kilishi_'s Reading List
23 stories
El'mustapha  by Pherty-xarah
Pherty-xarah
  • WpView
    Reads 329,407
  • WpVote
    Votes 25,579
  • WpPart
    Parts 73
'Mijin yar'uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya'yan sa ya zamto ba kowa a xuciyar sa sai ni. El'mustapha ya shiga cikin rukunni wasu mutane da nake ganin matuqar qima da mutuncinsu sannan kuma yabi ya manne a xuciyata yadda dai dai da minti daya na kasa manta shi, amma mutumin da baya ganin kowace mace a idanuwansa sai matar sa,,
BA UWATA BACE by meeshalurv
meeshalurv
  • WpView
    Reads 68,457
  • WpVote
    Votes 5,252
  • WpPart
    Parts 48
BA UWA TA BACE Zaune take gefe guda cikin gidan nasu, tana kallon abinda Yan gidan nasu sukeyi k'awar tace Hadiza zaune gaban mamar tasu tana mata lissafin kud'i da tasamu, daga daren jiya zuwa yau da safe. Mamar sai washe hak'ora take tana murna sannan tace "Ai na fad'a Miki idan Kika bi Alhaji Hamza kwanan gida sai ya Baki mamaki." Hadiza tace gashi kuwa ya bani mamaki mama domin tunda Nike arayuwata bantab'a kama irin kud'in Dana kama yau gugu na gugur naira har dubu hamsin mama tawani wutsilo daga kugerar da take Yar tsugunne, ta fad'o k'asa sannan ta d'aga Kai ta dubi Hadiza ko zafin fad'uwar bataji ba tace da gaske kike ko da Wasa Yar nan. Hadiza tace "wallahi mama kingansu ma" ta fito dasu ta nuna mata kud'in hannu na rawa mama ta k'arbesu ta tashi tana juyi da rawa agaban d'iyar Tata. Bilkisu ji tayi k'amar ta kurma ihu Dan bak'in ciki wannan wata irin uwa ce Allah ya Basu, wasu hawaye masu zafi ya zubo mata ganin yadda ita Tata rayuwar zata Kaya kenan ga wata uwar yunwa datakeji, Amma saboda tak'i bin abinda uwar Tata takeso ta hanata, gashi ita tashin hankalinta shine idan dare yayi wani irin tuggu zasu had'a mata Dan taji mamarta da yayanta na zancen, zuwan Alhaji kamilu zuwa gareta ko tanaso ko bataso yau sai ya kwana da ita, Anya kuwa wannan ita d'in uwa ce agaresu tana cikin wannan tunanin taji k'ara bud'e kyauren gidansu na langa langa daga Kan da zatayi Dan taga Mai shigowa sai taga k'awarta ce ta biyu zainab. Shigowa tayi cikin wata irin shiga domin kayan jikinta amatse suke sosai duka sun fitar da surar jikinta rabin breast d'inta duk awaje cikin takun yauk'i da yanga tashigo, tana yatsina ko sallama babu mamarta ta k'alla sannan tace "wallahi mama yau nagaji Dan wannan d'an iskan Alhajin bak'aramin sasuk'a ta yayi ba tun dare yake abu d'aya har safe gashi bak'arami ba ga abun tashi kamar tabarya, gaskiya ya cika d'an iska
AMRAH NAKE SO! (Completed✅) by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 191,684
  • WpVote
    Votes 17,464
  • WpPart
    Parts 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."
ABDOUL-NASSER (ALFAH) by Humaira7531
Humaira7531
  • WpView
    Reads 21,922
  • WpVote
    Votes 745
  • WpPart
    Parts 35
ya kasance shi mutunne da yatsani mace,sannan yana masifar son mutuwa baida wani buri daya wuce ace ya mutu,domin ya rasa farincki tsawon rayuwarsa.baya hudda da kowa haka bai magana da kowa face mutun guda amininsa kuma abokinsa malik.baida ruwan sha kamar giya,duk abunda zai illata rayuwarsa nemansa yake,idan yaga mace jiyake inama zai samu damar kasheta,tsanar dayayiwa mace babu abunda yayi ma ita. kwatsam saiga wata budurwa ta fado cikin rayuwarsa SOFIYYA wacce aka fi kira da (FIYAH).
MATA KO BAIWA by Hafssatu
Hafssatu
  • WpView
    Reads 35,866
  • WpVote
    Votes 784
  • WpPart
    Parts 59
Feena macace Mai matsananin kishi, wadda Tasha Alwashin duk ranan da mijinta yayi mata kishiya zata kasheshi ta kashe matar,sannan ta kashe kanta, Kowa yarasa, Dije yarinyar kauye yarinyan ce Mai ladabi da biyaya da bin umurnin iyayen ta, kwatsam sai gata gidan feena A matsayin matar gidan inda taje a matsayin baiwa Mai aikin Ana hakan sai ga ciki ya billo A jikin dije..qara qara shin ya abun yake me?..
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Reads 74,635
  • WpVote
    Votes 2,361
  • WpPart
    Parts 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
DUKKAN TSANANI  by Jeeddahtou
Jeeddahtou
  • WpView
    Reads 121,227
  • WpVote
    Votes 9,598
  • WpPart
    Parts 71
Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min
YAR BABBAN GIDA by DeejahtAhmad
DeejahtAhmad
  • WpView
    Reads 33,849
  • WpVote
    Votes 2,324
  • WpPart
    Parts 29
Na tsaneki at thesame time ina sonki, inajin tamkar na cilla ki ta saman bene na garzaya na taro ki gudun karki fad'a kiji ciwo~ *Alee* ♡ yacce kake nuna min halin ko oho yana ba'kanta raina mutu'ka~pherty ♡ kin gusar da duk wani manufata a kanki~Alee ♡ Na tsaneka bansan sake saka ka a idona~pherty ♡ Ta ya zaka so mutum ka kuma 'ki shi a lokaci d'aya~Alee ku biyoni danjin labarin sar'ka'k'kiyar soyayyar masoyan biyu. 'yar babban gida; labarin yarinya d'aya tilo 'yar masu dashi wacce ta fad'a tarkon soyayyar Alee wanda ya kasance maraya ciki da waje ga uwa uba 'kazantaccen talauci.
DABAIBAYI (COMPLETED)✅ by DeejahtAhmad
DeejahtAhmad
  • WpView
    Reads 47,597
  • WpVote
    Votes 3,826
  • WpPart
    Parts 36
...mahaifiyata ta 'bata tun ina da shekara takwas a duniya,... a lokacin da na dawo da sakamakon shedar kammala primary na tarar da gawar mahaifina kwance..., kawu na daya d'auki alwashin ruqo na ya guje ni a lokacin da nake tsananin buqatar sa...na tsinci kaina cikin mafarki da daddyna a kullum yana kuma jaddada min kada na bari haske na ya kufce min, lallai na kasance tare dashi..., se dai kuma na farka na ganni cikin wata rayuwa da ban ta'ba kawo wa cikin kundin littafin rayuwata ba...bayyanar Ammi na gefe guda kuma zaratan samarin biyu dake fad'i tashi a kaina, 'yan uwan juna, jini d'aya...shin ina zan kama?...
NAYI NADAMA  by Pherty-xarah
Pherty-xarah
  • WpView
    Reads 53,203
  • WpVote
    Votes 1,649
  • WpPart
    Parts 15
Farkon gani na da ita naji xuciyata ta amince da ita duk da nasan abinda ke tsakanin ku, na cigaba da ďawainiya da soyayyar ta har lokacin dana bar qasar nan, sanda ka gayamin kaga Ruhayma dalilinta na dawo wannan qasar, itace macen da nake so, itace macen da nake burin aure a matata ta biyu ashe bisa rashin sani ita MATATA CE.