING DINA 🥰!
INDO SARƘA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 79,043
  • WpVote
    Votes 5,550
  • WpPart
    Parts 57
Cikin dare lokacin ƙafa duk ta ɗauke banda kukan tsuntsaye ba abunda yake tashi, alokacin ta farka daga bacci kayan wajen Goggo tasa ta ɗauko zumbulelen farin hijabin tasa, kwandon kayan kwalliyarta da shafe sati bata buɗeshi ba, ta buɗe ta ɗauko hoda ta zazzaga ta shafe fuskarta, hannu da ƙafafuwa Ludayin miyar Baba Huwaila da tun rana ta ɓoyeshi ta ɗauka ta sa a hijabi, ƴar fitilarta ta ɗauka ta fito daga ɗaki saɗaf-saɗaf ta je wajen bakin ƙofa ahankali ta zare sakata ta fice, kamar Aljana ita kaɗai ce a waje haka ta samu ta ƙarasa bayan katangar gidan Mai Gari ( _Dake gida huɗu ne tsakanin gidana Baba Huwaila da na Mai Gari_) ta kamata ta ɗane ta dirga. A hankali ta ɗaga labulen ɗakin Mai Gari ta shiga ta same shi a kwance baccinsa yake hankali kwance, toshe bakinta tayi tana dariya ƙasa-ƙasa musamman da ta tuna irin muguntar da zata yiwa Mai Gari, sai da tayi ta gama ta koma saitin kan Mai Gari ta zaro ludayin miyar ta dai-dai ci kan sa ta bashi ƙwaaal, azabure Mai Gari ya tashi yana susar gurin baya yaja ganin mutum tsaye cikin fararen kaya. Indo canja murya tayi shigen ta Goggo sannan ta fara magana, " Ni ce Goggo Kakar Indo Sarƙa nazo tafiya kai cen makwancina tunda cin Amana zakayi " Mai Gari cikinsa ne ya juya baiyi aune ba sai ji yayi ɗumi na bin wandonsa, Indo na ganin Fitsari na bin ƙafar Mai Gari ta gimtse Dariyarta ta kuma cewa.....🥱