HauwauSalisu
labarin taurari uku Jiddah, Alawiyya, Mustapha, kowane ya ci wahalar rayuwa yadda ya kamata, Jiddah ta taso cikin gagarin rayuwa wadda hakan ya faru ne da mahaifinta yaba wata Kirista ita a Lagos mai suna Iyami, bayan ta gudo kuma ƙaddara tasa aka aura mata aure da Deeni wanda ya cigaba da gana mata azabar rayuwa, duk lokacin da sauƙi ya zo mata sai ya gushe. Alawiyya kuwa Barista ce wadda ta rabu da mahaifiyarta da mahaifinta tun tana ƙarama har ta girma sai ranar aurenta ta haɗu da mahaifinta mahaifiyarta kuwa sai bayan data zama lauya taci karo da fuskarta a labarai ta kashe mijinta, hakan yasa ta lashi takobin fitar da mahifiyarta ko ta halin ƙaƙa ne. Mustapha kuwa tun kafin aurensa yake da burin yin rayuwar aurensa cikin farin ciki da walwala tare da soyayya mai girman gaske amma sai bai dace ba duk da cewar matansa uku amma bai taɓa samun cikar burinsa ba na samun wadda zata kula da shi ta ba shi kulawar soyayya.
Akwai abubuwa da yawa a cikin labarin ku dai ku shiga kanku tsaye ku karanta wannan labari mai ban mamaki da al'ajabi.
Taku a kullum Haupha ✍️