aminat22222's Reading List
22 historias
RAYUWAR BADIYYA ✅  por Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    LECTURAS 280,091
  • WpVote
    Votos 21,641
  • WpPart
    Partes 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
KOWA YA GA ZABUWA... por Gureenjo6763
Gureenjo6763
  • WpView
    LECTURAS 50,683
  • WpVote
    Votos 2,074
  • WpPart
    Partes 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa sadda ze kawo mana karshen shi walau Mutuwa walau sakamako na farin ciki. HIDAYAT yarinya me ƙarancin shekaru marainiya gaba da baya, bata da kowa bata san kowa ba, ta taso cikin kangin rayuwar marikiya an aura mata mafi zaluncin miji cikin maza a rashin sani, wadda ya kasance ɗa ga marikiyarta Kaddarar ƴaƴa ta Haɗa ba tare da wannan azzalumin miji yayi maraba da su ba, ya rayuwa zata zame mata? Ta ina zata iya Kula da kanta da kuma yaranta? Cin su shan su, suruturarsu? Anya zata iya tsallake wannan jarabawar kuwa? Anya ba zata gaza a hanya ta fawallawa Allah lamuranta ta zubawa sarautar shi idanu ba? Shin da dangin miji zata ji ko da Shi karan kanshi mijin ko kuwa da baƙar rayuwa da take ciki? Shin zata iya tsira daga wannan taskar na Tsaka mai Wuya? Duk ku biyo ni cikin wannan littafi na KOWA YA GA ZABUWA... Na muku Alkawari ba Zaku taɓa yin nadama ba, Alqalamina a feke yake don Nishad'antar daku, fad'akantar daku da kuma ilmantar daku duk a cikin wannan littafi.. karku bari a baku labari.
RAYUWA TA THE NOVEL por SYESERM
SYESERM
  • WpView
    LECTURAS 2,374
  • WpVote
    Votos 61
  • WpPart
    Partes 79
LABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?
KASHE FITILA por BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    LECTURAS 251,750
  • WpVote
    Votos 18,495
  • WpPart
    Partes 53
Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru ga Maamu har zuwa lokacin da Allah Ya azurta mata tilon danta Awaisu. A daidai lokacin da take tunanin kyautatawa wadanda suka wahalta musu a baya sai Gimbiya matar dan nata ta murda kambun da ko iyayenta basu santa dashi ba.... Ga uwa, ga da sannan ga suruka.
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)  por Aysha_sona
Aysha_sona
  • WpView
    LECTURAS 227,119
  • WpVote
    Votos 9,578
  • WpPart
    Partes 112
Hassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi nazari akai. Million d'ari, shekara biyar, and your brother is free. It's a contract." Waenan sune kalaman da kyakyawan billionaire Hassan Sooraj ya ra'da mun a kunne. Mutumin dake sa zuciyata hargitsi a duk sanda na daura idanuna akansa. Ina so na kalli cikin kwayar idanunsa nace masa a'a amma taya zan fara? kanina yaci masa bashin naira million da'ya da'ya har d'ari. Bashin dana san har duniya ta na'de bazamu ta'ba iya biya ba saboda mu talakawa ne gaba da baya, ina zamu samu waenan makudan kudi mu biyashi? Abunda yafi daure mun kai yafi bani takaici shine yanda zuciyata kulum take dalmiya cikin kogin sonsa, mutumin da bai daukeni a bakin komai ba sai abar wasarsa. Sunana Hibba Abdullahi, shekarata ashirin da biyu a duniya, ni yar Biu ce, Babur gaba da bayanta, banida kowa banida komai sai kanina, gatanmun shine Allah. Shi kadaine zai iya fiddani daga tarkon wanan kyakyawan attajirin, mai dara daran idanu masu mugun firgitar mun da zuciya. Wanan shine labarin mu.
WATA KISSAR (Sai Mata)  por Ayshercool7724
Ayshercool7724
  • WpView
    LECTURAS 38,806
  • WpVote
    Votos 2,004
  • WpPart
    Partes 31
Labarin soyayya wanda zesa ma'abota karatu nishaɗi, labarin wata yarinya da ta jarumtar nunawa namiji tana sonshi, kuma ta jajirce gurin zama da shi dukda ƙalubale da kuma izzarsa da taurin kai amma tai amfani da salo da kissa gurin janyo hankalin sa kar abaku labari ku biyoni dan jin yadda zata kaya
KANA NAKA..! por JamilaUmar315
JamilaUmar315
  • WpView
    LECTURAS 13,785
  • WpVote
    Votos 867
  • WpPart
    Partes 20
In ya kalli FA"IZA sai yaji Fiye da madaukacin Takaicin daya ke ji in ya tuna itace yau MATAR SA..Fa"iza ba mafarkin sa bace a irin Rayuwar ISHAQ KABIR KAROFI..Sam Fa"iza bata dace ko kada'n da Tsarin Rayuwarsa ba, kowa yasan Ishaq dan gayu ne mai ilimi ne,kyakyawa ne dan Fafane dan Alfahari ne Duniya tasan da zamansa mai Burin Auran mace FARA mai kyau mai Tarin kwalayen matakan karatun.Zamani SAI DAI KASH" Hakan bai samu ba..Sakamakon kutse da Fa"iza tayi cikin Rayuwarsa ta Ruguza Mafarkinsa har Abada bazai daina Hango FA"IZA a matsayin Nakasun Mafarkinsa ba..
KYALKYALIN KAUNA por MSHAKURworld
MSHAKURworld
  • WpView
    LECTURAS 72,009
  • WpVote
    Votos 1,575
  • WpPart
    Partes 48
A story about a drug lord with an innocent girl suffering from dyslexia
DUKKAN TSANANI  por Jeeddahtou
Jeeddahtou
  • WpView
    LECTURAS 121,857
  • WpVote
    Votos 9,601
  • WpPart
    Partes 71
Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min
GINI DA YAƁE por 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    LECTURAS 21,331
  • WpVote
    Votos 3,164
  • WpPart
    Partes 44
Duhuwa itace abinda yake baibaiye da wannan ginin Ali ! Tayaya zaka yi ƙoƙarin gini akan ruɓaɓɓen tubali! Ginin da kuma yaɓen dukkaninsu ababen banza ne idan har aka samu tangarɗa awurin tubali! Tubali shine gini shine kuma yaɓe! Kayi kuskure daga wargaza nagartar tubalinka ta hanyar dasa tubalin toka a maimaikon na ƙaƙƙarfan dutse. Tirr da muguwar rayuwar ka Ali!!!